MANHAJAR WAYAR SALULA TA TARJMAR ALKUR'ANI MAI GIRMA DA HADISAI ARBAIN
TARJAMAR MA'ANONIN ALKURANI MAI GIRMA
Download Link 1
Download Link 2
HADISAI ARBA'IN
Download Link 1
Download Link 2
Friday, July 19, 2013
Sunday, July 7, 2013
JERIN SUNAYEN LITATTAFAN KOYI NA Mannir Ahmad Getso
1. Koyi yadda ake shiga Intanet
2. Koyi yadda ake Gina shafin Yanar Gizo
3. Koyi yadda ake aiki da Na'ura mai kwakwalwa
4. Koyi yadda ake Zanan Softwaya
5. Koyi yadda ake Kasuwanci ta Intanet
6. Koyi yadda ake Kasuwancin Forex
7. Koyi yadda ake Gyaran Na'ura Mai Kwakwalwa
8. Koyi yadda ake Zanan Softwaya da Java
9. Koyi Yadda ake Zanan Software da VB
Koyi yadda ake shiga Intanet 1 (2007)
GABATARWA
Da sunan Allah mai Rahama
mai Jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzommu Annabi Muhammadu
(SAW); Godiya da yabo sun tabbata ga Allah (SWT), wanda bai haifa ba kuma ba’a
haife shi ba, mamallakin kowa da komai, Wanda ya halicci kowane abin halitta,
kuma ya bawa dan Adam damar kera abubuwan bam mamaki, kuma ya bashi fasahar
jujjuya abubuwan daya kera. Tsira da aminci su kara tabbata ga babban bawansa,
kuma masoyinsa, Annabi Muhammad (SWA); Bayan haka, na rubuta wannan Littafin ne
domin wadanda suke son su koyi yadda zasu rinka shiga Intanet, ko wadanda ayyuka
sun yi musu yawa, basu da lokacin da za suje makaranta su koyo yadda ake shiga
Intanet, kuma suna matukar son su koyi yadda zasu rinka shiga Intanet. Shi wannan
littafi zai koyar da kai yadda zaka shiga Intanet, kaduba wasika ko ka aika da
wasika ko kayi nazari ta Intanet, da sauransu. Zakaga a zamanin yanzu komai sai
kaga anayinsa ta Intanet, kamar Rajistar Jarrabawar WAEC, NECO, JAMB da
sauransu zakaga ta Intanet zakaje kayi rajista, da sauran abubuwa da dama, sannan
zakaga ko assignment aka baku a makaranta maimakon kaje Library(dakin karatu),
kayi ta bincike, baka samo abin da kakeso ba, to a yanzu sai dai ka shiga
Intanet karubuta abin da kake nema, sai kwamfiyuta ta binciko maka amsar abin, misali:-
kana neman ma’anar kwayar zarra(wato atom), misali kanason ma’anarta kamar kala
goma, kaga anan ko dakin karatu kashiga sai kasha wahala kasamo ma’ana goma, amma
idan ka shiga Intanet kaje shafin yanar gizo ta Google karubuta “Definition of
an Atom” zakaga kwamfiyuta ta kawo maka shafin yanar gizo-gizo kamar sama da
dubu tamanin da sukayi Magana akan definition na. Kaga in bata Intanet ba duk wadannan
bayanan ba zaka samu ba. Misali kullum kana jin labaran BBC Hausa amma baka
taba ganin hotunan masu labaran ba, to kana zuwa Intanet idan kaje shafin yanar
Gizo Gizo na BBC Hausa idan kabincika zaka ga Inda aka jero sunayen masu aikin
BBC Hausa. Kuma shi wannan Littafi akwai
Video CD dinsa, da zai koyar maka da komai kana gani ta bidiyo yadda zaka gane
komai a saukake, zaka iya samun Video CD dinsa a wuraren da ake sayar da
Littafin.
MANNIR AHMAD
GETSO
Saturday, March 31, 2007 3/31/2007
4:25:00 PM
ME NENE INTANET?
Intanet, dabarace ta hanyar
hada Kwamfiyuta da wata kwamfiyuta yadda zasu rinka musayar sakonni, wato yadda
za’a samu damar aikawa da karbar sakonni, da wasu abubuwa ta cikin kwamfiyuta a
kowace kwamfiyutar datake Kan Intanet, a duk inda take a duniya. Misali kwamfiyuta
tana nan Najeriya an hadata da Intanet sannan wata kwamfiyuta tana china ita ma
an hadata da Intanet to daga nan Najeriya zaka iya bude kwamfiyutar da take
china, ka karanta abubuwan da ke cikin ta, ko ka ika mata da sako na rubutu ko
na Magana, ko na hoto, ko na bidiyo da sauransu.
ME CECE YANAR GIZO-GIZO (WEBSITE)
Yanar Gizo-Gizo: - tarin
shafuffuka ne akan Intanet, akan wadannan shafuffukan ne rubutu yake, ko hotuna.
Akan wadannan shafuffuka zaka iya bincike, ko karatu, ko a aikawa da sakwanni
zuwa wata kwamfiyuta a duniya, a cikin dan kankanin lokaci, Ta haka zaka iya
aikawa da sakonni na sauti, ko na magana, ko na hoto, ko na bidiyo kona abu mai
motsi (animation) da sauransu, zuwa ko wacce Kwamfiyutar da kakeson ka aika, a
duniya. Misalin shafin yanar gizo-gizo shine anan kasa, Shafin Yanar Gizo-Gizone
na Muryar Amuruka:-

TA YAYA INTANET YAKE AIKI?
Shi Intanet yana aiki ne,
kamar yadda wayar salula ta ke aiki, misali idan kana da Wayar-Salula (Handset)
da lamba, da wannnan lambar zaka rinka aikawa da sakonni, ko karban sakonni,
misalin lambar waya sune 08051619043, to itama duk Kwamfiyutar da ka
hada ta da Intanet tana da lamba, wannan lambar ita ake kira, IP ADDRESS, (IP na nufin INTANET PROTOCOL). Kowace
Kwamfiyuta idan aka hada ta da Intanet tana da IP Adress. Misalin IP address
shine 192.168.32.1 Shi Intanet ta wurin aikawa da sakonni
yana amfani da wani abu wanda ake kira Intanet Protocol shi Intanet protocol shine yake nuna ina
DATA (information, wato bayanai) dinka ina zasu ko daga ina suke, misali:- ka
rubuta wasika a Kwamfiyuta ta 192.168.45.2 zaka aikawa zuwa 192.168.87.45(misali
Yahoo Server), idan zaka aika da wasika irin ta gargajiya(takarda) ba wai
zakaje ka ajiye wasikar a post office(wurin aikawa da wasika) bane, a’a, ana
bukatar karubuta adireshin da wasikar zataje. To shima haka Intanet protocol
yake a Intanet, yana da lambobi kashi hudu (a yanzu), kuma kowace lamba tana
kasa da 256, lambobin suna nan kamar haka: - 192.112.36.5 ko 128.174.5.6 Kaga lambobin farko suna nuna daga wane
irin network sako yake, na dama daga karshe suna nuna daga wacce Kwamfiyuta
bayanin ya fito, misali:- kana wata
cyber café(wato dakin shiga Intanet) a Kwamfiyuta ta 12 sannan network din su
shine 128 kaga IP naka zai zama 128.XXX.XXX.12.(X tana nufin wasu lambobi). Idan
baka gane misalin farko ba, ga wani misali ko zaka gane:- misali kana da Wayar
Salula (Handset), da lamba, sai ka rubuta sako ka aika wa wani, shi wanda ka
aikawa sakon, ya riga ya cire layinsa daga cikin Wayar Salula (Handset) dinsa,
to lokacin da ka aika da wannan sakon, sakon zai tafi network (misali MTN), idan yaje can, sai su ajiye wannan
sakon har lokacin da wanda ka aikawa sakon yasa layinsa, yana sa layin sa, zai
ga sakon da ka aiko mai, ya karanta. To shima Email haka yake, idan ka budo
email dinka ka, ka rubuta wasika zuwa ga wani, shi wanda ka aikawa idan baya
kan Kwamfiyuta, to wannan wasikar zata tafi wurin webserver (misali YAHOO),
sune zasu ajiye wannan sakon, har duk lokacin da wanda ka aikawa sakon yaje ya
budo email dinsa, saisu toro masa da wasikunsa gaba daya, ya karantasu, wannan
abun yana faruwane a cikin dan kanknain lokaci. Su web server din zasu turo
masa ne ta hanyar WEB BROWSER (Wanda zanyi Magana anan gaba), bayan sun turo
masa shi kuma sai yakaranta ta wasikunsa akan web browser din, (misalign web
browser shine Microsoft Intanet
Explorer).
Ga
Misalin Hoton shafin yanar Gizo-Gizo na BBC Hausa.

YADDA ZAKA HADA KWAMFIYUTARKA DA INTANET
Idan kana da
kwamfiyuta, zaka iya hadata da Intanet ta hanyoyi kamar haka:- ta DIAL-UP,
ADSL, ISDN, V-SAT, RADIO(GPRS), HOT SPOTS, WI-FI, da sauransu duk wadannan
hanyoyi ne da zaka hada kwamfiyuta da Intanet, abin da ake nufi shine zaka iya
hada kwamfiyutarka da Layin wayar gidan ka, kamar starcoms, ko da tauraron dan
adam wato vsat, ko ta cikin iska, ko ta wayar tafi da gidanka, duk wadannan hanyoyi ne na hada kwamfiyuta da
Intanet.
Ga wani misali domin mai karatu ya kara
gane menene Intanet. Misali, idan kasiya Wayar Salula (Handset), bazaka iya
kiran kowa ba sai ka saka layi amma wata wayar zaka iya budo cikin ta, zaka iya
kara sunaye, harma zaka iya rubuta wasika amma ba zaka iya aikawa da wasikar ba
sabo da baka sa layi ba, na biyu idan zaka sa layi, zaka zabi, wane irin layi
zaka sa, layin VMOBILE, ko MTN,
ko glo, ko MTEL,
su wadannan su ake kira Network Service
Provider, idan kasiya layin, ajiki ne zaka ga lambarka, da wannan lambar zaka
iya kiran mutum, to itama haka
Kwamfiyuta take, idan ka siya Kwamfiyuta, zaka iya aikace aikacenka da ita har
zaka iya kallon CD zaka iya yin rubutu da ita, har inkasa mata wata Softwaya misali
softwayar ta Encata, kayi bincike da ita, sai dai bazaka shiga Intanet ba, idan
kana son ka hada ta da Intanet, da farko abin da zaka fara yi shine zaka je
kamfanin da suke samar da service na Intanet, wato Intenet Service Provider (I S P), sune
suke bada sabis na Intanet sune zasu
hada maka kwamfiyutarka da Intanet, ko su baka abin da zaka hada da kwamfiyutarka
ka shiga Intanet, ko suje su hada maka. Sannan suyi maka bayanin abubuwan da
zaka rinka biyansu. Idan kana son bayani game da Intanet Service Provider ko
yawan abin da ake biya zaka iya ziyartar shafin mu na yanar Gizo-Gizo.
ABUBUWAN DA AKE YI A INTANET
Ya wancin abubuwan da akeyi a Intanet a nan Nigeria baya
wuce aika wasika da karanta wasika, sai kuma duba labarai da bayanai, wadannan sune
zaka ga mutane sunfi yawanyi, alhali wadannan abububuwan abu daya kenan da
akeyi a Intanet. Ga kadan daga cikin irin abubuwa da akeyi a Intanet, sune:-
1. Karatun Alkur’ani Mai Girma: akwai
shafin yanar gizon da zaka je, ka karanta Alkur’ani, zaka iya zabar kira’ar da
kake so, da surar da kake so.
2. Koyon
Karatu: Akwai shafin yanar GizoGizo, da zakaje ka koyi karatu, ko a koyar
da kai, har a rinka baku assignment(Gwaji), har in ka gama karatun, kayi
jarrabawa idan kaci jarrabawar a baka sakamako abaka certificate wannan shi ake kira (E-LERNING ).
3.
Bincike
ta fannin ilimi mai zurfi, zaka
iya bincike ta fannin ilimi mai zurfi kamar su yadda sassan jikin mutum yake
aiki ko sinadaran da ke jikin mutum, idan sassan mutum ne zakaga ga yadda
zuciya take bugawa ko yadda sakonni suke tafiya tacikin kwakwalwa ko yadda cuta
take shiga jikin dan Adam da yadda take shiga cikin sassan jikinsa, da yadda
take yaduwa, ko ilimin taurari da nisan dake tsakaninsu, da ilimi mai zurfi. Ko
tarihin kasashe, Tarihin Al’umma da yarensu.
4. Sanin yadda abu yake aiki:- akwai shafin yanar gizo-gizon da idan kaje sazu nuna
maka yadda kwamfiyuta take aiki, ko yadda aka kera wayar salula, ko yadda ake
kera rediyo, ko yadda ake kera wasu na’urori na lantarki, lo yadda zaka kera
makunnin kashe wutan nefa ko kunnawa ta hanyar tafi ko ta hanyar atishawa ko ta
hanyar remote control na talabijin, wato misali kana cikin daki ankawo wuta, da
remote control zaka iya kunna wutan nepan ko idan kayi tafi sai kaga gulob din
ya kawo wuta indan ka sake yi sai kaga ya mutu, zaka iya ganin yadda wasu
abubuwa na bam mamki suke aiki, kamar yadda kwamfiyuta(robot) take aiki
kwamfiyuta(pc), da wasu abubuwa na bam mamaki.
5. Koyon yadda ake gyaran abu:-
akwai shafin yanar gizo gizon da idan kaje zasu kawo maka hoton yadda zaka gyara
abu, misali kana da waya sai ta samu matsala, ko ta daina kawo wuta na haske,
da kaje website din zaka zabi sunan wayarka da model dinta (lambarta) sai kaga
ankawo maka hotunan rikice rikicenta sai ka duba inda LCD Light yake sai kabudo
hoton zaka ga an nuna maka kaza zaka cire ko ka canza.
6. Neman Aiki:- akwai website (shafin yanar
GizoGizo) da dama da zaka shiga a Intanet ka nemi aiki, irin aikin rubutu ta
cikin Intanet kana zaune daga gida, ko yadda zaka rinka yiwa wasu kamfanoni
talle idan kana da website.
7. Siyayya:- a Intanet akwai
websites (Shafuffukan Yanar Gizo-Gizo ) da zaka zabi abin da kake son kasiya a
fada maka farashin sa, in ma kana da credit card (Kudin Intanet, misali
MasterCard) zaka iya siya, idan daga kasar waje ne ayo maka shippin (a aiko
maka ta cikin jirgin ruwa) zuwa Nigeria a fada maka adireshin da za kaje ka
karbi abin naka, Ga Misalin Shafin Yanar Gizon Da zakaje kayi Siyayya:-

8.
Aikawa da sakonni
da karban sakonni: - Ta Intanet zaka iya aikawa da sakonni zuwa wurare
daban-daban cikin dan kankanin lokaci, zaka iya aikawa da sako daga Intanet zuwa
wayar salula (handset).
9.
Kasuwanci:- zaka iya siye da siyarwa
ta Intanet, misali zaka iya siyan sha filin shafin yanar gizo (Web Hosting) da
sunan shafin yanar gizo(Domain Name) bayan kasiya wadannan sai kagina shafin
yanar Gizon(akwai littafina da yake koyar da yadda zaka gina yanar gizo), bayan
ka gina zaka iya siyar da shafin yanar gizon, ko kuma da shafin yanar gizon
naka ka gayyato wasu kamfanoni karinka yi musu talle a shafin naka suna biyan
ka, idan suna samun mutane suna zuwa shafinsu daga naka, wannan shi ake kira E-COMMERCE.
INANE CYBER CAFÉ?
Cybercafé wuri ne da aka tanada domin shiga Intanet,
wurine da za kaga Kwamfiyuta da yawa, an hadasu da Intanet, wato dakin shiga Intanet kenan, idan
kaje wurin kana son kayi browsing (wato ka shiga Intanet) zaka basu kudin iya
awowin da kakeson kayi, sai su baka wata takarda da take dauke da lambobi (password),
wadannan lambobin sune zakaje karubuta su ajikin Kwamfiyuta ka budo Intanet,
zanyi bayani akan yadda ake budowa nan gaba. Ga Misalin yadda Cyber Café Take:-

ME NE NE WEB BROWSER?
Web browser softwaya ce da
zata baka damar budo, da ganin Shafuffukan
Yanar Gizo-Gizo, wato Website,
Misalin
web browser sune: - Microsoft
Intanet Explorer, Opera, Netscafe Navigator, Mozilla, da
Dillo da sauransu.
ME AKE NUFI DA WEBSITE?
Website
itace tarin Shafuffukan yanar Gizo-Gizo, wadanda suke dauke da bayanai na
rubutu, ko hotuna, ko sauti, da abubuwa masu motsi, kamar yadda nayi bayani tun
a farko. Akan shafin ne zaka budo ka karanta bayanan da kake so, ko kaji, Misalan
shafuffukan Yanar Gizo-Gizo sune: - www.bbchausa.com www.yahoo.com www.google.com www.mannir.com , duk adireshin da kaga ya
fara da www ko http:// to website ne, www
yana nufin World Wide Web http:// na nufin Hyper Text Transfer Protocol. Sannan zakaga yawanci suna karewa da,
.com (company), ko .org (organization). Ko .net (network), da sauransu, ko kaga
ya kare da .co.uk wato yana nufin ita wannan website din ta Engila ce, .co.ng,
wannan website din ta Nigeria ce, akwai kuma wadanda zaka ga sun kare da .gov
wato na gwmanati ce, .edu na fanning ilimi ce, .mil ta sojoji ce wato military,
.info wato bayanai information, .Biz wato harkokin kasuwanci, da sauransu.
ME NE NE INTANET ADDRESS?
Internet address, abubuwane guda biyu
wato Email da www, su wadannan suna karkashin wani abu ne da
ake kira domain name system, amfaninsa shine domin tantance adireshin yanar
gizo-gizo a Intanet, misali, a cikin Gari zaka samu akwai, unguwa a Unguwa
akwai layi, a layi akwai gida, to haka ma wannan yake, misali a website na
yahoo zaka samu suna da folder na email, suna da folder na search suna, da
folder na shop, a cikin folder na email zaka samu akwai folder na mail a cikin
folder na mail za ka samu akwai folda, misali kana neman inda aka fassara
kalmomin kimiyya ne a sahfi na kaga a adireshin zaka samu kamar haka http://www.mannir.8m.com/kimiyya/kalmomi
wato yana nufin idan kashiga website din mannir akawai folder mai suna mannir a
wannan foldan(jaka) akwai wata folder mai suna kalmomi a folder kalmomi ne zaka
samu fassara kalmomin.misalin adireshin www shinw www.mannir.com ,
kaga wannan yana nufin shafin yanar gizo-gizon mannir, shi muka misalin
adireshi na email shine: ceo@mannir.com .
wato yananufin shugaba a adrieshim mannir. Wannan alamar @ ana furta tad a at
YADDA ZAKAYI AIKI DA MOUSE WURIN SHIGA INTANET
Shi
mouse wani abu ne da ake amfani dashi, wurin motsa pointer (wata yar kibiya da
zakaga tana yawo a cikin gilashin kwamfiyuta) dake cikin monitor(screen din
Kwamfiyuta), shine za kaga kana motsa shi itama pointer (kibiyar) na motsawa,
kuma idan zaka rike mouse zaka rike shine
kamar haka:-

sannan Idan dai kana browsing (kana cikin
Intanet) idan zakayi click(danna mouse) karinka matsa bangaren hagu, sannan
idan dai kana cikin website(shafin yanar gizo) baza kayi click din wuri ba sai
kaga pointa(kibiyar) ta zama hoton hannu , duk inda kaga ta zama hoton hannu
za’a iya shiga wurin, wato zaka iya click a wurin, sanan inda zakayi click din
zai iya zamowa rubutu ko hoto ko abu me motsi, duk lokacin da kayi click akan
abu zai bude maka wannan abin da kayi click akai, misali:- ka bude website din www.bbchausa.com kana duba shafin, sai kaga wani wuri an
rubuta SHIRIN SAFE to da kaje kan
tsakiyar rubutun zakaga pointer(kibiya) ta zama hannu, sai kayi click(ka danna)
wurin, to zai bude maka shafin da aka kawo cikakken labaran shirin safen,
sannan kada ka manta koyaushe zakayi click karinka yin click din bangaren hagu
na mouse, domin in kayi click din dama zai kawo maka wasu abubuwa ne,wato (menu)
sannan a wasu shafin zaka yi amfani da ENTER na kibod wurin yin click, kamar a yahoo sign, zaka iya yin amfani da ENTER wurin click
din sign in, kuma zaka iya yin amfani da mouse wurin
yin sama da shafi ko kasa da shafi, idan zakayi zakazo can bangaren karshe na
screen zaka ga wani arrow(kibiya) a sama da wata a kasa sai kazo kayi click akan aron(kibiyar), zaka ga shafin yanayin
sama ko kasa, idan kuma baka ganeba zaka iya amfani da aron sama ko na kasa
ajikin kibod, zakaga wasu kibiya daya na kallon sama daya na kallon kasa daya
na kallon dama daya na kallon hagu. Yanzu kuma zan koma inyi bayani daki-daki gameda
yadda zaka shiga Intanet.
NEMAN DAKIN SHIGA YANAR
GIZO-GIZO (CYBER CAFÉ)
Da
farko idan kanason ka shiga Intanet, zaka nemo inda cyber café take wato inda
kaga an rubuta cybercafé ko Intanet Café, ko Café, to duk inda kaga an rubuta
daya daga cikin wadannan to wannan wurin ana shiga Intanet. Sannan
idan garin dakake babu cyber café to zaka iya shiga Intanet ta cikin Wayar
Salula (Handset) idan tana da WAP. (kuma akwai littafin da na rubuta mai koyar
da yadda ake shiga Intanet ta cikin wayar Salula, da yadda zaka saita wayarka
tana shiga Intanet, sannan na yi bayani kadan a cikin wannan Littafin, zaka iya
samun littafin a inda ake siyar da wannan littafin, in kuma kanason littafin ta
Intanet, zaka iya aiko mana wasika zuwa adireshimmu na Email manniru@gmail.com .
YADDA AKE SHIGAR DA (PASSWORD) LAMBOBIN DA SUKE JIKIN TAKARDA, A BUDE
DESKTOP
Idan
kaje cyber café zaka fadi irin yawan awar da kake so kayi yawancin awa daya
bata wuce N100, ko N80, minti talatin kuma N60, ko N50 a yanzu. Idan ka basu
kudin zasu baka wata ‘yar takarda wacce take dauke da wasu lambobi (password) a
jikinta. bayan sun baka sai kazo ka samu Kwamfiyutar da ba kowa akai, ka zauna
ka shigar da lambobin dake jikin wannan
takardar, bayan ka zo ka zauna zaka ga screen na kwamfiyutar misali
kamar haka:-

A wadannan layikan guda
biyu ko daya da ka gani a nanne zaka shigar da lambobin da suke jikin takardar,
idan kuma baka gane yadda zaka shigar ba sai ka tambayi masu kula da wurin, sai su nuna maka yadda zaka shigar, bayan kazo
ka zauna, zaka duba inda aka rubuta (misali click
here to enter a password), zaka ga
wurine da dogon layi. Kamar yadda nayi bayani a baya, sai kazo cikin layin kayi
click (ka danna mouse) sai ka kwafe password (lambobin jikin wannan takardar)
zuwa cikin wannan dogon layin (idan kana rubutawa yanwaci zaka ga wannan alamar **** kada ka damu sai kaci gaba da rubutawa ) bayan ka
kwafe sai kayi click akan login, ko kadanna ENTER a jikin
kibod, kana dannawa zata bude maka DESKTOP, misali kamar haka:-

wanan wurin shi ake kira
Desktop duk lokacin daka bude kwamfiyuta shi zaka gani wadannan abubuwan kanana
dakake gani su ake kira Icons, icons ankasasu kashi uku ne ko fiye akwai
fayils, akwai foldes akwai programs, kuma kowanne akwai aikinsa a cikinsu daya
zamu dauka wanda dashi ne ake shiga Intanet. Wato zaka ganshi karamar e anzagaye ta
YADDA ZAKA BUDO
WEB-BROWSER KA SHIGA INTERNET
Bayan ka budo desktop, sai kaduba inda aka rubuta
daya daga cikin wadannan:- Internet
Explorer, Fire Fox, Opera, Netscape Navigator, SeaMonkey, Mozilla Firefox,
uBrowser, CompuServe. Da kaga daya daga cikin wadannan sai kayi double click
(kaje da pointa kan wurin ka danna mouse sau biyu), idan ba kaga ni ba sai kaje
can kasa gefen hagu zaka
ga inda ka rubuta START , bayan ka danna sai kaje wurin kayi click, bayan kayi click sai ka duba
inda aka rubuta Intanet Explorer,


wannan
shine mislain shafin yanar gizo na Yahoo, to yanzu ka shiga intanet ke nan,
kafin muje gaba, zan sake kara bayani ga me da Internet Explorer. Microsoft Intanet Explorer ita ce web browser din da
tafi sauki wurin shiga Intanet, kuma yawancin kowace cyber café kaje zaka samu
suna da Intanet explorer, don haka ko yaushe kaje browsin sai ka duba Intanet
explorer a desktop. Kuma ita Intanet explorer software ce, wani zai iya yin
tambaya yace wai mene Intanet explorer ko mene software, kuma mutane da yawa
suna mamakin wai ta yaya Kwamfiyuta take aiki, har idan bakayi abu daidaiba ta gyara
maka, harma kaga tana maka gargadi. Da farko kafin inyi bayani game da wannan,
ya kamata kasan mecece Kwamfiyuta Softwaya din ?, kamar yadda na yi bayani a farko, to ita
dai Kwamfiyuta duk abin da kaga tanayi to wannan abin sa mata akayi, duk wani
gargadi da kaga tanayi, to mutum ne yazauna ya shirya mata, mutumin da yake
shirya wa kwamfiyuta program shi ake kira Programmer, abin da ake shirya mata
shi ake kira programs, sannan
program din ake harhada wa a shirya mata, sai ake kiransu Software, sannan ita kwamfiyuta ta dogara ne da irin
programs din da aka saka mata sannan zaka ji ana cewa kwamfiyuta tana da virus,
to wannan virus din shima shiryashi akeyi sai a yada shi, sai kuma a kero
magani wato Antivirus. Sannan za’a iya shiryawa kwamfiyuta kowane softwaya, ko
kaima inka iya programming zaka iya shirya Kwamfiyuta program na Hausa, idan
ka saka mata program din da ka shirya zakaga kowane abu da zata rinka nuna maka
da hausa zakaga tana yi, har gargadi duk da hausa, tambaya ma da hausa, sabo da
kashirya mata da hausa, misali kanason ka kera programs na kwamfiyuta wanda zai
rinka yin yin hausa in mutmu ya taba wani madanna ga yanda zaka kera
karamin programs din:- da farko zaka
budo Microsoft Word a kwamfiyuta bayan ka bude sai ka danne Alt sannan ka danna
F11 zaka ga wani windows ya bude sai kaje kayi click din insert a can menu bar
sannan kadanna UserForm zaka ga wani form ya fito sai kaje inda aka rubuta
toolbox kaduba inda aka rubuta commandbutton sai ka danna bayan ka danna sai
kazio ka zana shi akan wannan UserForm din bayan ya fito sai kayi double click
akansa bayan kayi sai ka rubuta msgbox “Me yasa ka danna wannan madannin
kada ka kuskura ka sake dannawa, danna OK ka batarda ni” bayan ka gama
rubutawa sai ka danna ENTRE a kibod, yanzu ka gama tsara mata idan kana son
kayi run din Program sai ka danna F5 a
jikin kibod zaka gat a kawo maka wannan Form din sai ka danna inda aka rubuta
CommandButton1 kana dannawa zakaga ta rubuto maka abin da kabata umar nit a
rubuta tace maka me yasa ka danna wannan madannin kada ka kuskura ka sake dannawa, danna OK ka
batarda ni. Bayan ta nuna maka wannan abin kana danna ok zaka ga abin ya bata
kaga anan kayi programming, wato ka koya wa kwamfiyuta cewa idan aka danna
wannan madannin to sako ya fito(msgbox) sannan sakon yace abu kaza, to wannan
kadan ken an daga cikin programming, idan kanason kakoyi programming zaka iya
ziyartar shafimmu na yanar gizo ko ka aiko mana da wasika zuwa emel dimmu, ko
kanemi littafimmu dana rubuta da hausa mai koyarda yadda ake programming duba
karshe wannan littafin. To kaga wannan abin shi ake kira software programming, wato
a nan yawan abin da yake cikin kwamfiyuta
ya dogara ne da irin yawan
softwayar da aka saka mata, misali yanzu kana da handset kana son ka zuba mata
wakoki, kuma wadannan wakokin suna cikin CD ne, kaga ita handset din naka ba
zata iya daukan dukkaan CD, ba, ko kuma kai ba duka CD kake son ka dauka ba,
kai dai wakokin ka keson ka dauka, to kaga anan idan ka saka CD a kwamfiyutarka
sai ka Nemo softwayar yanka, wakoki, ka saka wa kwamfiyutar, sannan da wannan
softwayar zaka budo CD ka zabi inda kake son ka yanke sai ka yanke, CD, ka
mayarda shi MP3, sannan sai ka tura wa wayar taka, to kaga wannan duk aikin
Softwaya ne. akwai softwayar da idan ka kunna kwamfiyutar ka saidai kaji ta
fara karaun Alkur’ani. To kaga anan softwaya tana da matukar amfani a Kwamfiyuta.
Sannan idan kana son Softwaya na Hausa irin wanda muka shirya zaka iya aika mana da wasika zuwa
email din mu, sai mu aiko maka da adireshin yanar Gizon da zakaje kayi Download
din wannan Softwaya din. To kaga a nan
Microsoft Intanet Explorer softwaya ce da zata baka damar Ganin shafuffukan
Intanet, ne wanda kamfanin Microsoft take shiryawa.
YADDA AKE BUDE SABON
ADIRESHIN EMAIL NA YAHOO
Bayan kaje cyber café, ka siya
time ambaka password ka shigar da password din ka budo Intanet explorer,
(Misali=START—INTANET EXPLORER). Bayan ta budo maka wani shafi, Sai ka duba can
sama kusa da inda akarubuta Address, sai
kazo kayi click a kan wannan dogon layin, karubuta, misali:- www.yahoomail.com
kamar
haka:-

bayan
ka rubuta saika danna Go
ko ENTER. Bayan ka danna ENTER zaka ga ta bude maka wani shafi
Bayan
ta budo maka shafin, sai ka duba inda aka rubuta sign
up sai ka danna wurin
sai kayi click bayan kayi click sai kajira shi
zai kawo maka form din yahoo registration, bayan ya kawo maka form din yahoo
registration, sai ka cike shi, bayan ka cike a karshe zaka ga inda aka rubuta SUBMIT
ko inda aka rubuta I
agree sai kayi click din wurin, bayan kayi
click zaka dan jira har sai kaga ta kawo
maka
wani sabon shafi an rubuta Registration Completed. Kamar haka 


YADDA AKESHIGA ADIRESHIN E-MAIL
Shi E-Mail adreshi zaka iya bude shi a
wurare da dama kamar haka a: yahoo.com ko hotmail.com
ko mail.com ko lycos.com ko netaddress.com ko email.com ko 37.com. Kamar
yadda nayi bayani a baya, bayan kaje cyber café, kaje ka budo Intanet
explorer, zaka zo kusa da inda aka rubuta address, sai karabuta www.yahoo.com bayan karubuta sai ka danna Go
za’a budo maka wani
shafi, bayan shafin ya bude, sai kazoo gaba da inda aka rubuta yahoo ID,
anan sai karubuta email dinka ba dole
bane sai kasa @yahoo.com, bayan ka rubuta sai kadanna TAB ajikin kibod, ko kayi
click gaba da inda aka rubuta password sai karubuta password dinka, bayan
karubuta sai kayi click akan Sign in sai kajira yabude, bayan yabude zai budo maka
wani shafi zaka ga anrubuta Wellcome wane, shafi kamar
haka:-

idan kuma be bude ba, to kayi
kuskuren wani harafi daga cikin emel dinka ko password sai ka sake rubutawa .
IDAN ZAKA KARANTA WASIKA
Idan zaka karanta wasika, sai kayi click
Akan inda aka rubuta inbox,
ko kuma CHECK MAIL ko inda aka rubuta You have xx unread message

sai kayi click akan wurin, bayan kayi
click, zata jero maka wasikun dakake dasu sai kazo, kan
wasika, (kan
abin da wasikar ta kunsa) sai kayi click, kana yin click zaka ga wasikar ta
bude sai ka karanta.
RUFE WASIKA BAYAN ANGAMA KARANTAWA
Bayan ka gama karanta wasika, idan zaka
goge sai ka danna DELETE
zaka ganshi a saman wasikar
ko a kasan wasikar, in ka gama karanta wasikar sai ka danna CHECK MAIL ko INBOX.
IDAN ZAKA RUBUTA WASIKA
Lokacin daka bude email dinka, idan
wasika zaka rubuta sai kazo sama bangaren hagu zaka ga inda akarubuta COMPOSE
sai kayi click bayan kayi
click zai bude maka wani shafi kamar haka:- inda aka rubuta To sai karubuta
Adireshin Emel din wanda zaka aika wa wasikar misali:- mannirgetso@yahoo.com sai ka danna TAB ajikin kibod, inda
aka rubuta Subject kuma sai karubuta abin da wasikar ta kunsa, sai kayi
click acikin shafin da zaka rubuta wasikar sai kafara rubuta wasikarka

Kara girman rubutu
Idan zaka rubuta wasika kana son ka kara
girman rubutun, zaka duba sama kadan cikin inda kake rubuta wasikar, zakaga wata
alama karamar A, da babban A da karamar A, inkaje wurin kafin
ka danna zakaga an rubuta Front Size sai kayi click akan wurin, sai kazabi
girman rubutun dakakeso.
Sa kala a
rubutu
Idan kanason ka sakawa rubutun
dakake yi kala, za kaje jerin layin daka dauko na baya, inda kaga anyi wata
alamar T , kafin kayi click zakaga an rubuta text colour, sai kayi click din wurin, zakaga ya kawo maka kaloli, sai ka zabi kalar da kakeso,
kayi click akan kalar.
Saka hyperlink a rubutu
Shi hyperlink rubutu ne, wanda idan ka danna
rubutun zai kaika websites(shafin yanar Gizon) da aka rubuta a jikin wannan
hyperlink din, misali wani abokinka ne baisan website din Google ba sai kana son
ka aika masa da website ta cikin email dinka, sai kazo jerin wurin da ka dauko sauran,
zakaga inda akayi hoto kamar alamar duniya da wani abu kamar ankwa ajiki, kafin
kayi click zaka ga an rubuta create hyperlink sai kayi click akan wurin, amma farko sai
karubuta website din, misali Google (sai kayi highlight dinsa) yanda kuwa ake halayit kuwa shine, bayan
karubuta Google sai kasa mouse dinka kafin G
sai kadanne sai ka ja harzuwa e (wato e din karshen Google) zakaga rubutun yayi baki, sai kaje wurin creat hypalink kayi click sai karubuta website din
misali http://www.google.com sai kadanna ok, duk a cikin wasikar
zakayi wannan.
Sa Attach File

AJIYE WASIKA A DRAFT
Idan kana rubuta wasika sai baka gama ba
kuma kaga lokacin da kasiya na Intanet ya kusa karewa, ko kana son ka ajiye
wasikar ba yanzu kakeson ka aika wasikar ba, zaka iya aiye ta a draft(wurin
ajiye wasiku), lokacin da kadawo kaci gaba da rubuta ta sannan sai ka aika,
yadda zaka ajiye abu a draft shine, lokacin da kake rubuta wasika idan ka duba
saman wasikar zakaga inda aka rubuta SAVE AS DRAFT to nan zakayi click sai ta ajiye maka
wasikar duk ranar da kashiga Intanet sai kaci gaba gaba da rubuta wasikar.
Duk lokacin daka zo kabude email
dinka, idan zaka budo wasika daga DRAFT saika duba inda aka rubuta DRAFT sai kayi click din wurin bayan kayi click
din wurin zaka ga ta budo maka jerin wasikun daka ajiye su a draft sai dai
kawai kayi click akan wasika kaci gaba da rubutata. Lokacin daka gama rubuta
wasika gabadaya, sai kazo inda aka rubuta To:
sai ka rubuta adireshin
wanda zaka aikawa da wasikar awurin, misali
To: manniru@gmail.com idan kuma zaka aikawa da mutane da yawa
sai ka rubuta email din na farko sai kasa comma “ ,
“ misali zaka aikawa da mutum uku
mannirgetso@yahoo.com,sagir13131@yahoo.com,manniru@gmail.com
haka zakayi ta jera
sunayen email din kana raba su da kwama. Bayan ka gama rubutawa sai kaduba sama
zaka ga inda aka rubuta SEND
sai kayi click akan wurin,
idan wasikar ta tafi zata nuna maka Message Send,
IN ZAKA GOGE WASIKA
Kamar yadda nayi bayani da farko I dan
kana sonka goge wasika sai ka danna DELETE ko kayi check (ka zabi) wasikun da zaka
goge wato kayi musu good (wani dan box, a kwati zaka gani lokacin da ka bude
wasikunka a wannan karamin box din sai kazo cikinsa kayi click ) , bayan kayi
check din ko wace wasika sai kadanna DELETE zai goge maka wasikun dakayi check dinsu.
YADDA ZAKA NEMO WASIKA
Misali wani abokinka ya aiko maka da
wasika acikin wasikar ya aikoma da lambobin scratch card na NECO sai bakaga
wasikar ba, saboda kana da wasiku da yawa, kuma ya turo wasikar, to lokacin da
ka budo E-MAIL din ka zakaga inda aka rubuta
SEARCH MAIL a hagu a wurin zakaga wani dogon
box(layi) sai kayi click acikin sai ka rubuta NECO ko karubuta PIN bayan ka rubuta
sai kayi click akan SEACH
MAIL, in dai wasikar tana
email dinka zaka ga ankawo maka ita, sai kayi click akan wasikar, zaka gat a
bude.
YADDA ZAKA DUBA SAKAMAKON JARRABAWA TA INTANET (NECO, WAEC, KO JAMB)
Idan kanason kaduba sakamakon jarrabawarka
ta NECO, WAEC ko JAMB ta cikin Intanet, da farko bayan kaje kasiyo katin duba
sakamako ta Intanet (wato Scratch card na WAEC, NECO, Ko JAMB) sai kaje cyber
café(dakin shiga Intanet), bayan kasiya lokacin da kakeson kayi a Intanet na
minti talatin ko na awa daya (minti 30 N60, awa daya kuma N100 (ayanzu)), bayan
kashigar da password kabudo desktop saika bude Internet Explore, saika duba sama gaba da inda aka rubuta Address sai kayi click akan wannan
dogon layin sai karubuta adireshin da yake jikin katin duba jarrabawar, misali www.waecdirect.org
ko www.necoonline.com
. Bayan karubuta sai kadanna Enter ajikin kibod ko kayi click akan GO a gaban inda karubuta adireshin, bayan ya
bude maka, sai kacike wasu gidaze zaka gansu
yawanci a bangaren Dama (wato zaka zabi shekarar da kayi jarrabawar, sai karuta
lambar jarrabawarka sai karubuta, lambar katin da kuma PIN na katin duk acikin
wannan gidan zaka rubuta su). Bayan ka gama rubutawa sai kadanna SUBMIT.
YADDA ZAKA FITO DA SAKAMAKON JARABAWARKA DAGA SHAFIN
YANAR GIZO-GIZO (PRINT)
Bayan ka budo sakamakon naka sai kazo kan shafin kayi Right-Click(wato
kadanna Mouse amma bangaren dama zaka danna) bayan kadanna zaka ga anjero maka
wasu abubuwa a wadannan abubuwan sai kaje inda aka rubuta Print sai kayi click akan wurin, bayan kayi click wani dialog kamar
haka:- 

Bayan yabudo maka sai ka zabi sunan printa sai
kadanna Print ko ka danna ENTRE (in
baka ganeba sai katambayi masu café din. Ko shafi kakeson kayi print
haka zakayi.
KOYI YADDA AKEYIN CHATTIN
MENE CHATTING?
CHATTING
wata hanyace da zakayi magana da mutum ta hanyar rubutawa juna sako ta rubutu
dakuma ta hanyar sauti da kuma gani, wato zaku iya magana da mutum kana ganinsa
shima yana ganinka kuma kowa yana jin maganar dan uwansa.
Kuma
a chatin zaka iya haduwa abokai daga kasa she dabam dabam na duniya.
Kuma shi chattin amfi yawan yinsa ne ta hanyar rubutawa mutum sako ta rubutu,
misali ka hadu da wani dan SAUDIYA sai ka rubuta masa Assalamu Alaikum, a lokacin shima zai rubuto maka, Wa’alaikumussalam, a haka zaku yi ta magana dashi, idan
yana da webcam(abin da zaka iya ganin sa)
to zaka iya ganinsa, idan kaima kana da webcam zai iya ganinka,
ME AKEYI A CHATTING?
Abubuwan da akeyi a chattin
suna dayawa, ga kadan daga ciki :-
Kasuwanci. haduwa da
Malamai na BOKO (lectures, prof. da sauransu). Haduwa da abokai daga kasashe
dabam dabam. Yin aiki (na cika form, typing da sauransu), ana biyanka. Mitin(kamar
wata ma’aikata zata iya yin mitin idan ma’aikatan(masu aikin) nata suna nesa da
juna. Da sauransu. Yawancin
abubuwan da akeyi anayinsu ne ta hanyar aikawa da sakonni ta rubutu
Magana(VoIP), da kuma gani(webcam).
YADDA AKE SHIGA CHATTING (YAHOO MESSENGER)




bayan yabude maka saika duba can sama
inda aka rubuta Messenger
sai kayi click akan wurin
sannan kayi click din YAHOO
CHAT sannan JOIN A ROOM,

idan baka ganeba to ka duba sama inda
akayi wani abu kamar alamart hoton Wayar Salula (Handset) da kan telephone akan
layin idan kaduba bangaren dama zaka ga wani alamar kibiya (arrow) guda biyu
kamar haka irin wannan guda biyu ®, idan kaje kan arrow din sai kayi click, bayan kayi
click sai kayi click akan CHAT sai kajira shi yabude, in bai bude ba,
sai kasake zuwa wurin wannan arrow din ka sake click, har ya budo maka.
YADDA ZAKA ZAFI CATEGORY DA ROOM KASHIGA
Bayan ya bude zaka ga ya budo
maka wani windows, zaka ga jerin
CATEGORIES sai kazabi category din da zaka shiga sai kayi click (misali= SCHOOL & EDUCATION), bayan kayi click zai sake jero maka jerin
ROOMS anan ma sai ka zabi room din da zaka shiga

(misali:- study group), bayan kayi click sai kadawo
kasa zaka ga inda aka rubuta Go to Room sai kayi click, zaka ga yabudo maka wani
windows zaka jira har wani dogon abu yacika bazai wuse sakan 10, sai kayi click
akan Enter Chat.
YADDA ZAKA GA YAWAN MUTANEN DA SUKE CIKIN CHAT ROOM
Bayan kadanna ENTER CHAT zakaga ta budo maka chatroom din kamar
haka:-

idan ka duba bangaren dama,
zaka ga Email din wadanda suke cikin dakin ne. Idan kaduba wadanda suke
bangaren hagu kuma zakaga wadansu kamar sunsa headphone, wasu kuma kamar suna
cikin tibi, wasu kuma ba komai. Wadanda suke da abu kamar headphone zaka iya
magana dasu, wato suna (voice chat VoIP(Voice Over IP). Su kuma wadanda suke
cikin tibi, zaka iya ganin su kamar a TV, wasu kuma har zaka iya ganinsu kayi
magana dasu. Idan kana son Karin
bayani yadda zaku yi Magana da mutum kana ganinsa shima yana ganinka ta cikin Intanet ka ziyarci
shafimmu na yanar Gizo-Gizo a
http://www.mannir.8m.com
YADDA AKE DUBA MUTANEN DA SUKE CIKIN CHAT ROOM DA IRIN ABUBUWAN DA SUKE
RUBUTOWA
Idan kaduba bangaren dama, nan kuma
zakaga rubutu nata fitowa (misali mannir: joint the room), wato anan nunama yanzu mannir ya shigo
dakin chatin din kenan, kuma a nanne zakaga kowa na rubuto abin da yaga
dama (misali mannir: akwai wani ba haushe kuwa?), to anan ne idan kana son kayi wa mutum magana
sai kaje kan email dinsa kayi double click akai(ka danna mouse sau biyu).
YADDA AKE TABO MUTUM A CHATTING
A bagaren dama zaka iya ganin wanda kasan
email dinsa, ko wani wanda kake son kuyi cattin dashi, yanda zakayi shine kaje
kan email din mutum a bangaren dama kayi click, sannan sai ka dawo kasa kayi click akan inda aka rubuta IM, bayan kayi click zaka ga wani window ya
fito, to a wannan window din zaka rinka rubuta abinda da kakeson ka fadamai,
misali Assalamu Alaikum, sai ka danna
Enter ko Send, misali zaka iya rubuta mai Hi sai kayi send ko kadanna ENTER a jikin kibod.
YADDA AKEYIN CHATTING
Bayan kayi click akan ID(Yahoo ID) din mutum, kuma ka yi click akan IM, bayan wani window ya fito kamar haka:-

sai kazo nan kasa sai kayi
click, sai karubuta Hi, sai ka danna SEND ko kadanna ENTER, sai kajira kaga
reply, yana dawo da reply zaka ga bottom toolbar yayi ja, kamar haka:-

sai kayi click akan wurin. Idan anyo maka
Reply misali sager:Hi ko asl?, idan kaga plz asl?, yana tambayarka
shekarunka nawane, sannan kai namiji ne, ko mace ce, sannan a wane gari kake,
shine ma’anar asl, idan kanason kaga ma’anonin irinsu kaziyarci shafimmu na
yanar gizo, kaga ta haka zakuyi ta communication(Magana) da mutum.
WASU KALMOMIN CHATTING DA MA’ANONINSU
Akwai kalmomin da ake amfani
da su a wurin chattin don rage dogon rubutu, misali:-
Name? = yaya sunanka, Ko yaya
sunan ki.
Age? = shekarun ka/ki nawa.
Country? = a wace kasa aka
haife ka/ki ?.
Location? = a ina ka/ki ke
yanzu.
Asl? = shekarun ka/ki nawa,
na miji ne kai ko ke mace ce, a ina ka/ki ke yanzu?.
Asl plz? = don Allah shekarun
ka/ki nawa, na miji ne kai ko ke mace, a
ina kaki ke yanzu.
M/f? = Namiji ne kai ko mace
ke.
U? = kai kafara Magana ko
kaifa?
?chat = kanason muyi chat
??? = Ban gane abin da ka ce
ba
R? = sake gyara abin da ka
rubuto
Webcam? = zan iya ganin ka/ki
Voice? = zan iya Magana dake
Mic ? =ka/k nada abin Magana,
ko zan iya jin maganar ki/ki
Busy = aiki na ke yi sosai
?? = ina da tambaya
link? = kana da wani shafin
yanar gizo
web? = kana da website na kan ka
Dasauransu.
A
lokacin da kuka fara chattin da mutum zaka iya ganin ya rubuto maka:- asl?,
wato yana nufin kai waye, namiji ne ko mace kuma shekarunka nawa, kuma a wace
kasa ka ke ko kike kamar yadda nayi bayani da farko. Akwai abubuwa da dama da
ake rubutawa wurin chattin nan kadanne daga cikin su kenan.
IDAN KAYI ABOKI KANASON KA AJIYE SHI A MESSINGER LIST
Idan kuna cattin da mutum sai kanason ka
ajiye shi a messenger list(wurine da zaka ajiye email din mutane), yadda duk lokacin
daka shiga yahoo messenger zaka iya gane mutum yana cikin chattin ko baya nan),
lokacin da kuke chattin da mutum idan ka duba saman dakin shi wannan mutum zakaga
wani hoton kamar kai, anyi alamar Tarawa ajikin kan, to nan zaka zo kayi click,
zaka ga ya bude maka, wani window sai ka danna next har sau biyu na karshen sai
ka danna Finish, bayan ka gama zakaga sunan email dinsa a
jikin yahoo messenger dinka, kuma zaka iya zuwa da Email adireshin wani , ka
ajje a messenger list, kamar yadda zanyi bayani nan gaba.
YADDA ZA’A AJIYE E-MAIL DIN MUTANE A MESSENGER LIST
Zaka iya samun Email adireshin abokinka
ka ajiye shi a messenger list yadda duk lokacin da kashiga Intanet, zaka iya
ganewa shima yana kan Intanet(chattin) ko bayakai, misali ka samo email adireshin
mannirgetso@yahoo.com
idan ka budo yahoo messenger sai kaduba inda aka jera hoton su Wayar
Salula(Handset) da sauransu zaka ga wani abu Kamar alamar kan mutum da alamar
Tarawa ajikin abin
sai kayi click a wurin zai bude maka
wani wuri, sai karubuta email adireshin bayan ka rubuta sai kadanna next har sau biyu daga karshe sai ka danna finish, zakaga email dinsa ya fito a cikin yahoo
messenger dinka.

YADDA ZAKA GANE ABOKINKA YANA KAN
INTANET KO BAYANAN
Duk
lokacin da kashiga yahoo messenger, idan ka ajiye Email adireshin mutane a
messenger list, to a farkon sunan kowa zakaga hoton wani abu kamar kan mutum,
to duk kan da kaga yayi kala wato yayi kalar dorawa to wannan mai Email din
yana kan kan Intanet wato yana cikin chattin, wadanda kuwa kaga basu da kala to basa kan Intanet, ta haka
zaka iya gane aboikinka yana kan Intanet ko bayanan, idan bayanan zaka iya rubuta mai
sako yadda duk lokacin da yahau Intanet zai ga wannan sakon daka aika masa.
Idan kana son karubuta wa mutum sako zaka je kan adireshinsa na email saikayi
double click bayan kayi double click sai kajira ya budo maka wani karamin
window, bayan ya budo maka window din sai karubuta abin da kakeson aika masa,
sai ka aika masa.
YADDA ZAKUYI MAGANA DA MUTUM KANA GANIN SA YANA GANIN KA
Idan kanason ka yi magana da mutum kuma kana
ganinsa, da farko bayan kaje cyber cafe, zaka duba Kwamfiyutar da take da
webcam idan kuma bata da webcam, sai ka
tambaye su ko suna da webcam, da microphone/speaker , zasu sa maka shi a bayan
Kwamfiyutar, bayan sun saka maka, bayan ka budo YAHOO MESSENGER, lokacin da
kuke chattin da mutum idan kaduba saman dakin da kuke chatting din zaka ga inda
aka rubuta action sai kayi click akan wurin, ko kuma file ka duba inda
akarubuta webcam sai kayi click din nan, daga nan, zaka ga inda aka rubuta CALL
sai kayi click akan wurin, sai kajira wancan
ya amsa, idan shima yana da webcam, a nan kasa hoton wanine yana chatin da
webcam ana ganinsa:-


YADDA ZAKA BINCIKO BAYANAI TA CIKIN INTANET
A wannan bangaren zanyi
bayani a kan
yadda ake nemo bayanai ta Intanet, misali yadda zaka nemo assignment(aiki) ta
Intanet. A wajen nemo abu acikin Intanet ana amfani da wasu abubuwa guda biyu
wadanda ake kira:- Directories
da Search Engines.
Shi Directoies ana amfani dashi wurin nemo wani abu kebantacce,
misali:- abu ya shafi magana ne ta Doctors(Likitoci), ko Kwamfiyuta
Programmers, ko Engioneer, ko gyaran wayar salula ko softwaya, da sauransu, to idan zaka nemo abu, ya
dangantane da abinda kake nema, idan abin da kake nema ya danganta ne da wani
abu kamar yadda nayi bayani, to zakayi amfani da DIRECTORIES wurin nemo bayanan
ka, misalan adireshin DIRECTORIES kuwa sune:- www.searchsystem.com www.directories.goole.com www.dir.yahoo.com . idan kanason cikakken
bayani gameda DIRECTORIES ko kuma jerin sunayen Adireshin directory, ka ziyarci
shafin mu na yanar gizo wato http://mannir..8m.com .
Da
farko Idan zaka
binciko bayani ta cikin Intanet zaka iya
nemo bayanin da hausa I dan abin yashafi hausa, sannan zaka iya nemo shi da
turanci, misali zaka iya tambayar “Labarun BBC hausa” sai akawo maka Labaran
BBC Hausa.
MENE SEARCH ENGINES?
Search
Engines wasu Websites(Shafin Yanar Gizo-Gizo) ne wadanda an tanadesune don
binciko abu a Intanet, a nanne za kaje karubuta abin da kake nema, sai su
binciko maka abin da ka nema cikin kankanin lokaci. Yawanci idan ka budo search
engines zaka ga akwai wani dogon layi wanda acikin wannan dogon layi zaka rubuta
abin da kake nema, bayan ka rubuta sai ka danna ENTER.

ADIRESHIN WASU SEARCH
ENGINES
ALTAVISTA , GOOGLE zanyi bayaninsu nan gaba
ASKJEEVES = Shima wannan shafin bincike, shima yana
daga cikin adireshin da zakaje karubuta abin da kake nema, yakawo maka, misali
an baku assignment
a makaranta anan ne zakaje karubuta abin da aka tambayeku ya kawo maka bayani
akan abin
WASU MANYAN SEARCH ENGINES
Su wadannan search engines su ake kira meta search engines, su idan kasa su nemo maka wani bayani,
suma zasu tattaro bayanan da sauran manyan search engines su nemo musu, saisu kawo
maka abin da kowane search engines ya nemo, kadan daga cikin su kuwa sune:-
YADDA ZAKA BINCIKO WANI BAYANI A GOOGLE
Idan zaka budo Google, zakazo layin gaban
inda akarubuta Address sai karubuta www.google.com sai kadanna Go ko kadannna ENTER, A wannan dogon layin
daka gani ananne zaka rubuta duk abin dakake nema,bayan karubuta abin dakake
nema sai kadanna ENTER. Misali kana neman Labaran Hausa ne a Intanet, bayan
kabudo google sai kazo dogon layin nan kayi click sai karubuta “labaran hausa”
bayan karubuta sai kayi click akan Google search, ko ka danna ENTER, bayan kayi click sai kajira yabudo maka abin
daya nemo maka, idan yabudo maka zakaga wasu rubuce rubuce dabam dabam, to anan
sai karinka karanta kanun bayanan, idan kaga irin bayanin dakake nema sai kayi
click akan tushen labarin (inda kaga anja layi ko inda kaga kalna rubutun bulu),
ko kayi click a inda kaga anrubuta Catched, bayan ka danna zai kawo maka websites
din dasuke dauke da labaran hausa, anan sai kazabi inda kake so kaje, idan kaje
kaga ba irin bayanan dakakeso bane sai kadanna Back zaka gansi acan sama bangaren hagu, idan
ka danna zai dawo dakai baya, sai kasake zaban inda zaka, sai kayi click. Misali
dakaje Google sai karubuta Mannir Ahmad zakaga yakawo maka shafi kamar haka:-

Amfani da alamar “
“ =sai kuma abu na biyu, lokacin daka nemo
wancan zakaga ya kawo maka website din da akayi magana akan Mannir daga baya kuma akayi magana akan Ahmad, to saboda magance irin wannan matsalar
zaka iya amfani da wadannan alamun “ “ ,
yanda zakayi shine kafin karubuta abin dakake nema sai kafara dannan wanan
alamar ( “ ), (yadda ake dannata shine zaka danne SHIFT
sai kadanna alamar tana nan kusa da Enter), (kamar haka “labaran safe” ), bayan
karubuta abin dakake nema sai kasake danna ta, bayan kagama sai kadanna ENTER,
zai kawo maka shafunkan da asali akayi magana akan “labaran safe” . Abin dazaka
lura anan shine, misali kana neman inda akayi maganar Mannir Ahmad ne a
Intanet, idan kaje google karubuta Mannir Ahmad baka sa wannan alamun ba to zai
kawo maka websites da akayi magana akan Mannir daga baya kuma akayi magana akan
Ahmad, amma idan kasa wannan alamun zai kawo ma asali inda akayi ayi magana
akan “Mannir Ahmad”. Binciken abu a Intanet yana bukatar sanin ka’idojin
bincike domin sai kaje kata bata lokaci baka samu takamaimai abin dakake nema
ba, domin Karin bayani gameda yadda ake nemo abubuwa ta Intanet ka naimi
littafin mu da muka rubuta mai koyar da yadda ak bincike ta Inttanet.
YADDA ZAKA NEMO HOTO A GOOGLE
Idan hotuna kakeson kanemo, kamar hotunan
Wayar Salula (Handset) ko na gidaje kowane irin hoto dai, farko bayan ka budo www.google.com,
saI kaduba saman dogon layin zaka ga inda aka rubuta Images

sai kayi click akan Images din, bayan
kayi click, misali kanason hadset na Samsung, sai kaje kayi click akan dogon
layin, sai karubuta Samsung mobiles kana
rubutawa sai kayi click akan search, ko kadanna ENTER, zakaga an kawo maka
hotunan Wayar Salula (Handset) na Samsung iri-iri, to misali ace kanason kasiya
Wayar Salula (Handset) ne, kana son kasan kudin Wayar Salula (Handset) din idan
kazo zaka rubuta “Samsung
mobiles”+price sai kadanna
ENTER, idan aka kawo maka hotunan, sai kazabi iri wacce kakeso sai kayi click,
za’a kaika inda aka fani farashinata. Misali kanason kasiya nokia 6600 ne zaka
rubuta haka:- nokia
mobile+6600+price+Nigeria idan
karubuta sai kadanna ENTER, zakaga ankawo maka hoton Wayar Salula (Handset) din
sai kayi click akan Wayar Salula (Handset) din zaka, zaikai ka inda akafadi
farashin Wayar Salula (Handset) din a Nigeria.
YADDA ZA’A NEMO ABU A ALTAVISTA
Idan zaka bude altavista jaka
je wurin address sai ka rubuta www.altavista.com
bayan yabudo maka, sai karubuta abin da kake nema

Itama Altavista tana aikine kamar na
google amma ta wani wurin tafi google amfani, amfaninta kuwa shine misali
kanason akawo maka gaba daya websites din da MTN take dasu a Intanet to zakayi amfani da
Altavista ne, farko yadda ake budo ta shine:- zakazo gabada inda aka rubuta Address sai ka rubuta www.altavista.com
bayan karubuta sai kadanna ENTER bayan ta budo maka shafin, sai kazoo
kasa kadan zakaga inda akarubuta Worldwide sai kayi click din wani box(akwati)
kusada wurin sannan kayi click din cikin dogon layin sai karubuta host:mtnonline.com bayan karubuta sai kadanna ENTER, zakaga
ankawo maka gabadaya websites din MTN, idan kuma kanason websites din MTN dasuka
yi magana akan GPRS sai karubuta host:mtnonline gprs za’a kawo maka websites din MTN dasukayi
magana akan gprs.
NB=IDAN KANASON CIKAKEN BAYANI GAMEDA
YADDA AKE NEMO ABUBUWA A INTANET KA AIKA DA SAKO ZUWA:- manniru@gmail.com

Zaka iya shiga Intanet Ta cikin Handset, kayi Browsing, zaka iya
download(diban) hotuna, wakoki, Games da kuma Application (kamar Qur’an a
rubuce), da sauransu , kafin kafara shiga Intanet ta waya sai ka saita ta yadda
zata rinka shiga Intanet din, sannan in glo ne zaka kira Customer care ka fada
musu kanason kayi activate din Glo GPRS, in sunce , sannan sai ka saita wayarka
yadda zata rinka shiga Intanet.
Yadda zaka saita Glo GPRS
Profile
name= Glowap
Security=non-secure
Bearer=
GPRS
IP
Adress=010.100.098.022
UserName=wap
Password=wap
APN=glowap
Session
mode= Permanent
Connection
Security = off
Authentication
= normal
Login
type = automatic
Port
no. = 9201 na HTML, ko 3130 na WAP


Yadda
zaka saita na MTN

YADDA
ZAKA AIKA DA SAKO DAGA INTANET ZUWA WAYAR SALULA (HANDSET)
Akwai shafin yanar
gizo-gizo da zasu baka damar aikawa da sakonni zuwa wayar salula, (Misali ka
aika da sakon SMS daga Intanet zuwa wayar salula, idan kanason ka aika sako sai
kaje shafin. Yawanci wasu shafin sai kayi rajista kyauta, bayan kayi rajista,
zasu tambayeka lambar wayar ka, idan ka basu, zasu aiko maka da wasu code(lambobi),
da wadannan code din zakayi activate din account dinka dakayi rajista dasu,
bayan kayi activate din account din sai kafara aikawa da wasika, wasu shafin zasu
baka kyautar aika sako sau biyar, ko goma harma
dari, wasu kuma zasu baka damar aikawa da sako sau uku a rana, misalin
shafin da zaka aika da sako sune http://textnigeria.vsms.net
kaduba karshen wannan littafin zaka ga sunayen wasu safuffukan.
WASU KALMOMI DA MA’ANONINSU
·
INTANET EXPLORER = Softwaya
ce da zata baka damar shiga da ganin shafukan da suke Intanet .
·
CHATTING
= Hanya ce tayin magana ta hanyar rubutu da
hannu ko Magana ko gani wato tadi, ana yinsa ne ta hanyar rubutu, ko sauti
(magana), ko gani (kana ganin mutum) wato Webcam.
·
CLICK
= Idan akace kayi click ananufin kadanna mouse
dinka bangaren hagu zaka danna, kan
rubutu ko hoto ko hyperlink, da sauransu.
·
DESKTOP
= Wurine da, farko idan ka budo Kwamfiyuta shi
zaka fara budowa, daga nanne zaka zabi inda kakeson ka shiga, misali in zakayi
Browsing zaka duba Intanet Explorer, idan zakayi chattin zaka duba Yahoo
Messenger.
·
DOUBLE
CLICK = Ana nufin kayi click sau biyu a lokaci daya,
da sauri zakayi click din, kuma bangaren hagu na mouse zaka danna.
·
E-
MAIL = Shine kake amfani dashi wurin aikawa da wasiku
da sauransu misalin Email shine:- manniruahmad@yahoo.com .
·
Highlight
= ana nufin ka zabi rubutu yadda kuwa akeyi shine
zaka zo farkon rubutu saika danna mouse kada ka daga sai kaja a kan rubutun harzuwa
karshen rubutun kada ka daga mouse din, idan kayi hailayit zaka ga zagayen
rubutun yayi baki.
·
Hyperlink
= Rubutu ne da ake rubutwa wanda idan kayi click
akan rubutun, zai budo maka wani shafin Intanet na rubutun.
·
I
M = Sako ne da zaka rubuta shi a chattin, daka
rubuta shi zai tafi zuwa wurin wanda karubutawa kai tsaye, idan kana chattin da
mutum daka rubuta mashi, zai gani shima ya rubuto maka martani.
·
MESSENGER
LIST = Wurine a Yahoo Messenger da zaka ajiye email
din abokananka, yadda duk lokacin da kashiga yahoo messenger zaka iya gane
mutum yana kan Intanet ko bayanan,
·
PASSWORD
= Wasu lambobi da kake amfani dasu wurin bude
email dinka da wurin bude chatting da sauransu, in baka rubuta lambobin daidai
ba kokamanta su, bazaka iya bude Email dinka ba.
·
SOFTWARE
= Program ne da ake shiryawa Kwamfiyuta wadda
shi Kwamfiyuta zata rinka bi, ta gane me akasata ko me zata yi.
·
WAP
BROWSER = software ce ta Wayar Salula (Handset) wacce
zata baka damar ganin shafukan Intanet ta cikin wayarka.
·
Yahoo
ID = Email dinka da kake amfani dashi na yahoo
wanda dashi zaka rinka shiga chattin ko email dinka, amma idan aka zo
rubutashi, ana cire @yahoo.com, din misali email dina shine mannirgetso@yahoo.com to yahoo Id dina shine mannirgetso.
Idan
kana son fassarar Wasu kalmomin Kwamfiyuta ko na kimiyya, Ka ziyarci http://mannir.8m.com/kimiyya
SUNAYEN
WASU SHAFUFFUKAN YANAR GIZO-MASU AMFANI
Shafuffukan Bincike
www.yahoo.com
www.msn.com
www.google.com
www.altavista.com
www.ask.com
www.altheweb.com
www.search.com
www.dogpile.com
www.metacrawler.com
Shafuffukan Emel
www.yahoo.com
www.hotmail.com
www.gmail.com
www.aol.com
www.email.com
www.freemail.com
www.mail.com
www.lycos.com
www.netaddress.com
Shafukan Ajiya
www.streamloa.com
http://photos.yahoo.com
http://bookmarks.yahoo.com
http://briefcase.yahoo.com
http://spreadsheet.google.com
http://docs.google.com
www.filesanywhere.com
Shafuffukan Labarai
www.bbcnews.com
http://news.yahoo.com
http://www.voa.com
http://www.cnn.com
Littattafai
www.nigerianbooks.com
http://books.google.com
http://find.pcword.com/32480
www.audioquran.com/quran/quran
www.wikipedia.org
Shafuffukan Bincike Kebantacce
http://dir.google.com
http://directory.yahoo.com
Shafuffukan Nemo Hoto
http://image.google.com
http://images.yahoo.com
Diban Software (Downloading)
www.download.com
www.soft32.com
www.exefind.com
www.searchtruth.com
www.driverhq.com
www.emobilez.com/islam
http://example.microsoft.com/sample.asp
Maganin
Kwamfiyuta (Antivirus)
www.symantec.com
www.symantec.com/securitycheck
Softwaya Kyauta
www.completefreesoftware.com
www.opensource.org
www.freewarehome.com
www.freewarefiles.com
Karatu
www.freeflashtutorials.com
Jarrabawa
www.waecdirect.org
www.necoonline.com
www.neconigeria.com
Sako
zuwa waya (WEB2SMS)
http://textnigeria.vsms.net
www.ecall.com
www.textamerica.com
www.sendssnow.com
www.50sms.com
www.mobilemms.com
www.text-africa.com
http://freesms.1888usa.com/sms_global
www.smscountry.com
www.free-sms-message.com
Kere-Kere
www.electronicforu.com/electronicforu/lab
www.circuitguide.com
www.electronic_circuit_diagrams.com
www.discovercircuits.com
Wayar Salula
www.emobilez.com
www.emobilez.com/islam
www.emobiles.com/software/index.php
www.emobilez.com/secrets/
www.softwaregsm.com
Yanar
Gizo-Gizo na waya (WAP)
http://wap.oa.yahoo.com
http://wap.pocketdoctor.co.uk
http://mm.yahoo.com
http://e-messenger.net
http://wap.google.com
http://dictionary.refrence.com/wireless/index.html
http://wap.emobilez.net
http://wap.getjar.com
RUFEWA
A
nanne mukazo karshen wannan Littafi, dayake koyarda yadda ake shiga Intanet.
Don
Allah, duk kuskuren da aka gani, ko abin da ba’a gane ba acikin wannan littafi,
za’a iya aiko mana da wasika zuwa adireshimmu na Email manniru@gmail.com
Sannan
kuma, wannan Littafin na rubuta shine saboda wadanda basu san yadda ake
browsing ba (shiga Intanet), da kuma wadanda sunsani amma basu kwareba kamar
yadda nayi bayani a farkon wannan Littafin din, Duk wanda ya riga ya fahimci
wadannan, amma yanason Karin bayani, game da chattin ko bincike a Intanet, ko
yadda zai rinka yin Browsing (shiga Intanet) ta cikin Wayar Salula (Handset)
dinsa, Idan yanason wadannan bayanan zai iya ziyartar shafimmu a http://mannir.8m.com Ko ya binciki littattafan da na rubuta da
Hausa wadanda sukayi bayani akan:-
BROWSING
EMAILING
CHATTING
SEARCHING ON THE INTANET
MOBILE INTANET
WASU DAGA
CIKIN LITTATTAFAMMU
1. AN INTRODUCTION TO
VISUAL BASIC APPLICATION
2. EXCEL PROGRAMMING
WITH VISUAL BASIC APP.
3. FUNDAMENTAL OF
WEBDESIGN USING HTML
4. AN INTRODUCTION TO
WEB PROGRAMMING USING VSB/JS
5. WEB DESIGN PROGRAMMING WITH PHP & MYSQL
6. UNDERSTANDING &
USING COMPUTER SOFTWARE
7. VISUAL BASIC
PROGRAMMING
8. JAVA PROGRAMMING
9. PERL PROGRAMMING
10.
KOYI YADDA AKE SHIGA INTANET
11.
TRANSLATION OF SCIENTIFIC TERMS INTO HAUSA
12.
USING SCIENTIFIC CALCULATOR (HAUSA LANG.)
13.
FASSARAR KALMOMIN KIMIYYA
14.
INTRODUCTION TO WEBDESIGN & GRAPHICS
15.
KOYI YADDA AKE GYRAN NA’URA MAI KWAKWALWA
16.
ELECTRONICS PROJECTS
17.
KOYI YADDA AKE GINA YANAR GIZO
18.
KOYI DA KANKA ZANEN SOFTWAYA
19.
HOW TO DESIGN YOUR MOBILE
GAMES & APPLICATION
WASU DA GA
CIKIN SOFTWAYAR MU
1.
Mannir PL2
2.
Mannir PowerDVD
3.
Manir NetworkManager
4.
Mannir CyberLock
5.
Mannir SciCalc
6.
Manir C++ Builder
7.
Mannir J Editor
8.
Mannir CAD
9.
Hausa Word Prcocessing Sofwtare
10.
Hausa Taska (OS)
WASU
SOFTWAYARMU NA WAYAR SALULA
1.
QUR’AN KARIM
2.
TARJAMAR ALKUR’ANI
3.
HADISAI ARBA’IN
4.
MANNIR KAMUS
5.
AHLARI
6.
MOBILE NOTEPAD
7.
HAUSA PUZZLE GAME
8.
MOBILE WORM
9.
KAWA’IDI
10.
LOKUTAN SALLAH
GARGADI
BA’A YARDA A BUGA WANNAN
LITTAFI BA, TA KOWACE HANYA, BADA RUBUTACCEN IZININ MARUBUCINSA BA, HAKA KUMA
BA’A YARDA A SARRAFASHI TA KOWACE IRIN HANYA BA
E.T.C
Duk Softwaya ko Littafin da
kake bukata zaka iya aika mana da sako zuwa manniru@gmail.com,
mannir@mannir.com ko ka ziyarci shafimmu
na yanar gizo-gizo a www.mannir.com ko www.mannir.net www.mannir.org www.mannir.info Ko www.mannir.com/hausa
.
AKWAI VIDEO
CD NA WANNAN LITTAFIN, YADDA ZAKA GA KOMAI A BIDIYO, ZAKA IYA SAMUNSA A WURAREN
DA AKE SIYAR DA LITTAFIN
|
|||
|
|||
Subscribe to:
Posts (Atom)