Sunday, July 30, 2017

KOYI YADDA AKE AIKI DA NA’URA MAI KWAKWALWA

KOYI YADDA AKE
AIKI DA NA’URA MAI KWAKWALWA


NA
Mannir Ahmad getso






MALLAKA
Hakkin Mallaka (m) Mannir Ahmad Getso

Copyright © Mannir Books Publishing Department

Division of Mannir Microsystems

ANA IYA SAMUN WANNAN LITTAFI A WADANNAN WURARE:-


Ahtumu Business Centre, Getso
Giwa Islamiyya Pri. School, old side, Getso, Gwarzo LGA, Kano

Annur’s Book Shops
Beside General Hospital Gwarzo, off. Tasha,
Gwarzo LGA, Kano.  08080908625

I.I. Gwasamai Bookshop
Layi na Biyu Bayan Masallacin Abacha,
Abubakar Rimi market, sabon gari, kano
08055072544

S. Mukhtar Computer & Business Centre.
Kwanar Jaba Bus Stop, By Ahmadiyya Road Gama “C”
Nassarawa Local Government, Birgade, Kano State.
064930176, 08028910000, 08034366692.

Nasiha Printing Press,
Layin Unguwar Bello, Konannen Gidan Mai, Dorayi, Gwale LGA, Kano State

Dikkori Visual & Communication
Post Office. Off. Famingo Store, kano
08060364746

Rahama Computers  & Training Institute
Kofar Arewa, Jama’are, Bauchi State
08058640754


GARGADI
Ba’a yarda a buga wannan littafi ba ta kowace hanya bada rubutaccen izinin marubucinsa ba, haka kuma Ba’a yarda a sarrafa shi ta kowace irin hanya b

ABUBWAN DA SUKE CIKI









































GABATARWA

Ina farawa da sunan Allah mai Rahama mai Jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga manzommu Annabi Muhammad (SAW); Godiya da yabo sun tabbata ga Allah (SWT), wanda bai haifa ba kuma ba’a haife shi ba, mamallakin kowa da komai, Wanda ya halicci kowane abin halitta, kuma ya bawa dan Adam damar kera abubuwan bam mamaki, kuma ya bashi fasahar jujjuya abubuwan daya kera. Tsira da aminci su kara tabbata ga babban bawansa, kuma masoyinsa, Annabi Muhammad (SWA); Bayan haka, na rubuta wannan Littafin ne domin yan uwa na hausawa masu son su koyi yadda ake aiki da na’ura mai kwakwalwa, amma basu da lokacin da zasu je su koyo yadda ake aiki da na’ura mai kwakwalwa, ko kuma basu kware da iya yaren turanciba bare su gane yadda zasu rinka aiki da na’ura mai kwakwalwa. Shi wannan littafi zai koyar da kai yadda zakayi aiki da na’ura mai kwakwalwa kai da kanka batare da wani ya zo ya zauna ya koya maka ba. A zamanin nan namu a yanzu zakaga yawancin abubuwa sai da kwamfiyuta. Akwai abubuwa da dama wanda akeyi da kwamfiyuta misali buga takardu koyon karatu zanan gidaje lissafe lissafe, bincike, kallo faifan CD, ajiye wasu muhimman abubuwa da suaransu. Sannan shi wannan Littafi akwai Bidiyo CD na littafin wanda zai koya maka yadda zakayi aiki da na’ura mai kwakwalwa dalla dalla, komai kana gani ta bidiyo yadda zaka gane komai cikin sauki, zaka iya samun Bidiyo CD a wuraren da ake siyar da Littafin, sunan CD  KOYI YADDA AKE AIKI DA NA’URA MAI KWAKWALWA.
MANNIR AHMAD ADAM GETSO
Saturday, March 31, 2007   3/31/2007 4:25:00 PM






































ME CECE  KWAMFIYUTA?


Kwamfiyuta wata na’ura ce ko inji wanda tana sarrafuwa ne da taimakon ajiyayyun dokoki wadannan dokokin sune suke bawa kwamfiyuta doka tayi kaza ko ta sarrafa kaza tana karbar umarni ta hanya ta musamman ta sarrafa wannnan umarnin da taimakon kwakwalwarta ta fitar da bayani ta hanya ta musamman.


TA YAYA KWAMFIYUTA TAKE SARRAFA BAYANAI?


Kwamfiyuta tana sarrafa bayani ne da taimakon wani abu wanda ake kira program shi wannan program din shine yake nuna wa kwamfiyuta mai zatayi kuma tataya zatayi, shi wannan program din shiryashi akeyi.  Bangaren kwamfiyuta da yashafi shirya pogram shi ake kira programming, wanda yake shirya wa kwamyuta dokoki shi ake kira programmer. Misali yadda kwamfiyuta take aiki shine:- misali dan adam yana shakar iska ta hanci wannan iskar da ya shaka acikinta akwai wani sinadari da jinni yake bukata wato oksagin(oxygen) bayan munshaki iskar sai hunhu ya cire oksagin daga jikin iskar sai mu numfasar da wani sinadari da ake kira kabon dai okzayid sabo da anriga ansarrafa iskar, abin da zakayi la’akari anan shine na farko ka shaki iska ta shiga cikin hunhu ansarrafa ta, sannan kadawo da ita kaga anan akwai mashiga(input), sarrafawa(process), da kuma fitarwa(output), to itama kwamfiyuta haka take aiki awai inda za’a shigar mata da bayani sannan ta sarrafa bayanin sannan ta fitar da sakamako.


INA DA INA AKE AIKI DA KWAMFIYUTA?


Bayan buga takardu da akeyi da kwamfiyuta, ana amfani da kwamfiyuta a wurare da dama kamar:-

  • Makarantu: ana amfani da kwamfiyuta a makarantu da dama domin lissafe lissafen maki na dalibai, tattara sakamakon daliban makaranta gabadaya maka sakamakon, fitar da yawan maaki, ware na daya harzuwa na karshe, ajiye sunaye da bayanai na dalibai, ajiye sunayen abubuwan makaranta, koyar da dalibai, da sauransu.
  • Asibitoci: ana amfani da kwamfiyuta wurin ajiye rakod na marasa lafiya, gadaje, likitoci da kuma nas, kudaden da marasa lafiya suka bayar, kwamfiyuta(Robot) tana rarraba abinci ga marasa lafiya.
  • Bankuna: a bankuna ma ana amfani da na’ura mai kwakwalwa domin ajiye rakod na kwastama, bayanai game da akawun din kwastama, bawa kwastama kudi(ATM ako da yaushe ko da daddare kwastama zai iya zuwa yafitar da kudinsa daga cikin kwamfiyutar da aka ajiye ta don bayar da kudi wa kwastama(ATM))
  • Gidaje: a gidaje ma ana amfani da kwamfiyuta domin yin karatu, bincike, kallon faifan cd, wasanni na gem, lissafe lissafe, buga takarda ko wasika, aikawa da wasika, kasuwanci ta cikin Internet, da sauransu.
  • Gwamnati: Ma’aikatu na gwamnati suna amfani da kwamfiyuta wurin ajiye bayanai na game da ma’aikata, da lissafin salarainsu, da sauransu.
  • Kamfanoni da Ma’aikatu: kamfanoni da ma’aikatu suna amfani da kwamfiyuta wurin lissafin abubuwan da suke kerawa, ko amfani da kwamfiyuta wurin kera wani abu, misali kwamfanin kera motoci da jirage suna amfani da kwamfiyuta wurin kera motoci ko jirage, sanna kuma kwamfiyuta(Robot) na iya kera kwamfiyuta da sauransu


TARIHIN YADDA AKA KIRKIRO KWAMFIYUTA

Kafin zuwan kwamfiyuta dan adam yakera abubuwa da dama wurin aikawa da sako, ko nuna sako, misali a fako dan adam yana amfani da yatsunsa guda goma wurin yin lissafi, da yasamu ci gaba sai ya koma yana aiki da duwatsu idan zai irga dari sai ya hada dutse dari tukunna, idan zai tara saba’in da talatin sai ya samu dutse guda saba’in sannan yakara talatin akan saba’in din sannan ya irga yawan duwatsun sai yaga dari. Bayan ya sake samun ci gaba sai yake amfani da farin dutse da kuma bakin dutse shi farin dutse yana nuna goma, shi kuma baki na nuna daya idan zai nuna ashirin da uku sai ya sami fari guda biyu baki guda uku ya zama 23 kenan, idan zai tara 23 da kuma 4 sai ya saka farin dutse guda 2 sannna ya debo baki guda 3 sannan ya kara wani bakin guda 4 sai ya irgasu gaba daya. Daga baya bayan ya sake samun cigaba a wurin shekara ta 1200 sai yakirkiri wani abu wanda ake kira abakus, ana amfani da shi a lokacin a kasashen caina wurin yin lissafi. Bayan haka misalin shekaru dari uku da suka shige dan adam ya sake kera wasu injina na lissafi kamar su, PASKALINE(faskalin), THE STEPPEDD RECKONER, JACQUARD’S LOOM. Sannan a shekara ta 1822 aka samu wani banasare mai suna Charles Babbage yakera wani inji wanda za’a iya lissafi sosai da shi. Bayan yakera nasa a karni na farko na kwamfiyuta wato (Generation of Computers). Tun a karni na farko lokacin da ake yakin duniya na biyu a shekara 1939 zuwa 1945 yawancin kwamfiyutoci masu aiki da lantarki ankera su domin a lokacin da ake yakin kasar Jamani tayi amfani da kwamfiyuta wurin kera wani mizayil da kuma bamabamai. Sannan kuma a lokacin turawa sun kera wata kwamyuta wacce ake kira  COLOSSUS wanda zata taimaka ta sato musu duk wani zancen da Jamani ta aikawa sojojinta. A karni na farko kwamfiyuta girman ta a kalla yakai kamar gida guda lokacin sai manyan ma’aikatu ne suke aiki da ita.
Akarni na Biyu kuma an rage girman kwamfiyuta da taimakon wani abu wanda ake kira TRANSISTOR (tiranzista). Kwamfiyuta ankera tane da tiranzistoci wanda yawan wadannan tiranzistocin sune suke bawa kwamfiyuta dammar yin lissafi mai zurfi, cikin dan kan kanin lokaci, a lokacin zaka samu kwamyuta tana da tiranzistoci kamar dubu a cikin ta kuma a lokacin girman ta ya ragu sosai domin bata wuce girman daki ba.
A karni na uku da na hudu ne aka sake samun ci gaba ta yadda ake hada tiransistoci kamar dubu daya a jikin wani dan kankanen abu da ake kira (IC INTEGRATED CIRCUITS). Shi wannan IC din wani ya kunshi sama da tiransista dubu goma.
Karnin kwamfiyuta na biyar, a karni na biyar ansamu cigaba sosai domin a karni na hudu akwai kwamfiyutar da bata wuce girman tibi (TV) ba, sannan daga baya aka sake kera wacce zaka iya dorawa a cinyi wato (LAPTOP), a karni na biyar kuwa ankera kana nan kwamfiyuta wacce bata fi ka saka ta a aljihuba wacce zata iya yin abubuwan da babbar zatayi koma ta fita sauri. Domin transistocinta an matsesu kuma gasu da dimbin yawa ankera su yadda idan suka sami wuta yar kadan zasu iya sarrafa kansu. Wato yar karamar wuta ta isa suyi aiki.
A karnin damu ke ciki da kuma na gaba: a karnin da muke ciki a yanzu ankera kwamfiyuta girmanta baifi biro ba kuma zata iya duk wani aiki da babbar kwamfiyutar zatayi.
kwamfiyuta zata iya abubuwan ban mamaki, domin ankera kwamfiyuta mai siffar dan adam wato (ROBOT) wacce, zata iya shiga aji ta koyarda karatu, wato ta koyar da dalibai ko wane darasi, sannan akwai wacce an kera ta kamar likita zata iya yin aikin likita, misali kafada mata abubuwan da suke damunka tarubuto maka magun gunan da zaka nema, akwai wadanda an kerasu kamar sojoji, zasu iya fita suyi yaki sosai kamar yadda sojoji suke yaki, kuma duk kwamfiyuta ce, har zasu iya tuka mota, akwai irin su (AI ARTIFICIAL INTELLIGENCE) wadanda zasu iya dafa abinci su rarraba abinci a hotel da sauransu. Sannan zaka ga bayan wadannan abubuwan da muke dasu akwai Intanet (wato yanar gizo-gizo) idan kanason kasan me nene Intanet da kuma yadda ake shiga Intanet zaka iya laiman littafina mai suna KOYI YADDA AKE SHIGA INTANET. A Intanet zaka iya abubuwa da dama hatta kasuwanci zaka iya yi, zaka iyayin aiki na cike fom ko talle ka samu riba mai yawa, ko gina shafin yanar gizo-gizo (Idan kanason ka koyi yadda zaka gina shafin yanar gizo-gizo) kalaimi littafina mai suna KOYI YADDA AKE GINA SHAFIN YANAR GIZO-GIZO), akwai kasuwanci dabam dabam da akeyi a Intanet, akwai canjin kudaden kasashen waje, idan kanason Karin bayani game da yadda ake kasuwanci ta Intanetzaka iya ziyartar shafin yanar gizo-gizo a www.mannir.com./forum .

HALAYEN KWAMFIYUTA

Duk wata na’ura da zata iya sarrafa abubuwa da sauri kwamfiyutace zaka iya gane haayen kwamfiyuta kamar haka:-
  • Sauri: kwamfiyuta tana da matukar sauri domin zata iya sarrafa abubuwa kamar miliyan daya a cikin sakan, batare da tayi kuskure ko daya ba.
  • Yawa: kwamfiyuta tana iya daukan abubuwa masu dimbin yawa, akwai kwamfiyutar da zata iya daukan abu guda Biliyan dari uku, a cikin ma’ajinta(HARD DISK).
  • Sarrafuwa: kwamfiyuta ana sarrafata ta hanya da dama, duk yadda kakeson ka sarrafta, misali zaka iya jin labaran rediyo, zaka iya kallon labaran TV, idan kasaka katin kallon labarai, zaka iya buga waya da ita, zaka iya lissafe lissafe, zaka iya amfani da ita wurin kunna makunnin lantarki na dakinka, zaka iya koyan karatu da ita, da sauransu.
  • Bata dokoki(Programming): zaka iya shiryawa kwamfiyuta umarni ta rinka bin umar ninka, ko ka koyar da ita abu, misali zaka iya mayar da ita hausa, zaka iya sata ta karanta maka hausa, zaka iya mayar da rubutunta daga turanci zuwa hausa, zaka iya kera taskarta (OS) na hausa, idan kanason application na kwamfiyuta da zata rinka karanta hausa zaka iya samunsa a wannan shafin yanar gizo www.mannir.com/forum

AJUJUWAN KWAMFIYUTA

Kwamfiyuta an shiryata zuwa ajujuwa a kalla guda hudu sune:
Supercompupters, Mainframe, Minicomputers da Microcomputers.

Supercomputers: ===


ABUBUWAN DA SUKA HADU SUKA GINA TASKAR NA’URA MAI KWAKWALWA

Abubuwan da suka hadu suka gina ilimin na’ura mai kwakwalwa abubuwa ne guda biyu wato Hardware da Software.
Hardware sune bangaren kwamfiyuta wanda kake gain sannan katabashi misali:- Kibod, Mawus, Monita, da sauransu.
Software: wasu dokoki ne da kwamfiyuta take aiki da su domin ta sarrafa kanta, wanda wannan dokokin sune suke sa hardware tayi aiki, wadannan dokokin shiryasu aikeyi wanda zasu rinka ba kwamfiyuta dammar yin wani abu, misali akwai softwayar da zata taimaka maka wurin rubuta wasika da kwamfiyuta, akwai softwayar da zata taimaka maka domin yin lissafe lissafe, akwai softwayar da zata taimaka maka wurin aikawa da wasika zuwa wani wuri, akwai softwayar da zata taimaka maka wurin bude waya idan ta kulle, akwai softwayar da zata taimaka maka kayi karatun wasu litattafai, akwai softwayar da zata taimaka maka kamar yarda kaset na bido zuwa fai fayi CD akwai softaya da dama sama da miliyan daya kowacce akwai aiki da zata iya yi maka kaidai idan kanason kayi wani abu saidai kawai ka laimi softwayar. Idan babu softwaya hadwaya bazata yi aiki ba.

ABUBUWAN DA SUKA HADU SUKAYI KWAMFIYUTA

1. MOUSE(mawus) wani abu ne kamar bera da ake motsashi domin a zabu abu ajikin kwamfiyuta ko abu ne wani abu misali idan ka budo kwamfiyuta zaka ga abubuwa da dama a wurare dabam dabam da mawus din zaka juya kaje ka zabi abin da kake so.
2. Keyboard(Kibod) wani abu dogon abu ne wanda akwai madannai ajikinsa shi ake dannawa a shiagrwa da kwamfiyuta rubutu.
3. System unit: wannan shine ginshikin kwamfiyuta, itace asalin kwamfiyutar komai anan yake faruwa sauran abubuwan shigar da fitar da bayanaine, misali zaka shigar da rubutu da kibod rubutun zai shiga cikin system yunit a sarrafashi sannan a fitar da sakamakon jinkin monita.
4. Monitor(monita): shine abin da zaka gain kamar tibi(TV) shine yake nuna duk abubuwan da suke faruwa acikin kwamfiyuta shine idan kayi rubutu a kafin kafitar da rubutun ajikin ajikinsa ne zaka ga takardar kafin kabuga ta.
5. Speaker(Sipika) wannan itace sipika wacce zaka rinka jin sauti na fitowa daga cikinta, misali idan kasaka faifan cd ka kunna shi da kwamfiyuta zaka rinka jin sautin na fitowa daga jikin sipika.
6. Printer(Firinta): duk takardar da karubutu ko bayani idan kanason kafitar dashi a takarda zaka yi amfani da firinta domin fitar da bayanin ka a takarda.
7. UPS (Ultra Power Supply):  ups ana yana taimakawa ne wajen idan kana aiki da kwamfiyuta ko an dauke wuta zaka iya cigaba da aikin ka babu wuta hatsawon a kalla minti 15, domin ka krufe abubuwan da kake aiki da su har ka kashe kwamfiyutar ka.

AMFANIN KWAMFIYUTA

Ana amfani da kwamfiyuta a abubuwa da dama misali:-

  1. Buga Takardu
  2. Lissafe lissafe
  3. Bincike
  4. Aikin bankuna
  5. Shirya sakamakon jarrabawa
  6. Kere kera
  7. zane-zane
  8. Koyon karatu
  9. kasuwanci
  10. shiga Intanet
  11. Kera jirage da motoci

RASHIN AMFANIN KWAMFIYUTA

Kamar yadda yawancin abubuwa a duniya suna da amfaninsu kuma suna da rashin amfani haka ma ita ma kwamfiyuta tana da amfaninta kuma tana da rashin amfani, rashin amfanin kwamfiyuta sune:-

  1. Kwamfiyuta tana da tsada musamman Laptop
  2. Aikin da ma’aikata goma zasuyi a wata a rinka basu albashi kwamfiyuta zata iya yinsa a kwana daya, kaga su ma’aikta sun rasa aiki
  3. Anyi ta da turanci, kwamfiyuta aniyita da turanci kaga bahaushen da bai iya turanci ba, aiki da kwamfiyuta zai yi mai wahala.
  4. Tana da abubuwa da yawa, kwamfiyuta tana da abubuwa da yawa kafin ace ka koyi wannan, sannan ka koyi wannan sai ka dau lokacin sosai
  5. Karatunta akwai zurfi, karatun kwamfiyuta akwai zurfi, misali akalla kwamfiyuta tana da programming language sama da dari kafin ace ka koyi daya sai kadau watanni. To amma amfanin kwamfiyuta sun ninka rashin amfaninta yawa, domin da kwamfiyuta zaka iya abubuwa da dama.
  6. Tana diban cuta:- kwamfiyuta tana diban cuta (Virus) idan cuta ya kamata zata rinka wasu abubwa dabam kamar goge maka fayil canza fayil satan faswad da sauransu

No comments:

Post a Comment