Saturday, December 7, 2013

What is XMPP and why using it

What is XMPP

Extensible Messaging and Presence Protocol (XMPP) is a communications protocol for message-oriented middleware based on XML (Extensible Markup Language). The protocol was originally named Jabber, and was developed by the Jabber open-source community in 1999 for near real-time, instant messaging (IM), presence information, and contact list maintenance.

What is the problem if we don't use XMPP

In most cases the Raspberry Pi does not have a public IP address. The Raspberry Pi can initiate a connection to web servers that have public IP addresses. But those servers can not initiate a connection to Raspberry Pi. That means servers can not send any information to Raspberry Pi until Raspberry Pi start the connection. So the latency of messages from servers can not be guaranteed.

In order to minimize that latency, our Raspberry Pi can either inquire the server periodically or keep the connection alive. The first option is not efficient and the second option is not supported in free web services such as App Engine.

How XMPP solve this problem

There are many free XMPP servers on Internet and those servers can keep a long-lived TCP connection with our Raspberry Pi. Since all XMPP servers have public IP address, they can exchange messages freely. This method can eliminate the unnecessary latency introduced by polling intervals

Raspiberry Pi

The Raspberry pi is a mini computer which is designed in a single board with all the essential components required for running an operating system. The Raspberry pi is designed to be low cost and easy to use. The board has a micro USB port which can be used to supply 5V DC using an adaptor with rating not less than 1A. The board can be powered up from the USB port also but it is not recommended. The board has a HDMI port which can be used to connect it to the HD TV using an HDMI cable. A video input port is also available with a Raspberry pi board which can be used to connect an external camera. The board can also be connected to the PC monitor using a HDMI to VGA adaptor cable. The Raspberry pi board has a Composite RCA (PAL and NTSC) output which enables them to be connected directly to CRT TV screens and an audio output is also available. The board has two USB2 ports where the keyboard and mouse can be plugged in. There is an Ethernet port which can be used to connect the board to a computer network. The board also has a SD card slot and the Raspberry pi is designed to boot from the SD card.
The device using Broadcom controller chip which is an SoC (System on Chip). This controller has all the peripherals like timers, interrupt controller, GPIO, USB, PCM / I2S, DMA controller, I2C master, I2C / SPI slave, SPI0, SPI1, SPI2, PWM, UART0 and UART1. This SoC has the powerful ARM11 processor which runs on 700 MHz at its core. The controller also has a graphical processing unit (GPU) which includes VideoCore, MPEG-2 and MPEG-4. It also has a 512 MB SDRAM.    
The operating systems versions of Windows, Mac and Linux are available which can be installed in the Raspberry pi board. Raspberry Pi foundation introduced a new tool called "New Out Of Box Software" or "NOOBS" which includes a package of Operating systems which the user can select to install on the Raspberry pi board once it boots up for the first time. The operating systems the NOOBS installer includes are only Archlinux ARM, OpenELEC, Pidora, Raspbmc, RISC OS and the Raspbian. This article discusses how to install the Ubuntu operating system in the Raspberry pi.

Friday, July 19, 2013

Sunday, July 7, 2013

JERIN SUNAYEN LITATTAFAN KOYI NA Mannir Ahmad Getso



1. Koyi yadda ake shiga Intanet
2. Koyi yadda ake Gina shafin Yanar Gizo
3. Koyi yadda ake aiki da Na'ura mai kwakwalwa
4. Koyi yadda ake Zanan Softwaya
5. Koyi yadda ake Kasuwanci ta Intanet
6. Koyi yadda ake Kasuwancin Forex
7. Koyi yadda ake Gyaran Na'ura Mai Kwakwalwa
8. Koyi yadda ake Zanan Softwaya da Java
9. Koyi Yadda ake Zanan Software da VB

Koyi yadda ake shiga Intanet 1 (2007)

GABATARWA

Da sunan Allah mai Rahama mai Jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzommu Annabi Muhammadu (SAW); Godiya da yabo sun tabbata ga Allah (SWT), wanda bai haifa ba kuma ba’a haife shi ba, mamallakin kowa da komai, Wanda ya halicci kowane abin halitta, kuma ya bawa dan Adam damar kera abubuwan bam mamaki, kuma ya bashi fasahar jujjuya abubuwan daya kera. Tsira da aminci su kara tabbata ga babban bawansa, kuma masoyinsa, Annabi Muhammad (SWA); Bayan haka, na rubuta wannan Littafin ne domin wadanda suke son su koyi yadda zasu rinka shiga Intanet, ko wadanda ayyuka sun yi musu yawa, basu da lokacin da za suje makaranta su koyo yadda ake shiga Intanet, kuma suna matukar son su koyi yadda zasu rinka shiga Intanet. Shi wannan littafi zai koyar da kai yadda zaka shiga Intanet, kaduba wasika ko ka aika da wasika ko kayi nazari ta Intanet, da sauransu. Zakaga a zamanin yanzu komai sai kaga anayinsa ta Intanet, kamar Rajistar Jarrabawar WAEC, NECO, JAMB da sauransu zakaga ta Intanet zakaje kayi rajista, da sauran abubuwa da dama, sannan zakaga ko assignment aka baku a makaranta maimakon kaje Library(dakin karatu), kayi ta bincike, baka samo abin da kakeso ba, to a yanzu sai dai ka shiga Intanet karubuta abin da kake nema, sai kwamfiyuta ta binciko maka amsar abin, misali:- kana neman ma’anar kwayar zarra(wato atom), misali kanason ma’anarta kamar kala goma, kaga anan ko dakin karatu kashiga sai kasha wahala kasamo ma’ana goma, amma idan ka shiga Intanet kaje shafin yanar gizo ta Google karubuta “Definition of an Atom” zakaga kwamfiyuta ta kawo maka shafin yanar gizo-gizo kamar sama da dubu tamanin da sukayi Magana akan definition na. Kaga in bata Intanet ba duk wadannan bayanan ba zaka samu ba. Misali kullum kana jin labaran BBC Hausa amma baka taba ganin hotunan masu labaran ba, to kana zuwa Intanet idan kaje shafin yanar Gizo Gizo na BBC Hausa idan kabincika zaka ga Inda aka jero sunayen masu aikin BBC Hausa.  Kuma shi wannan Littafi akwai Video CD dinsa, da zai koyar maka da komai kana gani ta bidiyo yadda zaka gane komai a saukake, zaka iya samun Video CD dinsa a wuraren da ake sayar da Littafin.

 MANNIR AHMAD  GETSO
Saturday, March 31, 2007   3/31/2007 4:25:00 PM

 

ME NENE INTANET?

Intanet, dabarace ta hanyar hada Kwamfiyuta da wata kwamfiyuta yadda zasu rinka musayar sakonni, wato yadda za’a samu damar aikawa da karbar sakonni, da wasu abubuwa ta cikin kwamfiyuta a kowace kwamfiyutar datake Kan Intanet, a duk inda take a duniya. Misali kwamfiyuta tana nan Najeriya an hadata da Intanet sannan wata kwamfiyuta tana china ita ma an hadata da Intanet to daga nan Najeriya zaka iya bude kwamfiyutar da take china, ka karanta abubuwan da ke cikin ta, ko ka ika mata da sako na rubutu ko na Magana, ko na hoto, ko na bidiyo da sauransu.

ME CECE YANAR GIZO-GIZO (WEBSITE)
Yanar Gizo-Gizo: - tarin shafuffuka ne akan Intanet, akan wadannan shafuffukan ne rubutu yake, ko hotuna. Akan wadannan shafuffuka zaka iya  bincike, ko karatu, ko a aikawa da sakwanni zuwa wata kwamfiyuta a duniya, a cikin dan kankanin lokaci, Ta haka zaka iya aikawa da sakonni na sauti, ko na magana, ko na hoto, ko na bidiyo kona abu mai motsi (animation) da sauransu, zuwa ko wacce Kwamfiyutar da kakeson ka aika, a duniya. Misalin shafin yanar gizo-gizo shine anan kasa, Shafin Yanar Gizo-Gizone na Muryar Amuruka:-

TA YAYA INTANET YAKE AIKI?


Shi Intanet yana aiki ne, kamar yadda wayar salula ta ke aiki, misali idan kana da Wayar-Salula (Handset) da lamba, da wannnan lambar zaka rinka aikawa da sakonni, ko karban sakonni, misalin lambar waya sune 08051619043, to itama duk Kwamfiyutar da ka hada ta da Intanet tana da lamba, wannan lambar ita ake kira, IP  ADDRESS, (IP na nufin INTANET PROTOCOL). Kowace Kwamfiyuta idan aka hada ta da Intanet tana da IP Adress. Misalin IP address shine 192.168.32.1 Shi Intanet ta wurin aikawa da sakonni yana amfani da wani abu wanda ake kira Intanet Protocol shi Intanet protocol shine yake nuna ina DATA (information, wato bayanai) dinka ina zasu ko daga ina suke, misali:- ka rubuta wasika a Kwamfiyuta ta 192.168.45.2 zaka aikawa zuwa 192.168.87.45(misali Yahoo Server), idan zaka aika da wasika irin ta gargajiya(takarda) ba wai zakaje ka ajiye wasikar a post office(wurin aikawa da wasika) bane, a’a, ana bukatar karubuta adireshin da wasikar zataje. To shima haka Intanet protocol yake a Intanet, yana da lambobi kashi hudu (a yanzu), kuma kowace lamba tana kasa da 256, lambobin suna nan kamar haka: - 192.112.36.5 ko 128.174.5.6     Kaga lambobin farko suna nuna daga wane irin network sako yake, na dama daga karshe suna nuna daga wacce Kwamfiyuta bayanin ya fito,  misali:- kana wata cyber cafĂ©(wato dakin shiga Intanet) a Kwamfiyuta ta 12 sannan network din su shine 128 kaga IP naka zai zama 128.XXX.XXX.12.(X tana nufin wasu lambobi). Idan baka gane misalin farko ba, ga wani misali ko zaka gane:- misali kana da Wayar Salula (Handset), da lamba, sai ka rubuta sako ka aika wa wani, shi wanda ka aikawa sakon, ya riga ya cire layinsa daga cikin Wayar Salula (Handset) dinsa, to lokacin da ka aika da wannan sakon, sakon zai tafi network (misali MTN), idan yaje can, sai su ajiye wannan sakon har lokacin da wanda ka aikawa sakon yasa layinsa, yana sa layin sa, zai ga sakon da ka aiko mai, ya karanta. To shima Email haka yake, idan ka budo email dinka ka, ka rubuta wasika zuwa ga wani, shi wanda ka aikawa idan baya kan Kwamfiyuta, to wannan wasikar zata tafi wurin webserver (misali YAHOO), sune zasu ajiye wannan sakon, har duk lokacin da wanda ka aikawa sakon yaje ya budo email dinsa, saisu toro masa da wasikunsa gaba daya, ya karantasu, wannan abun yana faruwane a cikin dan kanknain lokaci. Su web server din zasu turo masa ne ta hanyar WEB BROWSER (Wanda zanyi Magana anan gaba), bayan sun turo masa shi kuma sai yakaranta ta wasikunsa akan web browser din, (misalign web browser shine  Microsoft Intanet Explorer).
 Ga Misalin Hoton shafin yanar Gizo-Gizo na BBC Hausa.


YADDA ZAKA HADA KWAMFIYUTARKA DA INTANET


Idan kana da kwamfiyuta, zaka iya hadata da Intanet ta hanyoyi kamar haka:-  ta DIAL-UP, ADSL, ISDN, V-SAT, RADIO(GPRS), HOT SPOTS, WI-FI, da sauransu duk wadannan hanyoyi ne da zaka hada kwamfiyuta da Intanet, abin da ake nufi shine zaka iya hada kwamfiyutarka da Layin wayar gidan ka, kamar starcoms, ko da tauraron dan adam wato vsat, ko ta cikin iska, ko ta wayar tafi da gidanka, duk  wadannan hanyoyi ne na hada kwamfiyuta da Intanet.
Ga wani misali domin mai karatu ya kara gane menene Intanet. Misali, idan kasiya Wayar Salula (Handset), bazaka iya kiran kowa ba sai ka saka layi amma wata wayar zaka iya budo cikin ta, zaka iya kara sunaye, harma zaka iya rubuta wasika amma ba zaka iya aikawa da wasikar ba sabo da baka sa layi ba, na biyu idan zaka sa layi, zaka zabi, wane irin layi zaka sa, layin VMOBILE, ko  MTN, ko glo, ko MTEL, su wadannan su ake kira Network Service Provider, idan kasiya layin, ajiki ne zaka ga lambarka, da wannan lambar zaka iya kiran mutum, to  itama haka Kwamfiyuta take, idan ka siya Kwamfiyuta, zaka iya aikace aikacenka da ita har zaka iya kallon CD zaka iya yin rubutu da ita, har inkasa mata wata Softwaya misali softwayar ta Encata, kayi bincike da ita, sai dai bazaka shiga Intanet ba, idan kana son ka hada ta da Intanet, da farko abin da zaka fara yi shine zaka je kamfanin da suke samar da service na Intanet, wato  Intenet Service Provider (I S P), sune suke bada sabis na Intanet sune zasu hada maka kwamfiyutarka da Intanet, ko su baka abin da zaka hada da kwamfiyutarka ka shiga Intanet, ko suje su hada maka. Sannan suyi maka bayanin abubuwan da zaka rinka biyansu. Idan kana son bayani game da Intanet Service Provider ko yawan abin da ake biya zaka iya ziyartar shafin mu na yanar Gizo-Gizo.

ABUBUWAN DA AKE YI A INTANET

Ya wancin abubuwan da akeyi a Intanet a nan Nigeria baya wuce aika wasika da karanta wasika, sai kuma duba labarai da bayanai, wadannan sune zaka ga mutane sunfi yawanyi, alhali wadannan abububuwan abu daya kenan da akeyi a Intanet. Ga kadan daga cikin irin abubuwa da akeyi a Intanet, sune:-
1.  Karatun Alkur’ani Mai Girma: akwai shafin yanar gizon da zaka je, ka karanta Alkur’ani, zaka iya zabar kira’ar da kake so, da surar da kake so.
2.  Koyon Karatu: Akwai shafin yanar GizoGizo, da zakaje ka koyi karatu, ko a koyar da kai, har a rinka baku assignment(Gwaji), har in ka gama karatun, kayi jarrabawa idan kaci jarrabawar a baka sakamako  abaka certificate  wannan shi ake kira (E-LERNING ).
3.  Bincike ta fannin ilimi mai zurfi, zaka iya bincike ta fannin ilimi mai zurfi kamar su yadda sassan jikin mutum yake aiki ko sinadaran da ke jikin mutum, idan sassan mutum ne zakaga ga yadda zuciya take bugawa ko yadda sakonni suke tafiya tacikin kwakwalwa ko yadda cuta take shiga jikin dan Adam da yadda take shiga cikin sassan jikinsa, da yadda take yaduwa, ko ilimin taurari da nisan dake tsakaninsu, da ilimi mai zurfi. Ko tarihin kasashe, Tarihin Al’umma da yarensu.
4.  Sanin yadda abu yake aiki:- akwai shafin yanar gizo-gizon da idan kaje sazu nuna maka yadda kwamfiyuta take aiki, ko yadda aka kera wayar salula, ko yadda ake kera rediyo, ko yadda ake kera wasu na’urori na lantarki, lo yadda zaka kera makunnin kashe wutan nefa ko kunnawa ta hanyar tafi ko ta hanyar atishawa ko ta hanyar remote control na talabijin, wato misali kana cikin daki ankawo wuta, da remote control zaka iya kunna wutan nepan ko idan kayi tafi sai kaga gulob din ya kawo wuta indan ka sake yi sai kaga ya mutu, zaka iya ganin yadda wasu abubuwa na bam mamki suke aiki, kamar yadda kwamfiyuta(robot) take aiki kwamfiyuta(pc), da wasu abubuwa na bam mamaki.
5.  Koyon yadda ake gyaran abu:- akwai shafin yanar gizo gizon da idan kaje zasu kawo maka hoton yadda zaka gyara abu, misali kana da waya sai ta samu matsala, ko ta daina kawo wuta na haske, da kaje website din zaka zabi sunan wayarka da model dinta (lambarta) sai kaga ankawo maka hotunan rikice rikicenta sai ka duba inda LCD Light yake sai kabudo hoton zaka ga an nuna maka kaza zaka cire ko ka canza.
6.  Neman Aiki:- akwai website (shafin yanar GizoGizo) da dama da zaka shiga a Intanet ka nemi aiki, irin aikin rubutu ta cikin Intanet kana zaune daga gida, ko yadda zaka rinka yiwa wasu kamfanoni talle idan kana da website.
7.  Siyayya:- a Intanet akwai websites (Shafuffukan Yanar Gizo-Gizo ) da zaka zabi abin da kake son kasiya a fada maka farashin sa, in ma kana da credit card (Kudin Intanet, misali MasterCard) zaka iya siya, idan daga kasar waje ne ayo maka shippin (a aiko maka ta cikin jirgin ruwa) zuwa Nigeria a fada maka adireshin da za kaje ka karbi abin naka, Ga Misalin Shafin Yanar Gizon Da zakaje kayi Siyayya:-


8.  Aikawa da sakonni da karban sakonni: - Ta Intanet zaka iya aikawa da sakonni zuwa wurare daban-daban cikin dan kankanin lokaci, zaka iya aikawa da sako daga Intanet zuwa wayar salula (handset).
9.  Kasuwanci:- zaka iya siye da siyarwa ta Intanet, misali zaka iya siyan sha filin shafin yanar gizo (Web Hosting) da sunan shafin yanar gizo(Domain Name) bayan kasiya wadannan sai kagina shafin yanar Gizon(akwai littafina da yake koyar da yadda zaka gina yanar gizo), bayan ka gina zaka iya siyar da shafin yanar gizon, ko kuma da shafin yanar gizon naka ka gayyato wasu kamfanoni karinka yi musu talle a shafin naka suna biyan ka, idan suna samun mutane suna zuwa shafinsu daga naka, wannan shi ake kira E-COMMERCE.




INANE CYBER CAFÉ?

CybercafĂ© wuri ne da aka tanada domin shiga Intanet, wurine da za kaga Kwamfiyuta da yawa, an hadasu  da Intanet, wato dakin shiga Intanet kenan, idan kaje wurin kana son kayi browsing (wato ka shiga Intanet) zaka basu kudin iya awowin da kakeson kayi, sai su baka wata takarda da take dauke da lambobi (password), wadannan lambobin sune zakaje karubuta su ajikin Kwamfiyuta ka budo Intanet, zanyi bayani akan yadda ake budowa nan gaba. Ga Misalin yadda Cyber CafĂ© Take:-

ME NE NE WEB BROWSER?

Web browser softwaya ce da zata baka damar budo, da ganin Shafuffukan  Yanar Gizo-Gizo, wato Website,
Misalin web browser sune: - Microsoft Intanet Explorer, Opera, Netscafe Navigator, Mozilla, da Dillo da sauransu.

ME AKE NUFI DA WEBSITE?

Website itace tarin Shafuffukan yanar Gizo-Gizo, wadanda suke dauke da bayanai na rubutu, ko hotuna, ko sauti, da abubuwa masu motsi, kamar yadda nayi bayani tun a farko. Akan shafin ne zaka budo ka karanta bayanan da kake so, ko kaji, Misalan shafuffukan Yanar Gizo-Gizo sune: - www.bbchausa.com www.yahoo.com www.google.com www.mannir.com , duk adireshin da kaga ya fara da www ko http:// to website ne, www yana nufin World Wide Web http:// na nufin Hyper Text Transfer Protocol. Sannan zakaga yawanci suna karewa da, .com (company), ko .org (organization). Ko .net (network), da sauransu, ko kaga ya kare da .co.uk wato yana nufin ita wannan website din ta Engila ce, .co.ng, wannan website din ta Nigeria ce, akwai kuma wadanda zaka ga sun kare da .gov wato na gwmanati ce, .edu na fanning ilimi ce, .mil ta sojoji ce wato military, .info wato bayanai information, .Biz wato harkokin kasuwanci, da sauransu.

ME NE NE INTANET ADDRESS?

Internet address, abubuwane guda biyu wato Email da www, su wadannan suna karkashin wani abu ne da ake kira domain name system, amfaninsa shine domin tantance adireshin yanar gizo-gizo a Intanet, misali, a cikin Gari zaka samu akwai, unguwa a Unguwa akwai layi, a layi akwai gida, to haka ma wannan yake, misali a website na yahoo zaka samu suna da folder na email, suna da folder na search suna, da folder na shop, a cikin folder na email zaka samu akwai folder na mail a cikin folder na mail za ka samu akwai folda, misali kana neman inda aka fassara kalmomin kimiyya ne a sahfi na kaga a adireshin zaka samu kamar haka http://www.mannir.8m.com/kimiyya/kalmomi wato yana nufin idan kashiga website din mannir akawai folder mai suna mannir a wannan foldan(jaka) akwai wata folder mai suna kalmomi a folder kalmomi ne zaka samu fassara kalmomin.misalin adireshin www shinw www.mannir.com , kaga wannan yana nufin shafin yanar gizo-gizon mannir, shi muka misalin adireshi na email shine:  ceo@mannir.com . wato yananufin shugaba a adrieshim mannir. Wannan alamar @ ana furta tad a at

YADDA ZAKAYI AIKI DA MOUSE WURIN SHIGA INTANET

Shi mouse wani abu ne da ake amfani dashi, wurin motsa pointer (wata yar kibiya da zakaga tana yawo a cikin gilashin kwamfiyuta) dake cikin monitor(screen din Kwamfiyuta), shine za kaga kana motsa shi itama pointer (kibiyar) na motsawa,
 kuma idan zaka rike mouse zaka rike shine kamar haka:-
sannan Idan dai kana browsing (kana cikin Intanet) idan zakayi click(danna mouse) karinka matsa bangaren hagu, sannan idan dai kana cikin website(shafin yanar gizo) baza kayi click din wuri ba sai kaga pointa(kibiyar) ta zama hoton hannu , duk inda kaga ta zama hoton hannu za’a iya shiga wurin, wato zaka iya click a wurin, sanan inda zakayi click din zai iya zamowa rubutu ko hoto ko abu me motsi, duk lokacin da kayi click akan abu zai bude maka wannan abin da kayi click akai, misali:- ka bude website din www.bbchausa.com kana duba shafin, sai kaga wani wuri an rubuta SHIRIN SAFE  to da kaje kan tsakiyar rubutun zakaga pointer(kibiya) ta zama hannu, sai kayi click(ka danna) wurin, to zai bude maka shafin da aka kawo cikakken labaran shirin safen, sannan kada ka manta koyaushe zakayi click karinka yin click din bangaren hagu na mouse, domin in kayi click din dama zai kawo maka wasu abubuwa ne,wato (menu) sannan a wasu shafin zaka yi amfani da ENTER na kibod wurin yin click, kamar a yahoo sign, zaka iya yin amfani da ENTER wurin click din sign in, kuma zaka iya yin amfani da mouse wurin yin sama da shafi ko kasa da shafi, idan zakayi zakazo can bangaren karshe na screen zaka ga wani arrow(kibiya) a sama da wata a kasa  sai kazo kayi  click akan aron(kibiyar), zaka ga shafin yanayin sama ko kasa, idan kuma baka ganeba zaka iya amfani da aron sama ko na kasa ajikin kibod, zakaga wasu kibiya daya na kallon sama daya na kallon kasa daya na kallon dama daya na kallon hagu. Yanzu kuma zan koma inyi bayani daki-daki gameda yadda zaka shiga Intanet.

NEMAN DAKIN SHIGA YANAR GIZO-GIZO (CYBER CAFÉ)

Da farko idan kanason ka shiga Intanet, zaka nemo inda cyber café take wato inda kaga an rubuta cybercafé ko Intanet Café, ko Café, to duk inda kaga an rubuta daya daga cikin wadannan to wannan wurin ana shiga Intanet. Sannan idan garin dakake babu cyber café to zaka iya shiga Intanet ta cikin Wayar Salula (Handset) idan tana da WAP. (kuma akwai littafin da na rubuta mai koyar da yadda ake shiga Intanet ta cikin wayar Salula, da yadda zaka saita wayarka tana shiga Intanet, sannan na yi bayani kadan a cikin wannan Littafin, zaka iya samun littafin a inda ake siyar da wannan littafin, in kuma kanason littafin ta Intanet, zaka iya aiko mana wasika zuwa adireshimmu na Email manniru@gmail.com .

YADDA AKE SHIGAR DA (PASSWORD) LAMBOBIN DA SUKE JIKIN TAKARDA, A BUDE DESKTOP

Idan kaje cyber cafĂ© zaka fadi irin yawan awar da kake so kayi yawancin awa daya bata wuce N100, ko N80, minti talatin kuma N60, ko N50 a yanzu. Idan ka basu kudin zasu baka wata ‘yar takarda wacce take dauke da wasu lambobi (password) a jikinta. bayan sun baka sai kazo ka samu Kwamfiyutar da ba kowa akai, ka zauna ka shigar da lambobin dake jikin wannan  takardar, bayan ka zo ka zauna zaka ga screen na kwamfiyutar misali kamar haka:-

A wadannan layikan guda biyu ko daya da ka gani a nanne zaka shigar da lambobin da suke jikin takardar, idan kuma baka gane yadda zaka shigar ba sai ka tambayi masu kula da wurin, sai su nuna maka yadda zaka shigar, bayan kazo ka zauna, zaka duba inda aka rubuta (misali click here to enter a password), zaka ga wurine da dogon layi. Kamar yadda nayi bayani a baya, sai kazo cikin layin kayi click (ka danna mouse) sai ka kwafe password (lambobin jikin wannan takardar) zuwa cikin wannan dogon layin (idan kana rubutawa yanwaci zaka ga wannan alamar **** kada ka damu sai kaci gaba da rubutawa ) bayan ka kwafe sai kayi click akan login, ko kadanna ENTER a jikin kibod, kana dannawa zata bude maka DESKTOP, misali kamar haka:-
wanan wurin shi ake kira Desktop duk lokacin daka bude kwamfiyuta shi zaka gani wadannan abubuwan kanana dakake gani su ake kira Icons, icons ankasasu kashi uku ne ko fiye akwai fayils, akwai foldes akwai programs, kuma kowanne akwai aikinsa a cikinsu daya zamu dauka wanda dashi ne ake shiga Intanet. Wato zaka ganshi karamar e anzagaye ta

YADDA ZAKA BUDO  WEB-BROWSER KA SHIGA INTERNET


Bayan ka budo desktop, sai kaduba inda aka rubuta daya daga cikin wadannan:-  Internet Explorer, Fire Fox, Opera, Netscape Navigator, SeaMonkey, Mozilla Firefox, uBrowser, CompuServe. Da kaga daya daga cikin wadannan sai kayi double click (kaje da pointa kan wurin ka danna mouse sau biyu), idan ba kaga ni ba sai kaje can kasa gefen hagu zaka ga inda ka rubuta START , bayan ka danna sai kaje wurin kayi click, bayan kayi click sai ka duba inda aka rubuta Intanet Explorer,
 sai kayi click akan wurin, idan kuma baka ga kowanne ba sai ka tambayi masu lura da cyber cafĂ© din.  Bayan kayi click akan Intanet Explorer zakaga ta bude maka shafi kamar haka:-


wannan shine mislain shafin yanar gizo na Yahoo, to yanzu ka shiga intanet ke nan, kafin muje gaba, zan sake kara bayani ga me da Internet Explorer. Microsoft  Intanet Explorer ita ce web browser din da tafi sauki wurin shiga Intanet, kuma yawancin kowace cyber cafĂ© kaje zaka samu suna da Intanet explorer, don haka ko yaushe kaje browsin sai ka duba Intanet explorer a desktop. Kuma ita Intanet explorer software ce, wani zai iya yin tambaya yace wai mene Intanet explorer ko mene software, kuma mutane da yawa suna mamakin wai ta yaya Kwamfiyuta take aiki, har idan bakayi abu daidaiba ta gyara maka, harma kaga tana maka gargadi. Da farko kafin inyi bayani game da wannan, ya kamata kasan mecece Kwamfiyuta Softwaya din  ?, kamar yadda na yi bayani a farko, to ita dai Kwamfiyuta duk abin da kaga tanayi to wannan abin sa mata akayi, duk wani gargadi da kaga tanayi, to mutum ne yazauna ya shirya mata, mutumin da yake shirya wa kwamfiyuta program shi ake kira Programmer, abin da ake shirya mata shi ake kira programs,  sannan program din ake harhada wa a shirya mata, sai ake kiransu Software, sannan ita kwamfiyuta ta dogara ne da irin programs din da aka saka mata sannan zaka ji ana cewa kwamfiyuta tana da virus, to wannan virus din shima shiryashi akeyi sai a yada shi, sai kuma a kero magani wato Antivirus. Sannan za’a iya shiryawa kwamfiyuta kowane softwaya, ko kaima inka iya programming zaka iya shirya Kwamfiyuta program na Hausa, idan ka saka mata program din da ka shirya zakaga kowane abu da zata rinka nuna maka da hausa zakaga tana yi, har gargadi duk da hausa, tambaya ma da hausa, sabo da kashirya mata da hausa, misali kanason ka kera programs na kwamfiyuta wanda zai rinka yin yin hausa in mutmu ya taba wani madanna ga yanda zaka kera karamin  programs din:- da farko zaka budo Microsoft Word a kwamfiyuta bayan ka bude sai ka danne Alt sannan ka danna F11 zaka ga wani windows ya bude sai kaje kayi click din insert a can menu bar sannan kadanna UserForm zaka ga wani form ya fito sai kaje inda aka rubuta toolbox kaduba inda aka rubuta commandbutton sai ka danna bayan ka danna sai kazio ka zana shi akan wannan UserForm din bayan ya fito sai kayi double click akansa bayan kayi sai ka rubuta msgbox “Me yasa ka danna wannan madannin kada ka kuskura ka sake dannawa, danna OK ka batarda ni” bayan ka gama rubutawa sai ka danna ENTRE a kibod, yanzu ka gama tsara mata idan kana son kayi run din Program sai ka danna F5 a jikin kibod zaka gat a kawo maka wannan Form din sai ka danna inda aka rubuta CommandButton1 kana dannawa zakaga ta rubuto maka abin da kabata umar nit a rubuta tace maka me yasa ka danna wannan madannin  kada ka kuskura ka sake dannawa, danna OK ka batarda ni. Bayan ta nuna maka wannan abin kana danna ok zaka ga abin ya bata kaga anan kayi programming, wato ka koya wa kwamfiyuta cewa idan aka danna wannan madannin to sako ya fito(msgbox) sannan sakon yace abu kaza, to wannan kadan ken an daga cikin programming, idan kanason kakoyi programming zaka iya ziyartar shafimmu na yanar gizo ko ka aiko mana da wasika zuwa emel dimmu, ko kanemi littafimmu dana rubuta da hausa mai koyarda yadda ake programming duba karshe wannan littafin. To kaga wannan abin shi ake kira software programming, wato a nan yawan abin da yake cikin kwamfiyuta  ya dogara  ne da irin yawan softwayar da aka saka mata, misali yanzu kana da handset kana son ka zuba mata wakoki, kuma wadannan wakokin suna cikin CD ne, kaga ita handset din naka ba zata iya daukan dukkaan CD, ba, ko kuma kai ba duka CD kake son ka dauka ba, kai dai wakokin ka keson ka dauka, to kaga anan idan ka saka CD a kwamfiyutarka sai ka Nemo softwayar yanka, wakoki, ka saka wa kwamfiyutar, sannan da wannan softwayar zaka budo CD ka zabi inda kake son ka yanke sai ka yanke, CD, ka mayarda shi MP3, sannan sai ka tura wa wayar taka, to kaga wannan duk aikin Softwaya ne. akwai softwayar da idan ka kunna kwamfiyutar ka saidai kaji ta fara karaun Alkur’ani. To kaga anan softwaya tana da matukar amfani a Kwamfiyuta. Sannan idan kana son Softwaya na Hausa irin wanda  muka shirya zaka iya aika mana da wasika zuwa email din mu, sai mu aiko maka da  adireshin yanar Gizon da zakaje kayi Download din wannan Softwaya din.  To kaga a nan Microsoft Intanet Explorer softwaya ce da zata baka damar Ganin shafuffukan Intanet, ne wanda kamfanin Microsoft take shiryawa.

YADDA AKE BUDE SABON ADIRESHIN EMAIL NA YAHOO
Bayan kaje cyber cafĂ©, ka siya time ambaka password ka shigar da password din ka budo Intanet explorer, (Misali=START—INTANET EXPLORER). Bayan ta budo maka wani shafi, Sai ka duba can sama kusa da inda akarubuta Address, sai kazo kayi click a  kan wannan dogon layin, karubuta, misali:-  www.yahoomail.com   kamar haka:-

bayan ka rubuta saika danna Go ko ENTER. Bayan ka danna ENTER zaka ga ta bude maka wani shafi
Bayan ta budo maka shafin, sai ka duba inda aka rubuta sign up sai ka danna wurin sai kayi click bayan kayi click sai kajira shi zai kawo maka form din yahoo registration, bayan ya kawo maka form din yahoo registration, sai ka cike shi, bayan ka cike a karshe zaka ga inda aka rubuta SUBMIT ko inda aka rubuta I agree sai kayi click din wurin, bayan kayi click  zaka dan jira har sai kaga ta kawo maka
wani sabon shafi an rubuta Registration Completed. Kamar haka

YADDA AKESHIGA ADIRESHIN E-MAIL

Shi E-Mail adreshi zaka iya bude shi a wurare da dama kamar haka   a: yahoo.com  ko  hotmail.com  ko mail.com   ko lycos.com ko  netaddress.com ko email.com   ko 37.com. Kamar  yadda nayi bayani a baya, bayan kaje cyber cafĂ©, kaje ka budo Intanet explorer, zaka zo kusa da inda aka rubuta address, sai karabuta www.yahoo.com bayan karubuta sai ka danna Go  za’a budo maka wani shafi, bayan shafin ya bude, sai kazoo gaba da  inda aka rubuta yahoo ID,
anan sai karubuta email dinka ba dole bane sai kasa @yahoo.com, bayan ka rubuta sai kadanna TAB ajikin kibod, ko kayi click gaba da inda aka rubuta password sai karubuta password dinka, bayan karubuta sai kayi click akan Sign in   sai kajira yabude, bayan yabude zai budo maka wani shafi zaka ga anrubuta Wellcome wane,  shafi  kamar haka:-


idan kuma be bude ba, to kayi kuskuren wani harafi daga cikin emel dinka ko password sai ka sake rubutawa .

IDAN ZAKA KARANTA WASIKA

Idan zaka karanta wasika, sai kayi click Akan inda aka rubuta inbox, ko kuma CHECK MAIL ko inda aka rubuta You have xx unread message

sai kayi click akan wurin, bayan kayi click, zata jero maka wasikun dakake dasu sai kazo, kan wasika, (kan abin da wasikar ta kunsa) sai kayi click, kana yin click zaka ga wasikar ta bude sai ka karanta.

 

RUFE WASIKA BAYAN ANGAMA KARANTAWA

Bayan ka gama karanta wasika, idan zaka goge sai ka danna DELETE zaka ganshi a saman wasikar ko a kasan wasikar, in ka gama karanta wasikar sai ka danna CHECK MAIL ko INBOX.

IDAN ZAKA RUBUTA WASIKA

Lokacin daka bude email dinka, idan wasika zaka rubuta sai kazo sama bangaren hagu zaka ga inda akarubuta COMPOSE 
sai kayi click bayan kayi click zai bude maka wani shafi kamar haka:- inda aka rubuta To sai karubuta Adireshin Emel din wanda zaka aika wa wasikar misali:- mannirgetso@yahoo.com  sai ka danna TAB ajikin kibod, inda aka rubuta Subject kuma sai karubuta abin da wasikar ta kunsa, sai kayi click acikin shafin da zaka rubuta wasikar sai kafara rubuta wasikarka

Kara girman rubutu

Idan zaka rubuta wasika kana son ka kara girman rubutun, zaka duba sama kadan cikin inda kake rubuta wasikar, zakaga wata alama karamar A, da babban A da karamar A, inkaje wurin kafin ka danna zakaga an rubuta Front Size sai kayi click akan wurin, sai kazabi girman rubutun dakakeso.

Sa kala a rubutu

Idan kanason ka sakawa rubutun dakake yi kala, za kaje jerin layin daka dauko na baya, inda kaga anyi wata alamar T , kafin kayi click zakaga an rubuta text colour, sai kayi click din wurin, zakaga ya  kawo maka kaloli, sai ka zabi kalar da kakeso, kayi click akan kalar.

Saka hyperlink a rubutu

Shi hyperlink rubutu ne, wanda idan ka danna rubutun zai kaika websites(shafin yanar Gizon) da aka rubuta a jikin wannan hyperlink din, misali wani abokinka ne baisan website din Google ba sai kana son ka aika masa da website ta cikin email dinka, sai kazo jerin wurin da ka dauko sauran, zakaga inda akayi hoto kamar alamar duniya da wani abu kamar ankwa ajiki, kafin kayi click zaka ga an rubuta create hyperlink sai kayi click akan wurin, amma farko sai karubuta website din, misali Google  (sai kayi highlight dinsa)  yanda kuwa ake halayit kuwa shine, bayan karubuta Google sai kasa mouse dinka kafin G sai kadanne sai ka ja harzuwa e (wato e din karshen Google) zakaga rubutun yayi baki, sai kaje wurin creat hypalink kayi click sai karubuta website din misali  http://www.google.com sai kadanna ok, duk a cikin wasikar zakayi wannan.

Sa Attach File

Attach file ana sakashine idan kanson ka aika da hoto ko wani file(fayil, takarda) daga Kwamfiyutar da kake, zuwa emel din wani, idan kanason ka aika da attach file lokacin daka budo wurin rubuta wasika zakaga wani wuri anrubuta Attach files sai kayi click a wurin zai budo maka wani shafi, sai kayi click akan browse , bayan kayi click, saika zabi file din da kakeson ka aika bayan kayi click akan file din sai kayi click akan open  sannan sai kayi click din attach files  sai kajirata ta gama loda (diban) file din sai kayi click akan continue message sai kaci gaba da rubuta wasikar ka.

AJIYE WASIKA A DRAFT

Idan kana rubuta wasika sai baka gama ba kuma kaga lokacin da kasiya na Intanet ya kusa karewa, ko kana son ka ajiye wasikar ba yanzu kakeson ka aika wasikar ba, zaka iya aiye ta a draft(wurin ajiye wasiku), lokacin da kadawo kaci gaba da rubuta ta sannan sai ka aika, yadda zaka ajiye abu a draft shine, lokacin da kake rubuta wasika idan ka duba saman wasikar zakaga inda aka rubuta SAVE AS DRAFT to nan zakayi click sai ta ajiye maka wasikar duk ranar da kashiga Intanet sai kaci gaba gaba da rubuta wasikar.
            Duk lokacin daka zo kabude email dinka, idan zaka budo wasika daga DRAFT saika duba inda aka rubuta DRAFT sai kayi click din wurin bayan kayi click din wurin zaka ga ta budo maka jerin wasikun daka ajiye su a draft sai dai kawai kayi click akan wasika kaci gaba da rubutata. Lokacin daka gama rubuta wasika gabadaya, sai kazo inda aka rubuta To:  sai ka rubuta adireshin wanda zaka aikawa da wasikar awurin, misali  To:  manniru@gmail.com  idan kuma zaka aikawa da mutane da yawa sai ka rubuta email din na farko sai kasa comma “  ,  “  misali zaka aikawa da mutum uku mannirgetso@yahoo.com,sagir13131@yahoo.com,manniru@gmail.com  haka zakayi ta jera sunayen email din kana raba su da kwama. Bayan ka gama rubutawa sai kaduba sama zaka ga inda aka rubuta SEND sai kayi click akan wurin, idan wasikar ta tafi zata nuna maka  Message Send,

IN ZAKA GOGE WASIKA

Kamar yadda nayi bayani da farko I dan kana sonka goge wasika sai ka danna DELETE ko kayi check (ka zabi) wasikun da zaka goge wato kayi musu good (wani dan box, a kwati zaka gani lokacin da ka bude wasikunka a wannan karamin box din sai kazo cikinsa kayi click ) , bayan kayi check din ko wace wasika sai kadanna DELETE zai goge maka wasikun dakayi check dinsu.

YADDA ZAKA NEMO WASIKA

Misali wani abokinka ya aiko maka da wasika acikin wasikar ya aikoma da lambobin scratch card na NECO sai bakaga wasikar ba, saboda kana da wasiku da yawa, kuma ya turo wasikar, to lokacin da ka budo E-MAIL din ka zakaga inda aka rubuta  SEARCH MAIL a hagu a wurin zakaga wani dogon box(layi) sai kayi click acikin sai ka rubuta NECO ko karubuta PIN bayan ka rubuta sai kayi click akan SEACH MAIL, in dai wasikar tana email dinka zaka ga ankawo maka ita, sai kayi click akan wasikar, zaka gat a bude.

 

YADDA ZAKA DUBA SAKAMAKON JARRABAWA TA INTANET (NECO, WAEC, KO JAMB)


Idan kanason kaduba sakamakon jarrabawarka ta NECO, WAEC ko JAMB ta cikin Intanet, da farko bayan kaje kasiyo katin duba sakamako ta Intanet (wato Scratch card na WAEC, NECO, Ko JAMB) sai kaje cyber cafĂ©(dakin shiga Intanet), bayan kasiya lokacin da kakeson kayi a Intanet na minti talatin ko na awa daya (minti 30 N60, awa daya kuma N100 (ayanzu)), bayan kashigar da password kabudo desktop saika bude Internet Explore, saika duba sama gaba da inda aka rubuta Address sai kayi click akan wannan dogon layin sai karubuta adireshin da yake jikin katin duba jarrabawar, misali www.waecdirect.org ko www.necoonline.com . Bayan karubuta sai kadanna Enter ajikin kibod ko kayi click akan  GO a gaban inda karubuta adireshin, bayan ya bude maka, sai kacike wasu gidaze zaka gansu yawanci a bangaren Dama (wato zaka zabi shekarar da kayi jarrabawar, sai karuta lambar jarrabawarka sai karubuta, lambar katin da kuma PIN na katin duk acikin wannan gidan zaka rubuta su). Bayan ka gama rubutawa sai kadanna SUBMIT.

YADDA ZAKA FITO DA SAKAMAKON JARABAWARKA DAGA SHAFIN YANAR GIZO-GIZO (PRINT)
Bayan ka budo sakamakon naka sai kazo kan shafin kayi Right-Click(wato kadanna Mouse amma bangaren dama zaka danna) bayan kadanna zaka ga anjero maka wasu abubuwa a wadannan abubuwan sai kaje inda aka rubuta Print sai kayi click akan wurin, bayan kayi click wani dialog kamar haka:-
 Bayan yabudo maka sai ka zabi sunan printa sai kadanna Print ko ka danna ENTRE (in baka ganeba sai katambayi masu cafĂ© din. Ko shafi kakeson kayi print haka zakayi.

KOYI YADDA AKEYIN CHATTIN

MENE CHATTING?

CHATTING wata hanyace da zakayi magana da mutum ta hanyar rubutawa juna sako ta rubutu dakuma ta hanyar sauti da kuma gani, wato zaku iya magana da mutum kana ganinsa shima yana ganinka kuma kowa yana jin maganar dan uwansa.
Kuma a chatin zaka iya haduwa abokai daga kasa she dabam dabam na duniya. Kuma shi chattin amfi yawan yinsa ne ta hanyar rubutawa mutum sako ta rubutu, misali ka hadu da wani dan SAUDIYA sai ka rubuta masa Assalamu Alaikum, a lokacin shima zai rubuto maka, Wa’alaikumussalam, a haka zaku yi ta magana dashi, idan yana da webcam(abin da zaka iya ganin sa)  to zaka iya ganinsa, idan kaima kana da webcam zai iya ganinka,

ME AKEYI A CHATTING?

Abubuwan da akeyi a chattin suna dayawa, ga kadan daga ciki :-
Kasuwanci. haduwa da Malamai na BOKO (lectures, prof. da sauransu). Haduwa da abokai daga kasashe dabam dabam. Yin aiki (na cika form, typing da sauransu), ana biyanka. Mitin(kamar wata ma’aikata zata iya yin mitin idan ma’aikatan(masu aikin) nata suna nesa da juna. Da sauransu.  Yawancin  abubuwan da akeyi anayinsu ne ta hanyar aikawa da sakonni ta rubutu Magana(VoIP), da kuma gani(webcam).

YADDA AKE SHIGA CHATTING (YAHOO MESSENGER)

Shi chattin daban yake da E-Mail da Browsing, shi bayan ka budo Desktop (bayan kashigar da lambobin jikin takatdar da kasiya), maimakon ka danna Intanet Explorer, shi sai dai ka danna YAHOO MESSENGER, zaka ganshi a kan desktop ko idan ka danna START—YAHOO MESSENGER, idan baka ganshiba sai ka tambayi masu kula da cyber cafĂ© din, kuma shi double click(sau biyu zaka danna ) (kada ka manta duk lokacin dazakayi click akan yahoo messenger ko waninsa ka dena click akan rubutu akan hoton zaka rinka click). idan kayi double click akan Yahoo Messenger zai budo ma hoto kamar haka:-
bayan ya budo maka, sai karubuta email dinka a gaban inda akasa Yahoo ID, amma idan kazo rubuta emai din badole sai ka saka @yahoo.com Kwamfiyuta tasan at yahoo.com ne, bayan ka rubuta sai kadanna TAB a kibod, ko kasa mouse kayi click a gaban inda aka rubuta PASSWORD anan sai karubuta password dinka, kamar dai yadda kake shiga email, bayan kagama sai kadanna Sign in ko kadanna ENTER duk wanda kadanna daidai ne, bayan ka danna sai ka jira ya bude maka, bayan ya bude maka kamar haka:-

bayan yabude maka saika duba can sama inda aka rubuta Messenger sai kayi click akan wurin sannan kayi click din YAHOO CHAT  sannan JOIN A ROOM,

 idan baka ganeba to ka duba sama inda akayi wani abu kamar alamart hoton Wayar Salula (Handset) da kan telephone akan layin idan kaduba bangaren dama zaka ga wani alamar kibiya (arrow) guda biyu kamar haka irin wannan guda biyu ®, idan kaje kan arrow din sai kayi click, bayan kayi click sai kayi click akan CHAT sai kajira shi yabude, in bai bude ba, sai kasake zuwa wurin wannan arrow din ka sake click, har ya budo maka.

YADDA ZAKA ZAFI CATEGORY DA ROOM KASHIGA

Bayan ya bude zaka ga ya budo maka wani windows, zaka ga jerin CATEGORIES sai kazabi category din da zaka shiga sai kayi click (misali= SCHOOL & EDUCATION),  bayan kayi click zai sake jero maka jerin ROOMS anan ma sai ka zabi room din da zaka shiga

 (misali:- study group), bayan kayi click sai kadawo kasa zaka ga inda aka rubuta Go to Room sai kayi click, zaka ga yabudo maka wani windows zaka jira har wani dogon abu yacika bazai wuse sakan 10, sai kayi click akan Enter Chat.

YADDA ZAKA GA YAWAN MUTANEN DA SUKE CIKIN CHAT ROOM

Bayan kadanna ENTER CHAT zakaga ta budo maka chatroom din kamar haka:-

idan ka duba bangaren dama, zaka ga Email din wadanda suke cikin dakin ne. Idan kaduba wadanda suke bangaren hagu kuma zakaga wadansu kamar sunsa headphone, wasu kuma kamar suna cikin tibi, wasu kuma ba komai. Wadanda suke da abu kamar headphone zaka iya magana dasu, wato suna (voice chat VoIP(Voice Over IP). Su kuma wadanda suke cikin tibi, zaka iya ganin su kamar a TV, wasu kuma har zaka iya ganinsu kayi magana dasu. Idan kana son Karin bayani yadda zaku yi Magana da mutum kana ganinsa  shima yana ganinka ta cikin Intanet ka ziyarci shafimmu na yanar Gizo-Gizo a  http://www.mannir.8m.com

YADDA AKE DUBA MUTANEN DA SUKE CIKIN CHAT ROOM DA IRIN ABUBUWAN DA SUKE RUBUTOWA

Idan kaduba bangaren dama, nan kuma zakaga rubutu nata fitowa (misali mannir: joint the room), wato anan nunama yanzu mannir ya shigo dakin chatin din kenan, kuma a nanne zakaga kowa na rubuto abin da yaga dama  (misali mannir: akwai wani ba haushe kuwa?),  to anan ne idan kana son kayi wa mutum magana sai kaje kan email dinsa kayi double click akai(ka danna mouse sau biyu).

YADDA AKE TABO MUTUM A CHATTING

A bagaren dama zaka iya ganin wanda kasan email dinsa, ko wani wanda kake son kuyi cattin dashi, yanda zakayi shine kaje kan email din mutum a bangaren dama kayi click, sannan sai ka dawo kasa  kayi click akan inda aka rubuta IM, bayan kayi click zaka ga wani window ya fito, to a wannan window din zaka rinka rubuta abinda da kakeson ka fadamai, misali Assalamu Alaikum, sai ka danna Enter ko Send, misali zaka iya rubuta mai Hi sai kayi send ko kadanna ENTER a jikin kibod.

YADDA AKEYIN CHATTING

Bayan kayi click akan ID(Yahoo ID) din mutum, kuma ka yi click akan IM,  bayan wani window ya fito kamar haka:-

sai kazo nan kasa sai kayi click, sai karubuta Hi, sai ka danna SEND ko kadanna ENTER, sai kajira kaga reply, yana dawo da reply zaka ga bottom toolbar yayi ja,  kamar haka:-
 sai kayi click akan wurin. Idan anyo maka Reply misali  sager:Hi ko  asl?, idan kaga plz asl?, yana tambayarka shekarunka nawane, sannan kai namiji ne, ko mace ce, sannan a wane gari kake, shine ma’anar asl, idan kanason kaga ma’anonin irinsu kaziyarci shafimmu na yanar gizo, kaga ta haka zakuyi ta communication(Magana) da mutum.

WASU KALMOMIN CHATTING DA MA’ANONINSU

Akwai kalmomin da ake amfani da su a wurin chattin don rage dogon rubutu, misali:-
Name? = yaya sunanka, Ko yaya sunan ki.
Age? = shekarun ka/ki nawa.
Country? = a wace kasa aka haife ka/ki ?.
Location? = a ina ka/ki ke yanzu.
Asl? = shekarun ka/ki nawa, na miji ne kai ko ke mace ce, a ina ka/ki ke yanzu?.
Asl plz? = don Allah shekarun ka/ki nawa, na miji ne kai ko ke  mace, a ina kaki ke yanzu.
M/f? = Namiji ne kai ko mace ke.
U? = kai kafara Magana ko kaifa?
?chat = kanason muyi chat
??? = Ban gane abin da ka ce ba
R? = sake gyara abin da ka rubuto
Webcam? = zan iya ganin ka/ki
Voice? = zan iya Magana dake
Mic ? =ka/k nada abin Magana, ko zan iya jin maganar ki/ki
Busy = aiki na ke yi sosai
?? = ina da tambaya
link? = kana da wani shafin yanar gizo
web? = kana da website na kan ka
Dasauransu.
A lokacin da kuka fara chattin da mutum zaka iya ganin ya rubuto maka:- asl?, wato yana nufin kai waye, namiji ne ko mace kuma shekarunka nawa, kuma a wace kasa ka ke ko kike kamar yadda nayi bayani da farko. Akwai abubuwa da dama da ake rubutawa wurin chattin nan kadanne daga cikin su kenan.

IDAN KAYI ABOKI KANASON KA AJIYE SHI A MESSINGER LIST

Idan kuna cattin da mutum sai kanason ka ajiye shi a messenger list(wurine da zaka ajiye email din mutane), yadda duk lokacin daka shiga yahoo messenger zaka iya gane mutum yana cikin chattin ko baya nan), lokacin da kuke chattin da mutum idan ka duba saman dakin shi wannan mutum zakaga wani hoton kamar kai, anyi alamar Tarawa ajikin kan, to nan zaka zo kayi click, zaka ga ya bude maka, wani window sai ka danna next har sau biyu na karshen sai ka danna Finish, bayan ka gama zakaga sunan email dinsa a jikin yahoo messenger dinka, kuma zaka iya zuwa da Email adireshin wani , ka ajje a messenger list, kamar yadda zanyi bayani nan gaba.

YADDA ZA’A AJIYE E-MAIL DIN MUTANE A MESSENGER LIST

Zaka iya samun Email adireshin abokinka ka ajiye shi a messenger list yadda duk lokacin da kashiga Intanet, zaka iya ganewa shima yana kan Intanet(chattin) ko bayakai, misali ka samo email adireshin mannirgetso@yahoo.com   idan ka budo yahoo messenger sai kaduba inda aka jera hoton su Wayar Salula(Handset) da sauransu zaka ga wani abu Kamar alamar kan mutum da alamar Tarawa ajikin abin sai kayi click a wurin zai bude maka wani wuri, sai karubuta email adireshin bayan ka rubuta sai kadanna next har sau biyu daga karshe sai ka danna finish, zakaga email dinsa ya fito a cikin yahoo messenger dinka.

YADDA ZAKA GANE ABOKINKA YANA KAN INTANET KO BAYANAN

Duk lokacin da kashiga yahoo messenger, idan ka ajiye Email adireshin mutane a messenger list, to a farkon sunan kowa zakaga hoton wani abu kamar kan mutum, to duk kan da kaga yayi kala wato yayi kalar dorawa to wannan mai Email din yana kan kan Intanet wato yana cikin chattin, wadanda kuwa kaga basu da kala to basa kan Intanet, ta haka zaka iya gane aboikinka yana kan Intanet  ko bayanan, idan bayanan zaka iya rubuta mai sako yadda duk lokacin da yahau Intanet zai ga wannan sakon daka aika masa. Idan kana son karubuta wa mutum sako zaka je kan adireshinsa na email saikayi double click bayan kayi double click sai kajira ya budo maka wani karamin window, bayan ya budo maka window din sai karubuta abin da kakeson aika masa, sai ka aika masa.

YADDA ZAKUYI MAGANA DA MUTUM KANA GANIN SA YANA GANIN KA

Idan kanason ka yi magana da mutum kuma kana ganinsa, da farko bayan kaje cyber cafe, zaka duba Kwamfiyutar da take da webcam idan kuma bata da webcam, sai ka tambaye su ko suna da webcam, da microphone/speaker , zasu sa maka shi a bayan Kwamfiyutar, bayan sun saka maka, bayan ka budo YAHOO MESSENGER, lokacin da kuke chattin da mutum idan kaduba saman dakin da kuke chatting din zaka ga inda aka rubuta action sai kayi click akan wurin, ko kuma file ka duba inda akarubuta webcam sai kayi click din nan, daga nan, zaka ga inda aka rubuta CALL
 sai kayi click akan wurin, sai kajira wancan ya amsa, idan shima yana da webcam, a nan kasa hoton wanine yana chatin da webcam ana ganinsa:-

 

YADDA ZAKA BINCIKO BAYANAI TA CIKIN INTANET

A wannan bangaren zanyi bayani a kan yadda ake nemo bayanai ta Intanet, misali yadda zaka nemo assignment(aiki) ta Intanet. A wajen nemo abu acikin Intanet ana amfani da wasu abubuwa guda biyu wadanda ake kira:- Directories   da  Search Engines.
Shi  Directoies ana amfani dashi wurin nemo wani abu kebantacce, misali:- abu ya shafi magana ne ta Doctors(Likitoci), ko Kwamfiyuta Programmers, ko Engioneer, ko gyaran wayar salula ko softwaya,  da sauransu, to idan zaka nemo abu, ya dangantane da abinda kake nema, idan abin da kake nema ya danganta ne da wani abu kamar yadda nayi bayani, to zakayi amfani da DIRECTORIES wurin nemo bayanan ka, misalan adireshin DIRECTORIES kuwa sune:- www.searchsystem.com www.directories.goole.com  www.dir.yahoo.com . idan kanason cikakken bayani gameda DIRECTORIES ko kuma jerin sunayen Adireshin directory, ka ziyarci shafin mu na yanar gizo wato http://mannir..8m.com .
                    Da farko Idan zaka binciko bayani ta cikin Intanet zaka  iya nemo bayanin da hausa I dan abin yashafi hausa, sannan zaka iya nemo shi da turanci, misali zaka iya tambayar “Labarun BBC hausa” sai akawo maka Labaran BBC Hausa.

MENE SEARCH ENGINES?

Search Engines wasu Websites(Shafin Yanar Gizo-Gizo) ne wadanda an tanadesune don binciko abu a Intanet, a nanne za kaje karubuta abin da kake nema, sai su binciko maka abin da ka nema cikin kankanin lokaci. Yawanci idan ka budo search engines zaka ga akwai wani dogon layi wanda acikin wannan dogon layi zaka rubuta abin da kake nema, bayan ka rubuta sai ka danna ENTER.
Nan kasa misalin shafin Binciko bayanai ne na Google an nemo bayani akan labaran safe da hausa.

ADIRESHIN WASU SEARCH ENGINES

ALTAVISTA , GOOGLE  zanyi bayaninsu nan gaba
ASKJEEVES = Shima wannan shafin bincike, shima yana daga cikin adireshin da zakaje karubuta abin da kake nema, yakawo maka, misali an baku assignment a makaranta anan ne zakaje karubuta abin da aka tambayeku ya kawo maka bayani akan abin

WASU MANYAN SEARCH ENGINES

Su wadannan search engines su ake kira meta search engines, su idan kasa su nemo maka wani bayani, suma zasu tattaro bayanan da sauran manyan search engines su nemo musu, saisu kawo maka abin da kowane search engines ya nemo, kadan daga cikin su kuwa sune:-

YADDA ZAKA BINCIKO WANI BAYANI A GOOGLE

Idan zaka budo Google, zakazo layin gaban inda akarubuta Address sai karubuta www.google.com sai kadanna Go ko kadannna ENTER, A wannan dogon layin daka gani ananne zaka rubuta duk abin dakake nema,bayan karubuta abin dakake nema sai kadanna ENTER. Misali kana neman Labaran Hausa ne a Intanet, bayan kabudo google sai kazo dogon layin nan kayi click sai karubuta “labaran hausa” bayan karubuta sai kayi click akan Google search, ko ka danna ENTER, bayan kayi click sai kajira yabudo maka abin daya nemo maka, idan yabudo maka zakaga wasu rubuce rubuce dabam dabam, to anan sai karinka karanta kanun bayanan, idan kaga irin bayanin dakake nema sai kayi click akan tushen labarin (inda kaga anja layi ko inda kaga kalna rubutun bulu), ko kayi click a inda kaga anrubuta Catched, bayan ka danna zai kawo maka websites din dasuke dauke da labaran hausa, anan sai kazabi inda kake so kaje, idan kaje kaga ba irin bayanan dakakeso bane sai kadanna Back zaka gansi acan sama bangaren hagu, idan ka danna zai dawo dakai baya, sai kasake zaban inda zaka, sai kayi click. Misali dakaje Google sai karubuta Mannir Ahmad zakaga yakawo maka shafi kamar haka:-


Amfani da alamar  “   “  =sai kuma abu na biyu, lokacin daka nemo wancan zakaga ya kawo maka website din da akayi magana akan Mannir  daga baya kuma akayi magana akan Ahmad, to saboda magance irin wannan matsalar zaka iya amfani da wadannan alamun “  “ , yanda zakayi shine kafin karubuta abin dakake nema sai kafara dannan wanan alamar (  “  ), (yadda ake dannata shine zaka danne SHIFT sai kadanna alamar tana nan kusa da Enter), (kamar haka “labaran safe” ), bayan karubuta abin dakake nema sai kasake danna ta, bayan kagama sai kadanna ENTER, zai kawo maka shafunkan da asali akayi magana akan “labaran safe” . Abin dazaka lura anan shine, misali kana neman inda akayi maganar Mannir Ahmad ne a Intanet, idan kaje google karubuta Mannir Ahmad baka sa wannan alamun ba to zai kawo maka websites da akayi magana akan Mannir daga baya kuma akayi magana akan Ahmad, amma idan kasa wannan alamun zai kawo ma asali inda akayi ayi magana akan “Mannir Ahmad”. Binciken abu a Intanet yana bukatar sanin ka’idojin bincike domin sai kaje kata bata lokaci baka samu takamaimai abin dakake nema ba, domin Karin bayani gameda yadda ake nemo abubuwa ta Intanet ka naimi littafin mu da muka rubuta mai koyar da yadda ak bincike ta Inttanet.

YADDA ZAKA NEMO HOTO A GOOGLE

Idan hotuna kakeson kanemo, kamar hotunan Wayar Salula (Handset) ko na gidaje kowane irin hoto dai, farko bayan ka budo www.google.com, saI kaduba saman dogon layin zaka ga inda aka rubuta Images
sai kayi click akan Images din, bayan kayi click, misali kanason hadset na Samsung, sai kaje kayi click akan dogon layin, sai karubuta Samsung mobiles  kana rubutawa sai kayi click akan search, ko kadanna ENTER, zakaga an kawo maka hotunan Wayar Salula (Handset) na Samsung iri-iri, to misali ace kanason kasiya Wayar Salula (Handset) ne, kana son kasan kudin Wayar Salula (Handset) din idan kazo zaka rubuta “Samsung mobiles”+price sai kadanna ENTER, idan aka kawo maka hotunan, sai kazabi iri wacce kakeso sai kayi click, za’a kaika inda aka fani farashinata. Misali kanason kasiya nokia 6600 ne zaka rubuta haka:- nokia mobile+6600+price+Nigeria idan karubuta sai kadanna ENTER, zakaga ankawo maka hoton Wayar Salula (Handset) din sai kayi click akan Wayar Salula (Handset) din zaka, zaikai ka inda akafadi farashin Wayar Salula (Handset) din a Nigeria.

YADDA ZA’A NEMO ABU A ALTAVISTA

Idan zaka bude altavista jaka je wurin address sai ka rubuta www.altavista.com bayan yabudo maka, sai karubuta abin da kake nema
Nan hoton marubucin wannan  Littafin ne da aka nemo daga Altavista.


Itama Altavista tana aikine kamar na google amma ta wani wurin tafi google amfani, amfaninta kuwa shine misali kanason akawo maka gaba daya websites din da MTN take dasu a Intanet to zakayi amfani da Altavista ne, farko yadda ake budo ta shine:- zakazo gabada inda aka rubuta Address sai ka rubuta www.altavista.com  bayan karubuta sai kadanna ENTER bayan ta budo maka shafin, sai kazoo kasa kadan zakaga inda akarubuta Worldwide sai kayi click din wani box(akwati) kusada wurin sannan kayi click din cikin dogon layin sai karubuta host:mtnonline.com bayan karubuta sai kadanna ENTER, zakaga ankawo maka gabadaya websites din MTN, idan kuma kanason websites din MTN dasuka yi magana akan GPRS sai karubuta  host:mtnonline gprs za’a kawo maka websites din MTN dasukayi magana akan gprs.
NB=IDAN KANASON CIKAKEN BAYANI GAMEDA YADDA AKE NEMO ABUBUWA A INTANET KA AIKA DA SAKO ZUWA:- manniru@gmail.com

YADDA AKE SHIGA INTANET TA CIKIN WAYAR SALULA (HANDSET)


Zaka iya shiga Intanet Ta cikin Handset, kayi Browsing, zaka iya download(diban) hotuna, wakoki, Games da kuma Application (kamar Qur’an a rubuce), da sauransu , kafin kafara shiga Intanet ta waya sai ka saita ta yadda zata rinka shiga Intanet din, sannan in glo ne zaka kira Customer care ka fada musu kanason kayi activate din Glo GPRS, in sunce , sannan sai ka saita wayarka yadda zata rinka shiga Intanet.

Yadda zaka saita Glo GPRS
Profile name= Glowap
Security=non-secure
Bearer= GPRS
IP Adress=010.100.098.022
UserName=wap
Password=wap
APN=glowap
Session mode= Permanent
Connection Security = off
Authentication = normal
Login type = automatic
Port no. = 9201 na HTML, ko 3130 na WAP
Idan kanason ka saita wayar ka tana shiga Intanet da farko sai ka saita handset din. In layin MTN gareka zaka aika sako ka rubuta SETTINGS kai aika zuwa 3888 zasu aiko maka da saitin. In kuma Layin GLO ga reka zaka rubuta sunan wayarka da lambar ta amma kada kasa space sai ka aika zuwa 927 da kuma 66, misali SonyEricsson P990i ka aika zuwa 927 da 667 na MMS. In kuma Vmobile gareka zaka rubuta wapgprs, ko wapgprs2, ko wapcsd, ko wapcsd2, ka aika zuwa 184, idan handset dinka tana daukan hoto (camera), sai ka kara 2 a gaban yazamo  wapgprs2, ko wapcsd2 in kuma babu sai karubuta wapgprs ko wapcd ba sai kasa 2 dinba.

Yadda zaka saita na MTN
YADDA ZAKA AIKA DA SAKO DAGA INTANET ZUWA WAYAR SALULA (HANDSET)
Akwai shafin yanar gizo-gizo da zasu baka damar aikawa da sakonni zuwa wayar salula, (Misali ka aika da sakon SMS daga Intanet zuwa wayar salula, idan kanason ka aika sako sai kaje shafin. Yawanci wasu shafin sai kayi rajista kyauta, bayan kayi rajista, zasu tambayeka lambar wayar ka, idan ka basu, zasu aiko maka da wasu code(lambobi), da wadannan code din zakayi activate din account dinka dakayi rajista dasu, bayan kayi activate din account din sai kafara aikawa da wasika, wasu shafin zasu baka kyautar aika sako sau biyar, ko goma harma  dari, wasu kuma zasu baka damar aikawa da sako sau uku a rana, misalin shafin da zaka aika da sako sune http://textnigeria.vsms.net kaduba karshen wannan littafin zaka ga sunayen wasu  safuffukan.

WASU KALMOMI DA MA’ANONINSU

·    INTANET EXPLORER = Softwaya ce da zata baka damar shiga da ganin shafukan da suke Intanet .
·    CHATTING = Hanya ce tayin magana ta hanyar rubutu da hannu ko Magana ko gani wato tadi, ana yinsa ne ta hanyar rubutu, ko sauti (magana), ko gani (kana ganin mutum) wato Webcam.
·    CLICK = Idan akace kayi click ananufin kadanna mouse dinka bangaren hagu zaka danna, kan rubutu ko hoto ko hyperlink, da sauransu.
·    DESKTOP = Wurine da, farko idan ka budo Kwamfiyuta shi zaka fara budowa, daga nanne zaka zabi inda kakeson ka shiga, misali in zakayi Browsing zaka duba Intanet Explorer, idan zakayi chattin zaka duba Yahoo Messenger.
·    DOUBLE CLICK = Ana nufin kayi click sau biyu a lokaci daya, da sauri zakayi click din, kuma bangaren hagu na mouse zaka danna.
·    E- MAIL = Shine kake amfani dashi wurin aikawa da wasiku da sauransu misalin Email shine:- manniruahmad@yahoo.com  .
·    Highlight = ana nufin ka zabi rubutu yadda kuwa akeyi shine zaka zo farkon rubutu saika danna mouse kada ka daga sai kaja a kan rubutun harzuwa karshen rubutun kada ka daga mouse din, idan kayi hailayit zaka ga zagayen rubutun yayi baki.
·    Hyperlink = Rubutu ne da ake rubutwa wanda idan kayi click akan rubutun, zai budo maka wani shafin Intanet na rubutun.
·    I M = Sako ne da zaka rubuta shi a chattin, daka rubuta shi zai tafi zuwa wurin wanda karubutawa kai tsaye, idan kana chattin da mutum daka rubuta mashi, zai gani shima ya rubuto maka martani.
·    MESSENGER LIST = Wurine a Yahoo Messenger da zaka ajiye email din abokananka, yadda duk lokacin da kashiga yahoo messenger zaka iya gane mutum yana kan Intanet ko bayanan,
·    PASSWORD = Wasu lambobi da kake amfani dasu wurin bude email dinka da wurin bude chatting da sauransu, in baka rubuta lambobin daidai ba kokamanta su, bazaka iya bude Email dinka ba.
·    SOFTWARE = Program ne da ake shiryawa Kwamfiyuta wadda shi Kwamfiyuta zata rinka bi, ta gane me akasata ko me zata yi.
·    WAP BROWSER = software ce ta Wayar Salula (Handset) wacce zata baka damar ganin shafukan Intanet ta cikin wayarka.
·    Yahoo ID = Email dinka da kake amfani dashi na yahoo wanda dashi zaka rinka shiga chattin ko email dinka, amma idan aka zo rubutashi, ana cire @yahoo.com, din misali email dina shine mannirgetso@yahoo.com to yahoo Id dina shine mannirgetso.
Idan kana son fassarar Wasu kalmomin Kwamfiyuta ko na kimiyya, Ka ziyarci http://mannir.8m.com/kimiyya

SUNAYEN WASU SHAFUFFUKAN YANAR GIZO-MASU AMFANI



Shafuffukan Bincike
www.yahoo.com
www.msn.com
www.google.com
www.altavista.com
www.ask.com
www.altheweb.com
www.search.com
www.dogpile.com
www.metacrawler.com


Shafuffukan Emel
www.yahoo.com
www.hotmail.com
www.gmail.com
www.aol.com
www.email.com
www.freemail.com
www.mail.com
www.lycos.com
www.netaddress.com


Shafukan Ajiya
www.streamloa.com
http://photos.yahoo.com
http://bookmarks.yahoo.com
http://briefcase.yahoo.com
http://spreadsheet.google.com
http://docs.google.com
www.filesanywhere.com



Shafuffukan Labarai
www.bbcnews.com
http://news.yahoo.com
http://www.voa.com
http://www.cnn.com


Littattafai
www.nigerianbooks.com
http://books.google.com
http://find.pcword.com/32480
www.audioquran.com/quran/quran
www.wikipedia.org


Shafuffukan Bincike Kebantacce
http://dir.google.com
http://directory.yahoo.com

Shafuffukan Nemo Hoto
http://image.google.com
http://images.yahoo.com

Diban Software (Downloading)
www.download.com
www.soft32.com
www.exefind.com
www.searchtruth.com
www.driverhq.com
www.emobilez.com/islam
http://example.microsoft.com/sample.asp


Maganin Kwamfiyuta (Antivirus)
www.symantec.com
www.symantec.com/securitycheck


Softwaya Kyauta
www.completefreesoftware.com
www.opensource.org
www.freewarehome.com
www.freewarefiles.com

Karatu
www.freeflashtutorials.com


Jarrabawa
www.waecdirect.org
www.necoonline.com
www.neconigeria.com

Sako zuwa waya (WEB2SMS)
http://textnigeria.vsms.net
www.ecall.com
www.textamerica.com
www.sendssnow.com
www.50sms.com
www.mobilemms.com
www.text-africa.com
http://freesms.1888usa.com/sms_global
www.smscountry.com
www.free-sms-message.com

Kere-Kere
www.electronicforu.com/electronicforu/lab
www.circuitguide.com
www.electronic_circuit_diagrams.com
www.discovercircuits.com


Wayar Salula
www.emobilez.com
www.emobilez.com/islam
www.emobiles.com/software/index.php
www.emobilez.com/secrets/
www.softwaregsm.com


Yanar Gizo-Gizo na waya (WAP)
http://wap.oa.yahoo.com
http://wap.pocketdoctor.co.uk
http://mm.yahoo.com
http://e-messenger.net
http://wap.google.com
http://dictionary.refrence.com/wireless/index.html
http://wap.emobilez.net
http://wap.getjar.com





RUFEWA


A nanne mukazo karshen wannan Littafi, dayake koyarda yadda ake shiga Intanet.
 Don Allah, duk kuskuren da aka gani, ko abin da ba’a gane ba acikin wannan littafi, za’a iya aiko mana da wasika zuwa adireshimmu na Email  manniru@gmail.com
Sannan kuma, wannan Littafin na rubuta shine saboda wadanda basu san yadda ake browsing ba (shiga Intanet), da kuma wadanda sunsani amma basu kwareba kamar yadda nayi bayani a farkon wannan Littafin din, Duk wanda ya riga ya fahimci wadannan, amma yanason Karin bayani, game da chattin ko bincike a Intanet, ko yadda zai rinka yin Browsing (shiga Intanet) ta cikin Wayar Salula (Handset) dinsa, Idan yanason wadannan bayanan zai iya ziyartar shafimmu a  http://mannir.8m.com  Ko ya binciki littattafan da na rubuta da Hausa wadanda sukayi bayani akan:-
BROWSING
EMAILING
CHATTING
SEARCHING ON THE INTANET
MOBILE INTANET

WASU DAGA CIKIN LITTATTAFAMMU
1.  AN INTRODUCTION TO VISUAL BASIC APPLICATION
2.  EXCEL PROGRAMMING WITH VISUAL BASIC APP.
3.  FUNDAMENTAL OF WEBDESIGN USING HTML
4.  AN INTRODUCTION TO WEB PROGRAMMING USING VSB/JS
5.  WEB DESIGN  PROGRAMMING WITH PHP & MYSQL
6.  UNDERSTANDING & USING COMPUTER SOFTWARE
7.  VISUAL BASIC PROGRAMMING
8.  JAVA PROGRAMMING
9.  PERL PROGRAMMING
10.     KOYI YADDA AKE SHIGA INTANET
11.     TRANSLATION OF SCIENTIFIC TERMS INTO HAUSA
12.     USING SCIENTIFIC CALCULATOR (HAUSA LANG.)
13.     FASSARAR KALMOMIN KIMIYYA
14.     INTRODUCTION TO WEBDESIGN & GRAPHICS
15.     KOYI YADDA AKE GYRAN NA’URA MAI KWAKWALWA
16.     ELECTRONICS PROJECTS
17.     KOYI YADDA AKE GINA YANAR GIZO
18.     KOYI DA KANKA ZANEN SOFTWAYA
19.     HOW TO DESIGN YOUR MOBILE GAMES & APPLICATION


WASU DA GA CIKIN SOFTWAYAR MU
1.        Mannir PL2
2.        Mannir PowerDVD
3.        Manir NetworkManager
4.        Mannir CyberLock
5.        Mannir SciCalc
6.        Manir C++ Builder
7.        Mannir J Editor
8.        Mannir CAD
9.        Hausa Word Prcocessing Sofwtare
10.     Hausa Taska (OS)

WASU SOFTWAYARMU NA WAYAR SALULA
1.        QUR’AN KARIM
2.        TARJAMAR ALKUR’ANI
3.        HADISAI ARBA’IN
4.        MANNIR KAMUS
5.        AHLARI
6.        MOBILE NOTEPAD
7.        HAUSA PUZZLE GAME
8.        MOBILE WORM
9.        KAWA’IDI
10.     LOKUTAN SALLAH

GARGADI
BA’A YARDA A BUGA WANNAN LITTAFI BA, TA KOWACE HANYA, BADA RUBUTACCEN IZININ MARUBUCINSA BA, HAKA KUMA BA’A YARDA A SARRAFASHI TA KOWACE IRIN HANYA BA


E.T.C
Duk Softwaya ko Littafin da kake bukata zaka iya aika mana da sako zuwa manniru@gmail.com, mannir@mannir.com ko ka ziyarci shafimmu na yanar gizo-gizo a www.mannir.com ko www.mannir.net www.mannir.org www.mannir.info  Ko www.mannir.com/hausa .


AKWAI VIDEO CD NA WANNAN LITTAFIN, YADDA ZAKA GA KOMAI A BIDIYO, ZAKA IYA SAMUNSA A WURAREN DA AKE SIYAR DA LITTAFIN
MANNIRMACRO DATA INFO.
C/D:9/21/2007 12:59:00 PM
E/T: 272
P/T :3/31/2007 4:25:00 PM
S/D: 10/18/2008 8:22:00 PM
F/S: 3944960
 

WASSALAM

10/18/2008 8:22:00 PM  3251712
By: - MANNIR AHMAD ADAM GETSO
3/31/2007 4:25:00 PM