GABATARWA
Da sunan Allah mai Rahama mai
jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga manzommu Annabi Muhammad (SAW);
Bayan haka, na rubuta wannan Hand Out dinne domin yan uwa na, irin wadanda
aiyuka sun yi musu yawa basuda lokacin da zasu je Computer, su koyo yadda ake
shiga Internet, Kuma suna matukar Sha’awan abin, amma basu da lokacin da zasuje
su koyo, ko basu da wanda zai zauna ya koya musu, To saboda hakane na rubuta
wanan hand Out din, Shi wannan wannan Hand Out din Gabatarwa ne game da
Internet, akwai wanda na rubuta, wandashi
idan kariga ka iya browsing, amma kana son Karin bayani game da yadda
akeyin wasu abubuwa a internet, misali:- yadda idan ka budo wasika daga Email dinka
zaka yi ka gano daga wane gari, ko wace cyber café a wace computa, wannan sakon
ya fito, ko yadda zaka shirya email dinka idan an aiko maka da wasika yarinka
mayar da reply ko baka kan internet, ko yadda zaka sa computer da kanta tabudo
ma email ko ta yi maka search din wani abu da kanta, duk nayi bayani a wannan
Hand out din.
To shi wannan Handout zai
taimaka maka ko baka taba shiga Internet ba, in ka bishi a hankali, daga farko
harkarshe, to Insha Allahu Zaka iya shiga Internet kai da kanka harma ka budewa
kanka sabon E-Mail Address, kayi browsing, ka iya binciko abubuwa dabam-dabam.
Sannan a wannan Hand Out din
nayi bayani gameda yadda ake shiga Internet daga cikin Handset, da yadda zaka
seta Handset dinka ta fara browsing, domin ko baka da lokacin da zaije cyber
café yayi browsing to ko kana wurin aikin ka, ko a’ina kake zaka iyayin
browsing, ta cikin Handset dinka, sannan nayi
bayani daki daki yadda zaka yi browsing din a handset, sannan kuma
yawancin abubuwan da zaka iya yi a computer, zaka iyayi a cikin handset din,
misali:- kaduba labaran da BBC zasu yi anjima, da sauransu.
Kuma na rubuta shine don
ganin yadda zamani yake, zaka ga ayanzu komai sai kaji ance Internet, hatta
idan Handset dinka ta kulle, zaka iya zuwa kabude tat a internet (zasu baka
nambobin da zakak danna ka bude ta), zaka ga ana ta abubuwa da dama a Internet
amma yawancin mutanemu basu sani ba, a yanzu hatta aiki, irin na
Gwamnati, da sauransu zakaga ta Internet ake nemanshi, (misali yanzu
akwai website din da zaka je, zasu jero maka sunayen Kamfanoni da suke neman
ma’aikata da irin ma’aikatan da suke nema, a lokacin kawai saida kacika form ka
aika musu idanm kayi sa’a sai su aiko maka adireshi, da wasu information din da
zakaje ka same su, sai kaga kasamu aiki, cikin sauki, batare da kaje kana
tashan wahala ba. To kaga duk irrin wadannan ba kowa bane ya sandasu, zaka ga
hatta idan rashin lafiya na damunka akwai inda zaka je, karubuta irin abubuwan
da suke damunka, sai kaga sunayemn magungunan wannan ciwon.
To duk sabo da haka ne nace bari in dan rubuta wannan
Handout din.
MANNIR AHMAD GETSO
GABATARWA GAMEDA INTERNET
MENE INTERNET
Internet (Internetworking),
wurine da ake shiga ta cikin computer, domin ayi bincike, ko a aika da sakwanni
zuwa kowace computa a duniya, a cikin dan kankanin lokaci.
Ta haka zaka iya aikawa
sakonni na sauti, ko na magana, ko na hoto, ko na bidiyo da sauransu, zuwa ko
wace computar da kakesonka aika, a duniya.
TA YAYA AKA SAMO INTERNET
Internet ansamo shine bayan
shekara 20 da suka wuce, samunshi ya samo asaline da wata hadakanyar Computa,
da majalisar tsaro ta amuruka da ake kira ARPAnet tayi, an hadane ta hanyar
harhada computer wuri daya domin su samu dammar aikawa da sakonni, zuwa kowace
computa cikin dan kankanen lokaci. Ta haka ne sai aka hada wayar computer da
layin telephone domin, aikawa da sakonni, zuwa kowane wuri na duniya, yadda
za’a iya aikawa da sakonnin ta daruruwan kilomitoci.
TA YAYA INTERNET YAKE AIKI
Shi
Internet yana aiki ne, kamar yadda wayar salula ta ke aiki, misali idan kana da
handset kana da namba, wanda da wannnan nambar zaka rinka aikawa da sakonni, ko
karban sakonni, misalign nambar sune 08051619043, to itama duk computer
da kayi connect tin dinta da Internet tan a da namba, wanda wannna nambar ita
ake kira, IP ADDRESS, (IP yana nufin INTERNET PROTOCOL).
Kowace
computa da nata misalign ip address shine 192.168.32.1
Shi Internet ta wurin aikawa
da sakonni yana amfani da wani abu wanda ake kira Internet Protocol shi
Internet protocol shine yake nuna DATA (information) dinka zasu ko daga ina
suke misali:- karubuta wasika a computa ta 192.168.45.2 zaka aika
192.168.87.45, ko idan zaka aika da wasika irin ta gargajiya bawai zakaje ka
ajje wasikar a post office bane, a’a yana bukatar karubuta adireshin da wasikar
zataje, to shima haka internet protocol yake a internet, yana da nambobi guda
hudu, kumka kowace namba tana kasa da 256, nambobin suna nan kamar haka:-
192.112.36.5 ko 128.174.5.6 kaga nambobin farko suna nuna daga wane
irin network sako yake, na dama daga karshe shike nuna daga wacce computa
bayanin yafito, misali:- kana kana cyber
café a computer ta 12 sannan network din su shine 128 kaga IP naka zai zama
128.XXX.XXX.12.
Idan baka gane misalign farko
bag a dan gajeren misali ko zaka gane:- misali kana da handset, da namba, sai
ka rubuta sako ka aika wa wani, shi wanda ka aikawan, ya cire layinsa daga
cikin handset dinsa, to lokacin da ka aika da wannan sakon, sakon zai ta fi
network (misali MTN), idan yaje can,
sai su ajje wannan sakon har lokacin da wanda ka aikawa sakon yasa layinsa,
yana sa layin sa, zai ga sakon da ka aiko mai, ya karanta. To shima Email haka
yake, idan ka budo email dinka ka, ka rubuta wasika zuwa ga wani, wanda ka
aikawa idan baya kan computer, to wannan wasikar zata ta fi wurin webserver (misali YAHOO), sun e zasu ajje wannan
sakon, har duk lokacin da wanda ka aikawa sakon yaje yabudo email dinsa, sai
sutoro maid a wasikunsa ga b daya , ya karantasu, zasu turo masa net a hanyar
WEB BROWSER (wanda zanyi Magana anan gaba), bayan sun turo masa shi kuma sai
yakaranta ta anan, web browser din.
TA YAYA ZAKA HADA INTERNET A COMPUTAR KA
Da farko kafin na fara Magana
akan, yadda zaka hada computer, da internet, an sake kawo misali. Game da
internet, misali:- Idan kasiya handset bazaka iya kiran kowa ba sai ka saka
layi amma zaka iya budo cikin ta, zaka iya kara suna ye, harma zaka iya rubuta
wasika amma ba zaka iya aikawa da wasikar ba sabo da baka sa layi ba, na biyu
idan zaka a layi zaka zabi, irin wane layi zaka sa, layin VMOBILE, ko MTN, ko glo, ko MTEL, su wadannan su ake kira Network
Service Provider, idan kasiya layin, ajiki ne zaka ga nambarka, wanda da shine
zaka iya kiran kowa, to itama haka
computa take, idan ka siya computa idan kanason Internet, zakasamu Intenet Service Provider (I S P).
=======================
ABUBUWAN DA AKE YI A INTERNET
1.
Bincike ta fanning ilimi mai zurfi, kamar su:-
Tarihin sahabbai, Tarihin yakukkunan da manzon Allah
yayi, Tarihin ka’aba, Tarihin sauran kasashe, Tarihin Al’umma da yarensu da
sauran abubuwa masu zurfi
Koyon karatu:-
2.
Akwai websites din dazakaje ana koyarma da karatu, har
a rinka baku
assignment, har in ka gama abaka certificate, idan kana son website duba feji
na ka duba karshen wannan Handout din TUNTUBE MU A.
3.
Neman magani
n wani ciwo:- idan wani ciwo na damunka akwai websites din dazakaje
karubuta abin dayake damun ka, idan kayi sendin, zakaga an aikoma
dasunayen magungunan wanan ciwon
4.
Neman Aiki:- akwai website da dama dazaka shiga
a Internet kanemi Aiki, kamar aikin Gwamnati, aikin typing kana zaune a gida,
da sau ransu. Idan kana son list din websites din ka duba karshen wannan
Handout din TUNTUBE MU A
5.
Siyayya:- a internet akwai websites din da zaka
rubuta abin da zaka siya a fadamaka farashin sa, in ma kana da credit card
kasiya idan daga kasar waje ne ayoma shippin dinsa zuwa Nigeria a fada maka
adireshin da zakaje ka karbi abin naka.
6.
Duba Taswira:- akwai websites da dama dazakaje
karubuta sunan local government dinku ko kauyenku akawo ma map din kauyen
gabadaya da hanyoyi duk, har wanda basan kauyen ba zaka iya nunamai hanyoin da
zai je gidanku.
7.
Aikawa da sakonni da karban sakonni:- ta
internet zaka iya aikawa da sakonni zuwa wurare dabam dabam, zaka iya aikawa da
sako daga website zuwa handest.
SAURAN ABUBUWAN SUNE:-
8.
Kallon labarai:- CNN, MSN etc Kallon Kwallon Kafa
9.
Jin Labarai:- BBC, MSN, etc
10. Yin abokanai daga kasashen
waje
11. Yin magana da mutum yana
ganin ka kana ganin sa.
12. Yin University ta Internet, (Degree)
INANE CYBER CAFÉ?
Cyber café wurine da aka tanada domin shiga Internet,
wurine da zakaga computoci duk anyi connectin dinsu da internet, idan kaje
wurin kana son kayi browsing zaka basu kudin iya awowin da kakeson kayi, sai su
baka wata takarda da take dauke da password din, wannan nambobin sune zakaje
karubuta su ajikin computa ka budo internet, zanyi bayani akan yadda ake budowa
nan gaba.
MENE WEB BROWSER?
Web browser itace softwayace
da zata baka damar budo, da ganin Shafuffukan
Yanr Gizo, wato Website,
Misalin web browser sune:- Microsoft
Internet Explorer, Opera, Netscafe Navigator, Mozilla, dasauransu.
ME AKE NUFI DA WEBSITE?
Website itace tarin Shafuffukan yanar Gizo, wadanda suke
dauke da bayanai na rubutu, ko hotuna, ko sauti, da abubuwa masu motsi. Wanda
nan zaka budo kakaranta bayanan da kake so.Misalan website sune, :- www.bbchausa.com www.yahoo.com www.google.com
, duk adireshin da kaga ya farad a www to website ne, www yana nufin World Wide
Web. Sannan zaka ga yawanci suna karewa da, .com (company), ko .org
(organization). Ko .net(network), da sauransu, ko kaga yak are da .co.uk wato
yana nufin ita wannan website din ta Engla ce, .co.ng, wannan website din ta
Nigeria ce, idan kanason cikakken bayani kaduba karshen wannna littafi.
MENE INTERNET ADDRESS?
Email address, abubuwane guda
wato Email da www, su wadannan suna karkashin wani abune da ake kira
domain name system, amfaninsa shine domin tantance adireshin yanargizo a
internet, misali, agari zaka samu akwai, unguwa a unguwa akwai layi a layi
akwai gida, to haka ma wannnan, misali www.yahoo.com
kaga wannan adirehi ne
BAYANI DAKI-DAKI GAME DA YADDA AKE SHIGA YANAR GIZO-GIZO
A wanan bangaren, zanyi
bayanine akan yadda zaka shiga Internet kayi browsing da yadda zakayi amfani da
mouse wurin yin browsing din, da fark bari nafara da mouse.
YADDA ZAKAYI AMFANI DA MOUSE
Shi mouse dashi ake amfani wurin motsa pointer din dake
cikin monitor (screen din computer), shine zakaga kana motsashi itama pointer
din na motsawa, kuma idan zaka rike mouse zaka rike shine kamar haka:-

Figure
1
sanan Idande kana browsing
idan zakayi click koyaushe karinka yin click din bangaren hagu, sannan idande
kana cikin website bazakayi click din wuri ba sai kaga pointa din ta zama hoton
hannu, duk inda kaga ta zama hoton hannu za’a iya shiga wurin, wato zaka iya
click a wurin, sanan inda zakayi click din zai iya zamowa rubutu ko hoto ko abu
me motsi, duk lokacin da kayi click akan abu zai bude ma wannan abun, misali:-
ka bude website din www.bbchausa.com
kana duba fejin sai kaga wani wuri an rubuta LABAUN SAFE to dakaje kan tsakiyar rubutun zakaga pointar
ta zama hannu, sai kayi click a wurin, to zai kaika shafin da aka kawo labarum
safen, sannan kada kamanta koyaushe zakayi click karinka yin click din bangaren
hagu na mouse din, sanan a wasu shafin zakakyi amfani da ENTER na kibod wurin
yin click, kamar a yahoo sign in zaka iya yin amfani da ENTER wurin click din
sign in din, kuma zaka iya yin amfani da mouse wurin yin sama da feji ko kasa,
zakazo can barin karshe na screen zaka wani arrow asama da wani akasa saikazo
kayin click akan aron zakaga fejin nayin sama ko kasa, idan kuma baka ganeba
zaka iya amfani da aron sama ko na kasa ajikin kibod din.
Sanan yanzu zan koma inyi
bayani daki-daki wurin shiga internet din.
1. NEMAN
DAKUNAN SHIGA YANAR GIZO-GIZO (CYBER CAFÉ).
Da farko idan kanason kashiga internet zaka tafi inda
cyber café take, wato inda zakaje kasamu mutane ana ta browsin kamar haka:-

sanan idan garin dakake babu
cyber café to zaka iya shiga Internet ta cikin Handset dinka zan yi bayani nan
gaba.
3. YADDA AKE SHIGAR DA PASSWORD DIN ABUDE DESKTOP
Idan kaje cyber café zaka
tambayi irin awar da kake so kayi yawnacin awa daya bata wuce N100, idan ka
basu kudin zasu baka watya ‘yar takarda wacce password din yake cikin ta, bayan
sun baka sai kazo ka samu computer da bakowa akai, zaka sameta kamar haka

Figure
2


wanan shi ake kira desktop.
YADDA ZAKA BUDO WEB-BROWSER KA SHIGA
Bayan ka budo desktop, sai kaduba inda aka rubuta daya
daga cikin wadannan:- Internet Explorer,
Fire Fox, Opera, Netscape Navigator. Da kaga daya daga cikin wadannan
sai kayi double click, idan bakaga ko wane ba sai kaje can kasa gefen hagu zaka
ga inda ka rubuta START sai kaje wurin kayi click, bayan kayi click sai
ka duba inda aka rubuta Internet Explorer, sai kayi double click akan wurin, idan kuma
baka ga kowanne ba sai ka tambayi masu lura da cyber café din. Bayan kayi click akan Internet Explorer
zakaga ta bude maka feji kamar haka:-

Ms Internet Explorer ita ce web browser din da tafi sauki
wurin shiga internet, kuma yawancin kowace cyber café kaje zaka samu suna da
internet explorer, don haka ko yaushe kaje browsin sai ka duba internet
explorer a desktop. Kuma ita internet explorer software ce, wani zai iya yin
tambaya yace wai mene internet explorer ko mene software, kuma mutane da yawa
suna mamakin wai tayaya computa take aiki, har im bakayi abu daidai ba tagyara
maka, harma kaga tana maka gargadi, to kafin im baka amsar wadannan tambayoyi
bari in dada fada maka wai menene computer kamar yadda na yi bayani a farko, to
ita dai computa duk abin dakaga tanayi to wannan abin sa mata akayi, duk wani
gargadiu dakaga tana yi to mutum ne yazauna ya shirya mata, wanan abin da ake
shirya mata shi ake kira program, sanan program din ake harhada wa ashirya mata
akirasu Software, ko kaima zaka iya shirya computer program na Hausa,
idan ka samata zakaga kowane abu da zata rinka nuna maka da hausa zakaga
tana yi, har gargadi duk da hausa, tambaya ma da hausa. Akwai wani software da
nashiray na hausa na yin maakin dalibai na makaranta, kana yin run din
program din a computa, zaka ga ta tambayeka da hausa; kamar haka zata tambayeka
maakin duka makarantar zakayi ko maakin wani aji zakayi?, idan ka zabi na aji, sai ta kara tambayarka.. daliban
ajin sunawane sannan darasi nawa kae koyarwa a ajin, idan ka shigar da
wanan zata tambaye ka daga maaki nawane mutum za’a sa ya fadi sanan tace shigar da maakin step by step sai ka
danna enter, idan ka gama ka danna ENTER, zaka ga taware maka suanan kowa
da maakin da yacoi da position din da ya zo, harma idan kana son kayi wa kowa
report shiit zata yi maka, kai dai akinka shine shigar da maaki. To kaga wannan
abin shi ake kira software, kuma akwai software dabam dabam danayi na hausa,
idan kana so, zaka iya aiko da email zuwa
manniruahmad@yahoo.com ko ka duba karshen wannan Handout din
TUNTUBE MU A.To kaga anan Ms Internet Explorer shima software ne wanda kamfanin
Microsoft takje shiryawa.
YADDA AKE BUDE SABON E-MAIL ADDRESS
Bayan kaje cyber café, kasiya
time ambaka password kashigar da password din ka budo internet explorer,
(fml=START—INTERNET EXPLORER). Sai ka duba can sama kusa da inda akarubuta Address,
sai kazo kayi click a wannan dogon layin, karubuta, mail.yahoo.com kamar haka:-

bayan ka rubuta sai kadanna Go
ko ENTER. Bayan kadanna enter zaka ta bude maka wani feji kamar haka:-

HANYOYIN DA ZAKABI KABUDO FORM DIN REGISTAR E-MAIL
NA YAHOO
Bayan yabudo maka fejin, sai
ka duba inda aka rubuta sign up sai kayi click bayan kayi click sai
kajira shi zai kawo maka form din yahoo registration, bayan ya kawo maka form
din yahoo registration,
YADDA AKE CIKE FORM DIN RIGISTAR YAHOO
yanzu sai kafara cike form
din kamar haka:-
AIKAWA DA FORM DIN
Bayan ka kamala cike form
din, sai kaduba inda aka rubuta I agree sai kayi click din wurin, bayan
kayi click din zaka dan cira har compuatr ta gama reading din form din bayan ta
gama bayan tagama in kayi dai dai zakaga ta kawo ma wani sabon feji an rubuta Registration
is Complete. Kamar haka

shi wanan fejin zaka iya yin
printing dinsa, idan kana son kayi printin dinsa kira masu kula da cyber café
din su yi maka printin din, in kuma zakayi dakanka sai kadanna FILE-PRINT.
KAMMALA REGISTER
Lokacin da ta nunama registration is complete, idan
kaduba kasan zakaga an rubuta continue to yahoo mail, sai kayi click din wurin,
idan kayi click din wurin, zakaga ya bude maka email din ka, zaka ga an rubuta
eg=welcome sager.
YADDA AKESHIGA E-MAIL
Shi E-Mail address zaka iya budeshi
a wurare kamar haka yahoo.com hotmail.com
mail.com lycos.com netaddress.com email.com
37.com. Kamar yadda nayi
bayani a baya, bayan kaje cyber café kaje harka budo internet explorer, zaka zo
kusa da inda aka rubuta address, sai karabuta mail.yahoo.com bayan
karubuta sai kadanna Go za’a budo
ma feji :-

bayan fejin ya bude, sai kazo
inda aka rubuta yahoo ID, anan sai karubuta email dinka ba dole bane sai
kasa @yahoo.com, bayan ka rubuta sai kadanna TAB ajikin kibod, ko kayi click
din inda aka rubuta password sai karubuta password dinka bayan karubuta
sai kayi click akan Sign in sai kajira yafude bayan yabude zakaga an ma Wellcome,
idan kuma by bude ba to kayi mistake din wani harafi, sai kasake shigarwa.

IDAN ZAKA KARANTA WASIKA
Idan zaka karanta wasika, sai
kayi click akan inda aka rubuta inbox, ko kuma CHECK MAIL ko inda
aka rubuta You have xx unread message, sai kayi click din wurin, bayan
kayi click ta jero maka wasikun dakake dasu sai kazo, kan wasika, kan abin da
wasikar ta kunsa sai kayi click, kana yin click zakaga wasikar ta bude sai ka
karantata.
RUFE WASIKA BAYAN ANGAMA KARANTAWA
Bayan ka gama karanta wasika,
idan zaka goge sai ka danna DELETE zaka ganshi a saman wasikar ko a
kasan wasikan,in ka gama karantawa sai kadanna CHECK MAIL or INBOX.
IDAN ZAKA RUBUTA WASIKA
Lokacin daka bude email
dinka, idan wasika zaka rubuta sai kazo sama bangaren hagu zaka ga inda
akarubuta COMPOSE sai kayi click
bayan kayi click zai bude maka wani feji kamar haka:-

Kara girman rubutu
Idan zaka rubuta wasika kana
son ka kara girman rubutun, zaka duba sam kadan cikin inda kake rubuta wasikar,
zakaga karamar A da babban A inkaje wurin kafin ka danna zakaga an rubuta Front
Size sai kayi click din wurin, sai kazabi rin girman rubutun dakakeso.
Sa kala a rubutu
Idan kanason kasawa subutun dakake yi kala, zakaje jerin
layin daka dauko na baya, inda kaga anyi wani T , kafin kayi click zakaga
anrubuta text colour, sai kayi click din wurin, zai kawomaka kaloli sai kazaba
kalan dakakeso kayi click.
Saka hyperlink a rubutu
Shi hyperlink rubutu ne,
wanda idan kadanna rubutun zai kaika websites din da aka rubuta a jikin wannan
hyperlink din, misali wani abokinka ne baisan ebsite din Google ba sai kana son
ka aika masa da website din ta cikin email dinka, sai kazo jerin wurin da
kadauko sauran zakaga inda akayi hoton kamar duniya da wani abu kamar akwa
ajikin, kafin kayi click zakaga an rubuta create hyperlink sai kayi
click din wurin, amma farko sai karubuta website din misali Google (sai kayi highlight dinsa) bayan karubuta sai
kasa mouse dinka a gaban G sai kadanne sai kaja harzuwa e zakaga yai baki sai kaje wurin creat
hypalink kayi click sai karubuta website din eg= www.google.com sai kadanna ok, duk acikin
wasikar zakayi wannan.
Sa Attach File
Attach file ana sashine idan
kanson ka aika da hoto ko wani file daga computer dinka, idan kanason ka aika
da attach file lokacin daka budo wasika zakaga wani wuri anrubuta Attach
files sai kayi click a wurin zai budo maka wani wuri sai kayi click akan browse
bayan kayi click saika zabi file dinda zaka aika bayan kayi click akan file
din sai kayi click akan open sannan sai kayi click din attach files sai kajirata ta gama loda file din sai kayi
click akan continue message sai kaci gaba da wasikarka.
AJJE WASIKA A DRAFT
Idan kana rubuta wasika sai
baka gamaba kuma kaga lokacin ka ya kusa karewa ko kana son ka ajje wasikar
bayanzu zaka aika da itaba, zaka iya ajje ta a draft lokacin da kadawo kaci
gaba da rubuta ta sannan sai ka aika, yada zaka ajje abu a draft shine, lokacin
da kake rubuta wasika idan kaduba saman wasikar zakaga inda aka rubuta SAVE
AS DRAFT to nan zakayi click sai ta ajje ma wasikar duk randa kazo sai kaci
gaba.
IDAN ZAKA DAUKO WASIKA DAGA DRAFT KACI GABA DA RUBUTA TA
Duk lokacin daka zo kabude
email dinka, idan zaka budo wasika daga DRAFT saika duba inda aka rubuta DRAFT
sai kayi click din wurin bayan kayi click din wurin zaka ga anbudoma jerin
wasikun daka ajje su a draft sai dai kawai kayi click akan wasika kaci gaba da
rubutata.
AIKAWA DA WASIKA
Lokacin dakagama rubuta
wasika gabadaya, sai kazo inda aka rubuta To: sai ka rubuta adireshin wanda zaka aikawa
da wasikar awurin, eg= To: manniruahmad@yahoo.com idan kuma zaka aikawa da mutane da
yawa sai ka rubuta email din na farko saikasa comma “ ,
“ misali zaka aikawa da mutum
biyu mannirgetso@yahoo.com,sagir13131@yahoo.com
haka zaka tajera sunayen email din kana raba su da kwama. Bayan ka gama
rubutawa sai kaduba sama zaka ga inda aka rubuta SEND sai kayi click din
wurin, idan wasikar ta tafi zata nunama Message Send ,
IN ZAKA GOGE WASIKA
Kamar yadda nayi bayani da
farko I dan kana sonka goge wasika sai ka danna DELETE ko kayi check din
wasikun da zaka goge wato kayi musu good (wani dan box zakagani lokacin da ka
bude wasikunka dan wannan karamin box din sai kazo cikinsa kayi click ) , bayan
kayi check din ko wane wasika sai kadanna DELETE zai goge maka wasikun
dakayi check din nasu.
YADDA AKE NEMO WASIKA
Misali wani yaynka ya aiko ma
da wasika acikin wasikar ya aikoma da
nambobin scratch card na NECO sai baka ga wasikar ba kuma shi yace ya turo ta,
to lokacin daka budo E-MAIL din ka zakaga inda aka rubuta SEARCH MAIL a hagu da wurin zakaga
wani dogon box sai kayi click acikin sai ka rubuta NECO ko karubuta PIN bayan
karubuta sai kayi click akan SEACH MAIL, in dai wasikar tana email dinka
zaka ga ankawo ma ita, sai dai kawai kayi click akan wasikar ta bude.
YADDA AKE AIKI DA MICROSOFT OUTLOOK DA OUTLOOK EXPRESS
Ms Outllok da Outlook express duk ku san aikin su daya
ne, bambancin shine, shi ms Outllok zaka
iya budo shafin yanar gizo, da Kalandu
da sauransu, Shikuma Outlook Express sai dai kakaranta, wasiku da wsu abubuwa
da zanyi bayani nan gaba, Idan Kabudo Ms outlook zaka ganshi kamar
haka:-

Shi kums Ms Outlook Express
Idan ka budo shi zakak ganshi kamar haka:-

A wannan Handout din zanyi
magana akan Outlook Express, Da farko kafin mufara bari nayi magana akan Amfaanin Oulook Ko mai
ya sa ake amfani dashi:-
v
ZAKA IYA SHIRYA WA OUTLOOK
RULES, YADDA ZAI YA REPLY DIN DUK WANI
MESSAGE DA AKAYO MA, misali zaka iya shirya mai cewa, Duk sakon da akarubuta, ko akwai wata
kalma acikinsa, ko ya fito daga wurin wane, ko ya kunshi, ko wannan sakon an
aikawa wa wani bayan ka, zaka iya shirya shi duk daya daga cikin abin nan idan ya faru, zaka
iya shirya wa akan:- amayar da sakon, ko amayar da sakon dauke da wani file, ko
a goge sakon, ko akaio sakon wani wuri, ko a wuce da skon, zuwa wani mutum, duk
zaka iya shirya wadannna da outlook express, Iidan baka gane misali na
farko ba ga wani misali:- zaka iya shiryawa outlook cewa duk wasikar da akaturo
maka idan an turawa wane ita to a goge wasikar, ko kuma a share waikar ko kuma
akai wasikar wani wuri, misali a yanzu a emai dina, idan ka aika da wasika, a
subject karubuta HANDOUT , to zaka ga
anyi mareply din wasikar , dauke da
Handout, to kaga ta haka zaka iya zama ka shirya abu, mai bam mamaki, misali idan idan ka iya VBA Programming, zaka iya
shiryawa, da outlook, cewa duk lokacin da aka bude file kaza to ya aika maka,
da wasika dauke da sunan wanda yabude file din da time&date din da ya bude
wannan file din, ko misali zaka iya shirya da Excel, cewa idan cell kaza ya
haura kaza to ya aika da email (idan baka gane wannan ba ga dan gajeran
misali), misali ace kana aiki ne a ma’aikatar Internet Service Provider (irin
aikin da nake yi). Misali kuna da worksheet(ms Excel), dauke da sunayen
customer da date din da suka fara da kuma iya yawan watannin da suka biya, to
da wannan worksheet din zaku iya shirya VBA da Outlook, yadda idan customer
sauransa kwana kaza to a, aika mai da wasika akan cewa time dinsa sauran kwana
kaza, to kaga idan aka shirya wannan ba sai ansha wahalar bin customer ba, shi
da kansa zai ga wasika,
v
Misali na Biyu shine, Da outlook zaka iya shiryawa, idan kaza ya faru
to computer tayi kaza, misalii zaka iya shiryawa idan anyo wasika, dauke da
kaza to computer ta kasha kanta, da haka zaka iya shiryawa computer ka idan
karubuto wani sako daga handset dinka to ta kasha kanta, kaga ta haka zaka iya
shiryawa idan, misali kafi ta daga office dinka kamanta computer ka abude zaka
iya rufeta daga handset, ta haka zakaji mutum yace ai na rufe computa ta daga
handset dina,
v
Misali a Uku shine misali kana da Computa, baka son kowa ya taba maka
kuma zaka yi tafiya to zaka iya, shirya macro da outlook yadda idan antaba maka file, computer zata yi
record din duk abin da akayi a kwamfutar ta aika maka zuwa email dinka kai kuma
daga can inda kake zaka iya budowa kaga abubuwan da akayi maka a computa, wannan shine misalin macro din da nakera
wanda, da zai iya record din duk abubuwan da kayi a computa 

v
Akwai abubuwa da dama masu dim binyawa da zaka iya yi, da outlook wa
dannan kadan na lissafo idan kanson cikakken bayani kaziyarci www.mannir.8m.com
YADDA ZAKA SETA OUTLOOK DA EMAIL DINKA
Da farko kafin kafara aiki da
outlook sai kaseta shi yadda zai rinka download din email dinka daga server.
Yanzu kuma zanyi magana akan yadda zaka seta outlook, ka fara aiki da shi zaka
bi step kamar haka:-
START-ALL PROGRAMS (KO
PROGRAMS )- OUTLOOK EXPRESS sai kayi click akan outlook express bayan kayi
click sai kabi wadannan steps din TOOLS-ACCOUNTS-ADD-MAIL sai karubuta sunan da
kakeson yarinka nunawa sai NEXT sai karubuta email dinka sai NEXT a wurin Mai
Incommin Mail Server saika zabi POP3 wurin incommin mail sai karubuta mail.yahoo.com sannan a wuri outgoing mail sai karubuta mail.yahoo.com
sai NEXT sai karubta email dinka sannan sai karubta password dinkasai
kadannna NEXT sannna sai ka danna FINISH da ganan ka gama seta email dinka a
outlook, anan zaka ga inda zaka rubuta wasika aikawa da wasika da sauransu,
idan kanasonkarin bayani ka ziyarci www.mannir.8m.com
Annan zan dakata akan
outlook, idan kanason cikakken bayani kanemi littafin da na rubuta mai magana
akan Ms outlook.
BAYANI GAMEDA CHATTING
MENE CHATTING?
CHATTING wata hanyace dazukuyi magana da mutum ta hanyar
rubuta wa juna sako, ta hanyar rubutu dakuma ta hanyar sauti da kuma gani, wato
zaku iya magana da mutum kana ganin sa yana ganinka.
Kuma shi chatting hanyace dazaka hadu da abokanai
daga kasa shen waje. Kuma shi chattin amfi yawan yinsa ta hanyar rubuta wa
mutumn sako, misali ka hadu da wani dan SAUDIYA sai ka rubuta mai assalamu
alaikum, a lokacin shima zai rbuto ma, wa’a laikumussalam, a haka zaku yi ta
magana dashi, idan yana da webcam zaka iya ganinsa, idan kaima kana da webcam
zai iya ganinka,
ME AKEYI A CHATTING?
Abubuwan da akeyi a chattin
suna dayawa, anayin kamar su:-
1.
Kasuwanci.
2.
Haduwa da Likitoci kana tambayarsu cututtuka suna baka sunayen
magunguna na cututtukan.
3.
Haduwa da malamai (irin mallam saudiya) kana tambayarsu wasu abubuwa
suna baka amsa.
4.
haduwa da Malamai na book.
5.
Haduwa da abokanai daga kasashe dabam dabam.
6.
Yin aiki (na cika form, typing da sauransu), ana biyanka.
7.
Mitin(kamar wata ma’aikata zata iya yin mitin idan ma’aikatan nata suna
nesa da juna.
Da sauransu. Yawancin abubwan da akeyi anayinsu ne ta hanyar aikawa da sakonni ta rubutu magana gani(webcam).
MENENE AMFANIN CHATTING?
-
Amfanin chatin ya na dayawa sosai domin tanan zaka iya
koyan karatun haddar Alkur’ani mai girma.
-
kuma zaka iya haduwa da likitoci kana tambayarsu magungunan cututtuka
suna baka amsa kamar yadda nayi bayani.
YADDA AKE SHIGA CHAT (YAHOO MESSENGER)
Shi chattinj dabam yake da
E-Mail da Browsing, shi bayan kabudo desktop, maimakon kadanna Internet
Explorer, shi sai dai kadanna YAHOO MESSENGER , zaka ganshi a nan
desktop ko idan ka danna START—YAHOO MESSENGER, idan baka ganshiba sai ka
tambayi masu kula da cyber café din, kuma shi double click zakayi akanshi(nb=
duk lokacin dazakayi click akan yahoo messenger ko waninsa ka dena click akan
rubutu akan hoton zaka rinka click), idan kayi double click akan Yahoo
Messenger zai budo ma hoto kamar haka:-


bayan yabude maka saika duba
can sama inda aka rubuta MESENGER sai kayi click din wurin sannan kayi
click din YAHOO CHAT sannan JOIN
A ROOM, idan baka gane ba to kaduba sama inda akayi wani abu kamar hoton
handset da kan telephone akan layin idan kaduba bangaren dama zaka ga wani
alamar arrow guda iyu kamar haka irin wannan guda biyu É,
idan kaje kan arrow din sai kayi click bayan kayi click sai kayi click akan CHAT
sai kajirashi yabude, in baibude ba sai kasake zuwa wurin wannan arrow din
ka sake click.
YADDA ZAKA ZAFI CATEGORY DA ROOM KASHIGA
Bayan ya bude zaka ga ya budo
maka wani wuri kamar haka:-

zaka ga jerin CATEGORIES sai
kazabi category din da zaka shiga sai kayi click (misali= SCHOOL &
EDUCATION), bayan kayi click zai
sake jero maka jerin ROOMS anan ma sai ka zabi room din da zaka shiga (misali:-
study group), bayan kayi click sai kadawo kasa zaka ga inda aka rubuta Go to
Room sai kayi click, zakga yabudo maka wani feji zaka jira harwani dogon
abu yacika bazai wuse sakan 10, sai kayi click akan Enter Chat .
YADDA ZAKA GA YAWAN MUTANEN DA SUKE CIKIN CHAT ROOM
Bayan kadanna ENTER CHAT zakaga
an bude maka chatroom din kamar haka:-

idan ka duba bangaren dama
Email din wadanda suke cikin dakin ne.
Idan kaduba wadanda suke
bangaren dama kuma zakaga wadansu kamarsunsa headphone wasu kuma kamar suna
cikin tibi, wasu kuma ba komai.
Wadan da suke da abu kamar
headphone zaka iya magana dasu, wato suna (voice chat).
Su kuma wadanda suke cikin
tibi, zaka iya ganin su, wasu kuma har zaka iya ganinsu kayi magana dasu.
Idan kana son kaji bayanin
yadda zaka iya ganinsu ko kayi magana da mutum ka duba karshen wannan Handout
din TUNTUBE MU A.
YADDA AKE DUBA MUTANEN DASUKE CIKIN CHAT ROOM DA IRIN ABUBUWAN DA SUKE RUBUTOWA
Idan kaduba bangaren dama
kuma, nan kuma zakana ganin rubutu na tafito wa (misali mannir: joint the
room), wato anan nunama yanzu mannir ya shigo dakin chatin din, kuma anan
ne zakaga kowan rubuto abin da yaga dama
(misali mannir: akwai wani bahaushe kuwa?), to kaga ananne idan kana son
kayi wa mutum magana sai kaje kan emaildinsa kayi double click.
YADDA AKE TABO MUTUM A CHATTING
Abagaren dama zakaiya ganin
wanda kasan email dinsa, ko wani wanda kake son kuyi cattin dashi, yanda zakayi
shine kaje kan email din mutum a bangaren dama kayi click, sananna sai kayo
kasa kayi click akan inda aka rubuta IM, bayan kayi click zaka ga wani
window ya fito, to a wannan window din zaka rinka rubuta abinda zaka aika wa
wancandin, misali zaka iya rubuta mai Hi sai kayi send ko kadanna ENTER.
YADDA AKEYIN CHATTING
Bayan kayi click akan ID din
mutum, kuma kayi click akan IM, wani window ya fito kamar haka:-

sai kazo nan kasa sai kayi
click, sai karubuta Hi, sai kayi ESND ko kadanna ENTER, sai kajira kaga reply,
yana dawo da reply zaka ga bottom toolbar yayi ja, sai kayi click din wurin.
Reply din zaka iya ganin sager:Hi ko
asl?, idan kaga msl asl?, yana tambayarka shekarunka nawane sannan
kai namijine ko mace sannan a wane gari kake, shine ma’anar asl, zan yi bayanin
irinsu nan gaba, to ta haka zaku ta communication da mutum, idan kana son
kayganshi saika ka duba karshen wannan Handout din TUNTUBE MU A.
WASU KALMOMIN CHATTING DA MA’ANONINSU
Akwai kalmomin da ake amfani da su a wurin chattin don
rage dogon rubutu, misali:-
-
Name? = yaya suanan ka, Ko ya sunan ki.
-
Age? = shekarun ka/ki nawa.
-
Country? = a wace kasa aka haife ka/ki?.
-
Location? = a ina ka/ki ke yanzu.
-
Asl? = shekarun ka/ki nawa, na miji ne kai ko ke mace ce, a ina ka/ki
ke yanzu?.
-
Asl plz? = don Allah shekarun ka/ki nawa, na miji ne kai ko ke mace, a ina kaki ke yanzu.
-
M/f? = Namiji ne ko mace.
-
Dasauransu
A lokacin da kuka fara chattin da mutum zaka iya ganin ya
rbuto maka:- asl?, wato yana nufin kai waye, namiji ne ko mace kuma shekarunka
nawa, kuma a wace kasa ka ke ko kike. Akwai abubuwa da dama da ake rubutawa
wurin chattin nan kadanne daga cikin su.
IDAN KAYI ABOKI ZAKA AJJE SHI A MESSINGER LIST
Idan kuna cattin da mutum sai
kanason ka ajje shi a messenger list(wurin da zaka ajje email din mutane, yadda
duk lokacin daka shiga yahoo messenger zaka iya gane mutum yana kan computer ko
baya nan), lokacin da kuke chattin da mutum din idan ka duba saman dakin shi
wannan mutum din zaka ga wani hot kamar kai anyi alamar Tarawa ajikin kan to
nan zakazo kayi click, zaka ga ya bude maka, wani feji sai ka danna next har
sau biyu na karshen sai kadanna Finish, bayan ka gama zakaga sunan email
dinsa a jikin yahoo messenger dinka, kuma zaka iya zuwa da Email adireshin wani
, ka ajje a messenger list, kamar yadda zanyi bayani nan gaba.
YADDA ZA’A AJJE E-MAIL DIN MUTANE A MESSENGER LIST
Zaka iya samun Email
adireshin din abokinka ka ajje shi a messenger list yadda duk lokacin da kahau
computer, zaka iya ganewa shima yana kan computa ne ko bayakai, misali kasamo
email adireshin manniruahmad@yahoo.com idan ka budo yahoo messenger sai kaduba inda
akajera hoton su handsets da sauransu zaka ga wani abu Kaman kan mutum da
alamar Tarawa ajikin abun, sai kayi click a wurin zai bude maka wani wuri, sai
karubuta email adireshin bayan ka rubuta sai kadanna next harsau biyu
daga karshe sai kadanna finish, zakaga email dinsa ya fito a cikin yahoo
messenger dinka.
YADDA ZAKA GANE ABOKIN KA YANA KAN
COMPUTER KO BAYANAN
Duk lokacin da kashiga yahoo messenger, idan ka ajje
Email adireshin mutane a messenger list, to a farkon sunan kowa zakaga hoton
wani abu kamar kan mutum, to duk kan dakaga yayi kala wato yayi kalar dorawa to
wannan mai Email din yana kan computer wato yana cikin chattin, wadanda kuwa
kaga basu da kala to basa kan computer, ta haka zaka iya gane aboinka yana kan
computa ko bayanan, im ma bayanan zaka iya rubuta mai sako yadda duk lokacin da
yahau kan computa zai ga wannan sakon.idan kana son karubuta wa mutum sako zaka
je kan email adireshinne saikayi double click bayan kayi double clcik sai
kajira ya budo maka wani kjaramin window bayan ya budo maka window din sai
karubuta abin da zakarubuta sai kayi send.
YADDA ZAKUYI MAGANA DA MUTUM KANA GANIN SA YANA GANIN KA
Idan kanasonka yi magana da mutum kuma kana ganinsa, da
farko bayan kaje cyber, zaka duba computer idan tana da webcam idan kuma bata
da webcam, sai ka tambaye su suna da webcam, da microphone/speaker , zasu sam
ka shi abayan computer bayan sunsa maka, lokacin da kabudo YAHOO MESSENGER,
lokacin da kuke chattin da mutum idan kaduba saman dakin da kuke chatting din
zaka ga inda aka rubuta action sai kayi click din nan, ko kuma file kaduba inda
akarubuta webcam sai kayi click din nan, daganan, zaka ga inda aka rubuta CALL
sai kayi click sai kajira wancan ya amsa, idan shima yana da webcam din.idan
baka gane ba ka ziyarci www.mannir.8m.com
BINCIKO BAYANAI A INTERNET
YADDA ZAKA BINCIKO BAYANAI TA CIKIN INTERNET
A wanna
shafin zanyi bayani ne akan yadda zaka binciko bayanai ta cikin Internet. A
wajen nemo abu acikin Internet ana amfani da wasu abubuwa guda biyu wadanda ake
kira:-
Directories da Search Engines.
Shi Directoies ana amfani dashi wurin nemo wani
abu kebantacce, misali abun yashafi magana ne ta Doctors, ko Computer
Programmers, ko Engioneer, da sauransu, to idan ain dazaka nemo ya danganta da
misalansu ne kamar yadda nakawo, to zakayi amfani da DIRECTORIES wurin nemo
bayanan ka, misalan adireshin DIRECTORIES kuwa sune:-
www.searchsystem.com www.directories.goole.com www.dir.yahoo.com
.idan kanason cikakken bayani gameda DIRECTORIES dakuma jerin sunayen Adireshin
su saika ka duba karshen wannan Handout
din TUNTUBE MU A.
Yanzu kuma zanyi bayani a kan Search Engines.
Da farko
Idan zaka binciko bayani ta cikin Internet zaka iya iya nemo bayanin da hausa I
dan abin yashafi hausa, sanan zaka iya nemo shi da turanci, misali zaka iya
tambayar “Labarun BBC hausa” akawo maka bayani akan Labarun BBC din.
MENENE MISALIN ABUBUWAN DA ZAKA IYA NEMOWA A INTERNET
……………………………………
MENE SEARCH ENGINES?
Search Engines wasu Websites ne wadanda wadanda ananne
zaka rubuta abin da kake nema, sai su binciko makashi, yawanci idan ka budo
search engines zaka ga akwai wani dogon layi wanda acikin layinne zaka rubuta
abin da kake nema sai ka danna ENTER.
ADIRESHIN WASU SEARCH
ENGINES
Search Engines da suka fi sanuwa kuma sukafi nemo abubuwa ciki sauri Kadan daga cikin su sune:-
ALTAVISTA = Zanyi bayani akansa nan
gaba.
GOOGLE = Shima zanyi bayanin sa nan
gaba insha Allahu.
ASKJEEVES = Shi wannan taskar binceken
shima yana daga cikin adireshin da zakaje karubuta ain da kake nema, yakawo
maka, misali an baku assignment a makaranta anan ne zakaje karubuta abin da aka
tambayeku ya baka amsar abin, in kana son cikakken bayani akan sauran websites
din da zakaje karubuta assigment a kawo maka amsa karubu wasika zuwa ka duba
karshen wannan Handout din TUNTUBE MU A.
WASU MANYAN SEARCH ENGINES
Su wadannan search engines su
ake kira meta search engines, su idan kasa su nemoma wani bayani, suma
zasu sa sauran manyan search engines su nemo musu sai sukawo maka abin da
kowane search engines ya nemo, ka dan daga cikin su kuwa sune:-
Idan kanason gabadayansu karubuto ka duba karshen wannan
Handout din TUNTUBE MU A.
YADDA ZAKA BINCIKO WANI BAYANI A GOOGLE
Idan zaka budo Google, zaka
zo kusada inda akarubuta Address sai karubuta www.google.com sai kadanna Go ko
kadannna ENTER, bayan kadanna zai budo maka feji kamar haka:-


Amfani da alamar “
“ =sai kuma abu na biyu lokacin
dakayi wancan search in zai iya kawo maka website din da akayi magana akan labrun
daga baya kuma akayi magana akan hausa, to saboda magance irin
wannan matsalar zka iya amfani da wadannan alamun “ “ , yanda zakayi shine kafin karubuta abin
dakake nema sai kafara dannan wanan alamar (
“ ), (yadda ake dannata shine
zaka danne SHIFT sai kadanna alamar tana nan kusa da Enter), (kamar haka
“labaran safe” ), bayan karubuta abin dakake nema sai kasake danna ta, bayan
kagama sai kadanna ENTER, zai kawo maka fejinan da asali akayi magana akan
“labaran safe” . Abin dazaka lura anan shine, misali kana neman inda akayi
maganar mannir ahmad ne a internt, idan kaje google karubuta mannir ahmad baka
sa wannan alamun ba to zai kawo maka websites da akayi magana akan mannir daga
baya kuma akayi magana akan ahmad, amma idan kasa wannan alamun zai kawo ma
asali inda akayi ayi magana akan “mannir ahmad”. Binciken abu a internet yana
bukatar sanin ka’idojin bincike domin sai kaje kata bata lokaci baka samu
takamaimai abin dakake nema ba, domin Karin bayani gameda yadda ake nemo
abubuwa ta internet ka ka duba karshen wannan Handout din TUNTUBE MU A.
YADDA ZAKA NEMO HOTO A GOOGLE
Idan hotuna kakeson
kanemo,kamar hotunan handsets ko na gidaje kowane irin hoto dai, farko bayan ka
budo google.com, idan kaduba saman dogon layin zaka ga inda aka rubuta Images
sai kayi click din wurin bayan kayi click din, misali kanason hadset na
Samsung, sai kaje kayi click akan dogon layin, sai karubuta Samsung
mobiles kana rubutawa sai kayi click
akan search, ko kadanna ENTER, zakaga an kawo maka hotunan handsets din Samsung
iri-iri, to misali ace kanason kasiya handset din ne, kana son kasan kudin
handset din idan kazo zaka rubuta “Samsung mobiles”+price sai kadanna
ENTER, idan aka kawo maka hotunan sai kazabi iri wacce kakeso sai kayi click,
za’a kaika inda aka fani farashinata. Misali kanason kasiya nokia 6600 ne zaka
rubuta haka:- nokia mobile+6600+price+Nigeria idan karubuta sai kadanna
ENTER, zakaga ankawo maka hoton handset din sai kayi click akan Handset din
zaka, zaikai ka inda akafadi farashin handset in a Nigeria. Idan kanason
cikakkaen bayani gameda yadda ake searchin din image ka duba karshen wannan
Handout din TUNTUBE MU A.
YADDA ZA’A NEMO ABU A ALTAVISTA
Yadda Altavista take zaka
ganta kamar haka:-

NB=IDAN KANASON CIKAKEN
BAYANI GAMEDA YADDA AKE NEMO ABUBUWA A INTERNET KA AIKA DA SAKO ZUWA:- manniruahmad@yahoo.com ko ka duba
karshen wannan Handout din TUNTUBE MU A.
YANAR GIZO TA HANDSET
YADDA ZAKA SHIGA YANAR GIZO-GIZO TA CIKIN WAYAR TAFI DA GIDANKA
( how to Browse on your
mobile phone)
Zaka iya shiga Internet ta cikin wayar tafidagidanka (handset), zaka iya
binciko bayanai, zaka iya siga E-Mail dinka, zaka iya yin CHATTING, zaka iyayin
Dowloading din game, da sauran abubuwa da daama. Duk handsets din da kaga tana
da daya daga cikin wadannan :- gprs, wap, wap browser, www service, internet,
to wannan Handset din zaka iya browsing da ita. Da farko kafin kafara browsing
a handset dinka sai kayi abubuwa guda biyu, farko sai network din da kake
amfani adshi sun yi activate din layinka, kuma ka seta handset naka (zanyi
bayanin yadda akeyi nan gaba).
ME AKE NUFI DA “WAP” “GPRS” “CSD”
·
WAP (Wareless Application Protocol), ita
kamar software ce da zata iya baka damar ganin abubuwan da suke internet ta
cikin handset dinka, kamar Internet Explorer ne a computer, idan baka da web
browser (Internet Explorer) bazaka iya ganin shafuffukan da suke cikin Internet
ba, to haka ma wap browser take.
·
GPRS
(General Packages Radio Service) shi kuma tananne za’a yi connectin handset
dinka zuwa Internet, bayan GPRS akwai wasu hanyoyi da za’a iya connecting dinka
da internet, don haka kafin kafara yin browsing sai anyi activate din GPRS
alayinka tukun.
CSD(Circuit Switch Data) kamar gprs ne ana connecting
dinka ta data ne, sai dai shi zakayi kamar calling ne yafi gprs ciran kudi
TA YAYA ZAKAYI ACTIVATE DIN WAP/GPRS A HANDSET DINKA
Kamar yadda nayi bayani da farko cewa:- kafin kafara
browsing a handset dinka sai kayi
abubuwa guda biyu, na farko shine sai kayi activate din GPRS a layinka, na biyu
sai kaseta wap acikin handset dinka, idan kana son kayi activate din layinka
abune mai sauki, zakakira CUSTOMER CARE na layinla sai kace musu “ I want
activate wap gprs”, zasu yi maka bayanin yadda zakayi.
IN KANA DA LAYIN MTEL
Idan kana da layin mtel kanason ayi activate din WAP/GPRS,
zaka kira Customer care ne kamar yadda nayi bayani a baya, sai kace musu “I
want activate gprs”.
IN KANA DA LAYIN VMOBILE
I dan kana da layin VMOBILE
kanason kayi activate wap, abin da zakayi shine, zakayi masu message ne sai
kayi send, zasu aiko maka da message din ta OTA (Over The Air ), wato
zasu aiko ma da setting din komai, idan sun aiko maka sai kayi save din abinda
suka aiko maka, Abin da zaka rubuta
shine:-
Idan Handset dinka bata da
camera, kuma kana zaunane a Lagos
zaka rubuta masu message, abin da zaka rubuta kuwa shine:- wapgprs kayi send zuwa 184, idan
kuma handset dinka tana camera, zaka rubuta wapgprs2 kayi sned zuwa 184,
Idan kuma ba acikin garin
Lagos kake ba zaka rubuta wapcsd2 kayi
send zuwa 184 idan Handset dinka tana da camera, Idan kuma bata da
camera zaka rubuta wapcsd kayi send zuwa 184, idan kuma
setting mms kakesonyi shima zakayi kamar sauran ne amma shi zakarubuta mms a
inda karubuta wap, misali:-
mmscsd2, Idan kayi haka basu aiko
maka da komai ba sai ka kirasu a customer care., idan kana son Karin bayani, ka
aikomin da wasika zuwa manniru@gmail.com
IN KANA DA LAYIN GLO
Idan kana da layin GLO kanason kayi activate din GPRS a handset dinka, abin
da zakayi shine zaka rubuta message sai ka aika masu zasu aiko maka da setting
din, abin da zaka rubuta shine:- activate wap
<kamfanin handset dinka>
<model din handset dinka> sai kayi send zuwa 927, misali:- activate wap nokia 6600 kayi send zuwa 927, idan kuma ka aika basu aiko maka da komai ba har
bayan kwana uku sai ka kirasu a CUSTOMER CARE 121
IN KANA DA LAYIN MTN
In kana da layin MTN kanason
kayi activate din “MTN WAP” shima zakarubuta message ne zaka rubuta:- settings kayi send zuwa 3888 in
ka aika basu aiko maka da komai ba har bayan kwana 1, sai kasake rubuta settings
amma shi zakayi send zuwa 4777, idan duk kayi haka basu aiko mada
komai ba sai kakira shu a CUSTOMER CARE 180 sai kace masu “I want
activate mtn wap/gprs” zasu yi ma bayanin yadda zakayi.
IDAN KANA DA NOKIA, SONY
ERICSSON, SIEMENS, KO MOTOROLA, KA ka
duba karshen wannan Handout din TUNTUBE MU A, IN SHA ALLAHU ZAN AIKOMAKA DA
SETTING TA CIKIN OTA(OVER THE AIR).
WADANNE IRIN ABUBUWA MUTUM ZAI IYAYI IDAN MUTUM YA SETA HADSET DINSA TANA WAP/GPRS
Idan ka seta Handset dinka
tana wap/gprs zaka iya:-
-
Shiga Internet kayi Browsing kamar yadda zaka yi a computer
-
Download din Games Iri-iri.
-
Download din Ringtons.
-
Download din Wallpaper, picture da sauransu
-
Koyon Karatu
-
Chatting
-
Da sauran Abubbuwa dabam dabam
YADDA ZAKAYI BROWSING A HANDSET DINKA
Awannan shafin zanyi bayanine akan yadda zakayi browsing
a handset dinka. Idan zaka shiga Internet a handset dinka, zaka tadanna menu
harka kamo inda kaga an rubuta daya daga cikin wadannan:- www service, wap browser, Fun box,
Internet, wap, gprs, service. Bayan kaga daya daga cikin su sai kadanna Ok
(misali in Samsung gareka zaka danna,
MENU—FUN BOX—WAP BROWSER—HOME PAGE), bayan ka danna OK sa kadanna, Home
Page, to daga nan sai kajira network suyi connecting dinka da internet in
sunyi zakaga hoton G ko GPRS a saman screen dinka, bayan sun bude maka
zakaga wannan G din ta futo,to daga nan sai kafara Bowsing dinka, idan baka
gane yadda zakayi ba sai kaduba inda aka rubuta Go to, a jikin handset
dinka idan kaga wurin sai kadanna OK bayan kadanna sai karubuta wap.google.com
ko karubuta wap.oa.yahoo.com zai kaika yahoo bayan anbudo maka, zaka ga google kamar yadda
kake ganinsa a computer sai kazo dogon layin nan sai karubuta abun dakake nema
a internet, idan kuma kanason email dinka ne sai karubuta yahoo mail sai kadanna
search bayan ankawo maka sai kayi click zai kai ka inda zka yi sign in zuwa
Email dinka, Idan baka gane ba ko kanason cikakken bayani gamea yadda ake
browsing a Handset to kai aiko da message zuwa manniruahmad@yahoo.com ka duba karshen wannan Handout din TUNTUBE MU
A
WASU ADIRESHIN WAP MASU
AMFANI
Adireshin da zakaje, ka fadi
kaga cututtuka da magungunansu
·
Shine:- wap.pocketdoctor.co.uk
Adireshin dazakae kayi
chatting, na yahoo messenger
·
Shine:- uk.yahoo.com
Adireshin yahoo a handset
·
Shine:- http://oa.yahoo.com ko http://wap.oa.yahoo.com
Adireshin chatting na
MSN/HOTMAIL
·
Shine:- wap.e-messenger.net
Adireshin Google Search
Engines a Handset
·
Shine:- wap.google.com
A direshin da zakaje kaduba
dictionary, ko kanason ma’anar wata kalma
·
Shine:-
dictionary.reference.com/wireless/index.htm
WASU KALMOMI DA MA’ANONINSU
·
INTERNET EXPLORER = Software ce wacce zata baka damar shiga da ganin fejinan da suke cikin
Internet.
·
CHATTING = Hanya ce tayin magana ta hanyar rubutu da hannu, dazakayi da abokananka
ko yan uwanka da suke cikin Internet,
za’a iya yinsa ne ta hanyar rubutu, ko sauti (magana), ko gani (kana ganin
mutum) wato Webcam.
·
CLICK = Idan akace kayi click ananufin kadanna mouse dinka bangaren hagu, zaka
danna kan
rubutu ko hoto ko hyperlink, da sauransu.
·
DESKTOP = Wurine da, farko idan ka budo computer shi zaka fara budowa, daga nanne
zaka zabi inda zaka, misali in zakayi Browsing zaka duba Internet Explorer,
idan zakayi chattin zaka duba Yahoo Messenger.
·
DOUBLE CLICK = Ana nufin kayi click sau biyu a lokaci daya, da sauri zakayi click din,
kuma bangaren hagu na miouse din.
·
E- MAIL = Shine kake amfani dashi wurin aikawa da wasiku da sauransu misalin
Email shine:- manniruahmad@yahoo.com .
·
Highlight = ana nufin kayi select din rubutu yadda kuwa akeyi shine zaka zo
farkon rubutu sai saika danna mouse kada ka daga sai kajaa kan rubutun harzuwa
karshen rubutun kada kada ka daga mouse din, idan kayi haka zaka ga zagayen
rubutun yayi baki.
·
Hyperlink = Rubutu ne da akerubutwa wanda idan kayi click akan rubutun to zai kaika
wani website ne.
·
I M = Sako
ne dazaka rubuta shi a chattin, wanda
daka rubuta shi zai tafi zuwa wurin wanda karubutawa kai tsaye, idan
kuma yin chattin da mutum daka rubuta mashi, zai gani shima ya rubuto maka.
·
MESSENGER LIST = Wurine a Yahoo Messenger dazaka aje email din abokananka, yadda duk
lokacin da kashiga yahoo messenger zaka iya gane mutum yana kan computer ko
bayanan, kamar yadda nayi bayani, acan baya.
·
PASSWORD = Wasu nambobi da kake amfani dasu wurin bude email dinka da wurin bude
chatting da sauransu, in baka rubuta nambobin daidai ba ko kamanta su, bazaka
iya bude Email dinka ba.
·
SOFTWARE = Program ne da ake shirya wa computer wadda shi computer zata rinka bi,
ta gane me akasata ko me zata yi.
·
WAP BROWSER = software ce ta Handset wacce zata baka damar ganin fejinan da suke
cikin Internet daga cikin Handset dinka.
·
Yahoo ID = Email dinka da kake amfani dashi na yahoo wanda dashi zakana shiga
chattin ko email dinka, amma idan aka zo rubutashi, ana cire @yahoo.com, din
misali email dina shine mannirgetso@yahoo.com
to yahoo Id dina shine mannirgetso.
Idan kana son fassarar Wasu
kalmomin Computer, Ka ziyarci www.mannir.8m.com
RUFEWA
Daga nanne muka zo karshen
wannan Hand-Out dayake koyar da yadda ake shiga Internet, akwai na biyun sa da
na rubuta wanda shi na rubuta shine akan wadanda suka kware da browsing amma
sunason Karin bayani game da wadansu abubuwa kamar yadda na fada da farko, anan zan daga birona, Duk abin da baka
ganeba, zaka iya aiko mana da wasika, ta cikin Email ko tacikin wayar tafi
dagidanka, zuwa:- manniruahmad@yahoo.com ko manniru@hotmail.com domin samun Karin
bayani.
Sannan kuma, wannan Hand Out
din na rubuta shine saboda wadanda basu san yadda ake browsing ba (shiga
Internet), da kuma wadanda sunsani amma basu kwareba kamar yadda nayi bayani a
farkon wannan Handout din, Duk wanda ya riga ya fahimci wadannan, kuma amma
yanason Karin bayani, game da chattin ko bincike a internet, ko yadda zai rinka
yin Browsin a handset dinsa, Idan yanason wadannan bayanan zai iya ziyartar
website dinmu a www.mannirweb.faithweb.com Ko ya binciki littafan da na rubuta kamar da
Hausa wadanda sukayi bayani akan:-
·
BROWSING
·
EMAILING
·
CHATTING
·
SEARCHING ON THE INTERNET
·
MOBILE INTERNET
Duk an rubuta wadannan
Littafai da Hausa. Sannan kuma ga wanda yake son a rinka koyardashi abubuwa
dabam dabam na bangaren Computer, kamarsu:- Computer Programmin, ms
access, ms excel, ko ms powerpoint, da sauransu, Da kuma ta bagaren
Internet,duk insha Allahu zamu iya koyar dashi ta cikin Internet kamar yadda
muke koyar da sauran Mutane, Sannan malami irin na makaranta, musamman na
primary, idan suna son Karin bayani game da yadda ake shigarwa computer da
maakin yan makaranta, ta fitar da total ta fitar da position, ta fitar da su
average, ta ware wadanda suka haye da wadanda suka fadi tayi print din Report
sheet na yan makaranta, idan suna so sukoyi wadannan abubuwan, sai su aiko mana
da wasika ko su ziyarci website dimmu a www.mannirweb.faithweb.com anan duk zai sami wani bayani, ya iya aiko
mana da Email.
TUNTUBE MU A
·
WEBSITES
o
www.mannirweb.8m.com
o
www.mannir.faithweb.com
·
E-MAIL ADDRESSES
·
Gsm Numbers:-
o
08025095444
o
08035906774
o
08056241130
GARGADI
BA’A YARDA A BUGA WANNAN HANDOUT DIMBA, KO AYI
PHOTOSTAT DINSA , SAI DA IZININ MARUBUCI.
WASU DAGA CIKIN HANDOUT DA NA BUGA
- FUNDAMENTALS OF PROGRAMMING IN
VISUAL BASIC
- AN INTRODUCTION TO VISUAL BASIC
APPLICATION FOR EXCEL
- AN INTRODUCTION TO VISUAL BASIC
APPLICATION FOR ACCESS
- AN INTRODUCTION TO VISUAL BASIC
APPLICATION FOR MS WORD
- AN INTRODUCTION TO WEB
PROGRAMMING USING VBSCRIPT
- AN INTRODUCTION TO WEB
PROGRAMMING USING JAVASCRIPT
- WINDOWS PROGRAMMING USING MACRO
- WINDOWS PROGRAMMING USING VBSCRIPT&JAVASCRIPT
- WEB PROGRAMMING WITH VISUAL J++
- INTRODUCTION TO IINTERNET IN
HAUSA
- INTRODUCTION TO PROGRAMMING WITH
VISUAL BASIC
E.T.C
Idan kanason handout din zaka iya aiko min da wasika
zuwa manniru@gmail.com ko ka ziyarci www.mannir.8m.com
WASSALAM
By:- MANNIR AHMAD
ADAM GETSO
No comments:
Post a Comment